← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 74

Sashe 3

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasham...da yaransu na Bajju yana nufin abu me kyau.kuma a zahirin gaskiya wannan suna ya dace da ita dan me kyance, matsakaiciyace a tsawo,me k'irar kalangu,gata da yalwataccen gashi me tsawo da santsi,shi yasa ba kasafai take kitso ba, manyan idanunta masu maik'o(Oil eyes)da d'an k'aramin bakin ta su suka k'ara mata kyau na musamman,wankan tarwad'a ce a yanayin kalar fatar jiki,itama dalibace anan Kaduna State College Of Education(KSCOE) Gidan Waya.Aranar farko a kuma kallan farko data ma Julaibib so da k'aunarshi suka mamaye zuciyar ta ba tare data shirya hakan ba, duk tarin samarin dake mata nacin suyi soyayya sai taji ba wanda yamata nan duniya daya wuce Julaibib,ta so k'warai a ranar suyi magana amma hak'anta bata tadda ruwaba, saboda kwarjinin daya mata lokacin data tunkareshi,ashe gaba da gabanta aljani daya taka wuta.To amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da jifa"naci da shishshiginta yasa suka fara gaisawa duk da idan ba ita ta gaishe shiba ko zasu had'u sau dubu a rana bazai nuna yama ta6a ganin taba.

Duk inda tasan zata ganshi to in dai ba tana da lecture ba to tana wajan,yau da gobe sai ya fahimci tana neman wuce makad'i da rawa sai yadad'a kamewa,amma da Musaddiq sun saba dan suna d'an ta6a hira dan shima yana da miskilanci idan baiga dama ba,amma gangaran d'in miskilai sai "Julaibib Abdullahi D'ansarai ".

Musaddiq yana zaune a capteria yana cin abinci tazo tasa meshi tana fad'a mishi "Wallahi Musaddiq na ka sa danne zuciyata,na ka sa yin yak'i da ita,gaskiyar magana ina san Julaibib zan aureshi".

Cikin tsoro da mamaki yace kina san Julaibib?Yagirgiza kai"to gaskiya ki cigaba dayin yak'in wajan ganin kin cireshi a zuciyarki,baza ki samu abinda kike so...ta tareshi da sauri"me yasa za kace haka? Saboda baki dace dashi ba"wai d'an dambe ya d'auki adda"ni nasan Julaibib farin sani wallahi,kinga kuma addininmu ba d'aya bane. Idanunta suka ciko da k'walla,"wai yau ita ake fad'ama namiji ba zai so taba a yadda take d'in nan me kyau...

Tayi jimmm..na wucewar wasu dak'ik'u "Musaddiq kafad'a mishi "ni Kasham tanuna kanta ina sanshi,ina neman goyon bayan shi ya yadda muyi aure,na mishi alk'awari zanyi abinda yakeyi (Sallah)zanbi addininshi (Musulunci) Abincin da bai gama ciba kenan yamik'e dan zata dame shine kawai.Tabishi da kallo dan ALLAH kafad'a mishi.Ya amsa da To.

Rannan tana zaune a d'akin karatu, nazari da bincike(Library) ta ka sa yin abinda yakaita tunanin Julaibib ne kawai yacika kanta,kamar ance ta d'ago kai sai kawai gashi yashigo dak'in,yaja kujera yazauna.

Ganinshi yak'arasa kashe mata jiki, tanajin wani sabon yanayi daya tsirga ilahirin jiki da zuciyarta,gefe guda kuma tana jin takaicin k'in kar6an tayin soyayyar data keta mishi naci duk da kasancewarta k'wararriya data isa da kanta in dai a fagen hilatar d'a namiji yafad'o tarkon tane,ba wanda ta ta6a d'anama tarko bai fad'aba sai Julaibib,ta rasa me zatayi dan shawo kanshi,dan abinda takeji game dashi ba irin abinda takeji game da sauran maza bane,wani irin abune me sark'ak'iya,me zagaye ilahirin gangar jiki da zuciya,ita kanta bata san ya zata fassara shiba wallahi.Tasake kallanshi rubutu yakeyi cikin natsuwa,takad'a kai.

"Julaibib...you're an enigma".

Ahankali ta furta hakan,sannan tabi d'akin da kallo mutane dayawa sun gama abinda yakaisu sun fita,saita samu k'warin gwiwa koda zai wulak'anta ta bazai mata ciwo dayawa ba tunda mutane kad'anne. Tamatsa gaban kujerar dayake zaune,tasunkuyo tana kallan fuskarshi"Sannu da aiki Julaibib...tafurta hakan da wani salo irin na ta na yanga.Bai d'ago ya kalletaba kamar yadda take fa ta,bai kuma amsaba "shiruma amsace"rubutun shi kawai yakeyi.

