← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 74

Sashe 73

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)

Yayi shiru yana tasbihi a cikin zuciyarshi"ALLAH Alhakimu gwanin iya hakima, ALLAH buwayi gagara misali...Qudirarka da yawa take"ni Julaibib Abdullahi D'ansarai ni zan auri 'yar da Sumayya ta haifa?Lallai ba wanda yasan abinda gobe zata haifar sai ALLAH,dan shi wallahi har ya manta da wata Kasham da Sumayya a rayuwarshi...A hankali mafarkan da ya dinga yi na shekara da shekaru suka dawo mishi wannan mafarki me ban mamaki da yarasa gane ma'anarshi

"Kasham da yake gani cikin shigar kayan fulani idan tayi magana sai kuma yaji muryar Sudaida.

Wannan yana nuna Sudaida matar shice,haka kuma zai auri wata kenan me alak'a da Kasham d'in?Gashi kuwa ya tabbata 'yar data haifa a cikinta...kayan fulanin kuma yana nufin kenan Bafulatana ce?Yajijjiga kai"ko shakka babu tunda Alhaji Salim Iyayenshi Fulanine amma girman birni dan ko Iyayensu basuyi kiwon shanu ba bare kuma su... La'ilaha'illallah.

Sai yasake tuno ranar da Maimun yake fad'a ma Musaddiq mafarkin da yayi"Wai shi da Kasham ne suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi"Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka take tayaka kiwo saboda tsabar k'auna?A lokacin bai kula suba.Yayi ma Alhaji Salim godiya sosai,amma har yabar gidan bai daina mamakin wannan al'amarin ba.

Bayan tafiyarshi Ummi tashigo d'akin da sallama,ta zauna tana kallanshi"Abbana kace za muyi wata magana idan ka dawo daga masallaci, yana murmushi yace ban manta ba Ummi,ya san yana da yak'ini zata amince,sai yafara mata nasiha akan biyayya ga Ya'ya a wajen Iyayensu wajibine matuk'ar abinda suka zo dashi bai sa6ama shari'ar musulunciba,a hankali kuma yafara kambama halayenta na k'warai, ganin tana ta murmushin jin dad'i,sai ya maida abun zuga"ai na san baza ki bani kunya ba;baza ki watsa min k'asa a cikin idanu ba,ni a duniyar nan ban ta6a ganin yarinya me tsananin biyayya ga mahaifanta ba irinki,nima kinga shi yasa nake miki wata irin k'auna mumaiyiza(ta musamman)

Tagyad'a kai"tabbasss ta yadda Abbanta yana mata k'auna ta musamman d'in dan kome nata na musamman ne wallahi a wajen shi. Cikin d'oki tace"me kake so in maka ne Abbana? Yakalleta cikin kulawa"aure zan miki Ummi,kuma ni da kaina na za6ar miki mijin.Da sauri ta sunkwui da kai dan batayi tsammanin abinda zai fad'a kenan,tanajin wata irin kunya na lull6eta.

Yacigaba da magana "shekaru da yawa da suka wuce ina da labarin shi, mutumin kirkine... kuma nima a yanzu nayi nazarin shi tsafff...naga hakan ganin idanuna,hasashena yana bani zai rik'eki da aminci da amana,burina kullum a kanki Ummi shine kiyi aure,kiyi bautar cikin aure tunda ibadane, ranar alk'iyama ki samu sakamako mafi kyau da daraja,kisamu shiga darul-karamah (aljannah) aljannarma ina miki kwad'ayin samun mad'aukakiya (firdausss)

Yayi shiru yana kallanta"Ummi kiyi magana mana ai ba auren dole zan miki ba,idan kina da za6inki na kuma bincika naga shima mutumin kirkine,toh shi zan aura miki,zan kuma ba wancan hak'uri na san zai fahimceni,tayi k'asa da murya cikin jin nauyinshi"Abbana ina fata in biku in muku biyayya a duk abinda kuka umarceni ko da bana so,zan tilastama kaina so,dan na san baza ku cuceniba,dan nima inaso agaba a bini,na san kuma sai na biku na samu albarkanku,nima zanga da kyau a rayuwata ta gaba.

Yayi lallausan murmushi yana yaba hangen nesan ta"toh kin yadda da za6in Abban naki koda mutumin me gemu da k'asumba cike da furfura kamar na Abbanki?Tasake sunkwui da kai"shi wallahi haka Abba yake magana wasu lokutan sai yaba ka kunya.

Haka rannan yace ma Mamansu wai tana ta wani shashshare shi,to shi gaskiya ya gaji da wannan shariyar,aure zai k'ara kuma sa'ar Ummi zai auro.Ita kuma ta galla mishi harara"dan ALLAH ka auro wacce bata kai Ummi bama.Sai yafara dariya yakalleta"ke Ummi ki zama shaida ai kinji abinda tace ko?Batayi magana ba,sai guduwa d'aki tayi ta barsu,yanzu ma tashi tayi yana kiranta amma bata dawo ba.Alhaji Salim yana da shak'uwa sosai tsakanin shi da Ya'yanshi,dan haka zaiyi wuya yafad'a musu abinda yake so na ayi ko abari kaga basubi umarnin na shiba.

Haiya Bara'atu tak'arasa shigowa"to ai Alhaji wannan al'amari yayi dan shirun budurwa yaddan ta,bazawara kuma sai ta tanka.Tamishi wannan kallan nata dasu biyu suka san ma'anar ta"ko kuwa?Yana dariya ya amsa"ai zancenki ba ja kare ya mutu a juji.