Tatsareshi da manyan idanunta masu maik'o,ya mata kyau cikin fararan kayan,yau kanshi ba hula,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata sheki da k'amshin irin mayukan gyaran gashi da yake amfani dasu,jikinta ya gama mutuwa murus,ga k'amshin arabian perfumes d'inshi yadad'a jefata a wani irin yanayi,ta lumshe idanunta wani murmushi ya su6uce mata "ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baiciba yayi burgima"taja dogon numfashi tana zuk'e k'amshin,ahankali kuma tafara fesar da iskar tabaki ta hanci sannan tabud'e idanunta tacigaba da mishi kallan k'auna me cike da shauk'i har yagama rubutun,yatattara takaddun daya shigo dasu a gefe, yakwashi wad'anda yad'ibo a d'akin yamayar dasu mazauninsu.

Magana take mishi amma yayi kamar ALLAH baiyi ruwan tsiran taba,ganin haka yasa tayi saurin k'arasawa bakin k'ofar da zai fita ta tare hanya sai yaja yatsaya.

Please...Julaibib...
Magana nake so muyi please...tahad'a tafukan hannayenta alamar magiya."please Julaibib, wallahi with all my heart ina sanka,kana burgeni, me zai hana ka aureni?

Yagirgiza kai"Bazan iyaba.Idanun ta suka ciko da k'walla"wai kai wannan amsar ta "Bazan iyaba"bazata bar bakinka bane D'ansarai? Wai me zan yine da zaka so ni Julaibib?Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi nadama tana 6ata mishi lokaci fa.

Ki matsa zan wuce.Tasake kallanshi "Julaibib zanyi sallah fa...yad'ago yana mata rikitaccen kallanshi "Ki bani hanya nace ko? Yafurta hakan da 6acin rai a fuskarshi.

Yamata wani irin kwarjini data kasa aiwatar da k'udurin zuciyarta.Sai tagyad'a kai ta kuma matsawa a kofar"shi kenan zo ka wuce.Ya ra6a ta gefenta kamar wanda akace idan ya ta6ata ya gama amfani a doron duniya.

Tabi bayanshi da kallo har ya6ace ma ganinta...sai tayi d'an yak'e mak'alallun k'wallan cikin idanunta suka samu damar d'igowa a kyakkyawar fuskarta, sai kuma wani sanyi-sanyi data faraji, tsigar jikinta yana tashi alamar zazza7i yana so yakawo mata ziyara.

Harshenka zakinka idan kasa keshi yacin yeka"...

11 Rabi'a Thani 1441
8 December 2019

We Ibrahim's Daughters👇

Asdilat KD...2 geda with Ra'ibs.

DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}

Bismillahi wabihi nasta'in.

...GWAJIN DAFI💔

Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)

Shafi na biyu.

Musaddiq yashigo da sallama, yad'auki ya zauna yasha,sannanya kalli Julaibib "sak'o aka bani wajanka...sai kuma yaja yayi shiru. Yad'an d'ago ya kalleshi"Uhun ina jinka sak'on me? Yaciro d'an k'aramin kati launin ruwan k'asa yanata kyal-kyali yamik'a mishi "karanta kagani.Kasham ce take gayyatar su party dan murnar zagayowar ranar da aka haifeta(Birthday) ranar talata a Bigard Hotel.

Yad'ago yana mishi wani rikitaccen kallo "nasha fad'a maka yarinyar nan ta daina aiko ka wajena kana zuwa kana fad'amin ko?Ya jijjiga kai"to ba laifi ka cigaba amma abinda zan maka zaka sha mamakinshi wa...bai bari ya k'arasa ba shima yatareshi"ba laifinka bane nawane ainan d'in tace za tazo tasame ka da kanta, ni kuma sanin da nayi baka san hakan yasa nace mata ka tafi Matsirga amma takawo in ajiye maka da...shima Julaibib ya tare da sauri..."na tafi Matsirga,na tafi Matsirga fa kace?To saboda me zaka min k'arya?Ganin ranshi ya 6aci yace"kayi hak'uri D'ansarai.Baice komai ba yakoma yakwanta,duk sukayi shiru,zuwa can Musaddiq yasake kallanshi."Kasham da gaske tana sanka Julaibib, ko zamu d'an lek'a matane ko na rabin awa dan itama taji dad'i yaba kyauta tukwuici.Yagalla mishi harara"idan zakaje to ni ina ruwana?Musaddiq yayi murmushi"D'ansarai autan Inna me duniya.Inje kuma?To ni asuwa?Kare da gudun laiya?Da dai zakaje dana maka kara na rakaka.

Yamik'e ni ga ka tafiya ta wajan Safiyya,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"Ka gaisheta.Musaddiq yad'an zaro idanu dan mamaki "Wuuu yau wace rana Julaibib yaji zanje wajan masoyiyata yace agaisheta? Julaibib yamik'e zaune da sauri,yana k'ok'arin kai mishi naushi yagoce yana dariya, ah ka ga mugu da 6allallan kafad'a kake so inji hirar"uu tambayata kakeyi?To tsaya yanzu zaka gani ya yunk'ura zai mik'e Musaddiq yafito daga d'akin da gudu yana fad'in "mu had'u a gidan Hajiya bayan sallar la'asar".

Agajiye yashigo gidan,dawowar shi kenan daga Kaduna.Yaya Karima ta tareshi "oyoyo barka da dawowa.Yauwa Yaya Karima.Yacire takalman shi masu rufi,sannan ya zauna a tabarmar tsakar gidan suna gaisawa.Inna tafito daga D'akin-girki"lale D'ansarai autan Innar shi"sukayi dariya to gashi,ruwa tabashi a k'aramin kwanan sha.

Yakar6a"nagode Inna.Da bismillah yafara shan ruwan,ruwan randan Inna me dad'in gaske ga wani irin sanyi,kowa kuma ya san ruwan randa sanyin shi baya cutarwa,ga k'amshin saiwoyin da take sawa a ciki da suke k'arama ruwan armashi wajan sha.Kad'an yarage sannan ya ajiye kwanan cikin hamdala ga ALLAH.Yakalle ta"Inna ruwan randarki gard'i da d'and'anonshi har yafi ruwan roba Swan.Sukayi dariya.

Abdullahi babban d'an Yaya Karima yayi sallama ya shigo yana rik'e da hannun k'anwarshi Kamila da take kuka."Mama ga tanan tak'iyin shiru tunda ta dawo daga makaranta,wai me yasa baki bari an taso suba kikayi tahowarki.?Ya k'arasa wajan Kawunshi cikin murna "Kawu sannu da zuwa,sannan ya gaisheshi.Yarik'o hannunshi "Yauwa Abdul yakaratu?Ya d'ibo Inibi to ga tsarabar ka.Abdul yasa hannu biyu yakar6a"nagode Kawu ALLAH amfana.

Karima takalleshi kwana biyu ka daina zumunci sai Musaddiq kad'ai yake sadar da ita."Baban Abdul dai yagaji shine yace in biyo sawu ko mun maka laifine"?Yayi murmushi yana shafa kai"Yaya Karima ba kumun laifi ba,bana samun lokacine amma Insha-ALLAH wannan Juma'ar zan shigo kin san tsarin karatunmu ba d'aya bane.Ta gyad'a kai"hakane Ubangiji yanuna mana Juma'ar.Ya amsa da amin.

Wata magana zamuyi.Sai ya tattara hankalin shi ga sauraran abinda zata fad'a."Julaibib me zai hana kafito da yarinyar da kake so a had'a bikinka dana Musaddiq?Ina sha'awa k'warai ace yadda kuke kome tare to lokacin aure ma ku angwance tare.Yagirgiza kai"ni bani da budurwa ma, ki tayani addu'a ALLAH yakawo tagari.To amin. Amma duk yan matan Gidan-Waya ba wacce ka k'yasa?Yad'anyi tsaki'ni fa ba tsayawa kallansu nake yiba,abinda yarabani daku,yakaini can d'in shi nakeyi (karatu)

Musaddiq yashigo yatarar da zancen, yace tab shi autan Inna sai a hankali kuma gashi da farin jini a wajan yan matan amma kowacce sai yace bata da kamun kai,bayan shi kanshi ya sani a shari'ance ba haramun bane dan mace ta yaba da kai tafurta maka kalmar k'auna.Musaddiq yaja dogon tsaki yana hararar Julaibib saboda tuno abinda yata 6ama yar course d'insu.....

Atikah Aliyu Kagoro.

Jikar Sarkin Kagoro ce tana da hankali da natsuwa kuma k'wak'walwannar dai Ubangiji ya hore mata shi na fahimtar karatu,Malamai ma ji da ita sukeyi bari d'alibai yan karankad'a miya.Tunda taga Julaibib tace nan duniya ba wanda yamata da aure kamarshi.sai dai kashhh...yawatsa mata k'asa a idanu.Atikah Aliyu Kagoro tayi kukan rashin shi.
Chapter 3 · 0% Book details