Ranar wata alhamis ba makarantar Islamiyya kuma dama ta gama secondary ana zaman jiran sakamako kafin a d'ora zuwa Jami'a,suna D'akin-girki Alhaji Salim yabisu yana musu sannu da aiki.Suka amsa mishi cikin sakin fuska.Yakalli Ummi "bar kwa6in nan ana sallama dake a waje.Tad'anyi jimmm...Hajiya Bara'atu ta kalleta cikin kulawa"jeki mana Ummi.

Tajuya jikinta a sanyaye tana sanye da riga da zani na atamfar classic,tasa bak'in silifas da hijab tafita,sai dai bata ga kowa ba sai Julaibib,tasha jinin jikinta,ta gaishe shi duk da d'azu tagan shi a hanya da take dawowa daga gidan Alhaji Hafiz kuma ta gaisheshi.Yak'araso in da take tsaye"ai ni nake sallama.

Sai tasunkwui da kai k'asa batace kome ba tana wasa da gefen hijab d'inta"to yaya na miki?nan ma shiru tayi sai yacigaba kinga karfa kiga dan na kwana biyu gemu da k'asumba sun cika fuskata toh na iya soyayya sai na zama tauraronki.Sai kuma yayi shiru yana kallanta ganin har lokacin batace kome ba.Sai yakad'a kai cikim jimamai"Oh D'ansarai marayan ALLAH ba uwa da uba ba sauran dangi da alama baka samu kar6uwa ba dan haka sai ka d'au na Annabawa kawai.Yadda yayi furucin cikin tsananin tausayin kai yasa tad'an d'ago tana murmushi,amma ba shi take kallo kai tsaye ba"Yaya Julaib...ba haka bane ai tunda Abbana ya gamsu da kai bani da ja...shima kallan fuskarta yayi..ALLAH buwayi sai lokacin yake ganin kamanninta da Sumayya har jerarrun hak'oranta farare, da manyan idanunta masu maik'o,wad'annnan sune abinda ta d'auko na ta kai tsaye da kowa zai iya ganewa.Kad'an sukayi hira yamata sallama dan ya lura a takure take.

Watanni uku bayan nan aka d'aura aurensu Alhaji Hafiz yatsaya a matsayin waliyinshi, aka kai amarya gidan mijinta ana musu fatan zaman lafiya. Ummi tashiga bautar gidan aure da duka k'arfi da kuma iyawarta,zaman nasu ba yabo ba fallasa, suna mutunta juna,tana bashi girma a matsayinshi na babba kuma mijinta sama yake da ita,shima yana jin tausayinta amatsayinta na k'arama kuma mace me rauni...

Yasauke gwauron numfashi a sanda k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai tagama tariyo mishi kakaf rayuwarshi daki-daki.

Yauma abinda yasa yamata haka jiya yatafi Gidan-Waya yakwaso kayansu anan yaci karo da kayayyakin Iyalinshi...abinda ya famo mishi wani miki kenan haka ya kwana ranshi ba dad'i... Ummi bata kar zomo ba sai ya bata rataya...yayi huce haushin kaza a kan dami.Yajijjiga kai"gaskiya Ummi bata cancanci haka ba,ai idan d'an kaciya baici kazaba toh tsakani da ALLAH bai kamata kuma yayi baraba...Har lokacin yana jiyo sautin kukanta dan haka ya mik'e dakyar duk da har lokacin kan nashi bai daina ciwo ba.

Ruqayya...tanaji amma tak'i amsawa "haba Ruqayya...sai ya zauna ya gewayeta"Ruqayya Esbeer...ni me laifi ne,laifina kuma babbane...amma na gane kuskurena gani a gabanki na zo ki yafemin...d'ago kanki ki gani na san ke macen albarka ce,baki furta kalamanki ba har sai da kika rasa hanyar bi wajen shawo kan matsalar gidanki,ni d'innan nina tunzira zuciyarki,amma Insha-ALLAH zan kiyaye furucina...ni dai ki taimakeni ki yafemin...ta tari numfashin shi tamik'e zaune tana kallanshi da idanunta da suka kad'a jawur"na yafe maka.

sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta cigaba da magana"Julaib...ina tabbatar maka kana d'aya daga cikin bayin da ALLAH yake so Insha-ALLAH idan katuno da jarabawar Annabi Ayuba Alaihissalam"ya kamu da ciwo tsawon lokaci, Ya'yanshi suka dinga mutuwa,duk jama'a suka k'aurace mishi to amma da yayi hak'uri ya mik'a al'amura a wajen Ubangijin mufa?ALLAH mahaliccin mu yace mishi "madallah da wannann bawa nawa me yawan hak'uri da juriya.

Julaib...karage tunanin nan,ka sani wanda duk ya mutu toh ya mutu kenan abadan,babu sauran soyayya da k'auna da zaka nuna mishi face ka yawaita aika mishi da abincin shi(addu'a)idan kana da hali ka mishi sadaka me gudana,toh Julaib...ka musu anata aika musu da ladan kullum ta ALLAH, kaima kullum kana musu addu'a,nima ina musu, Abbana...Mamanmu, kai da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH ga wad'anda suka ga kisan gillan da aka musu,da wad'anda sukaji labari da sauran yan'uwanmu musulmai na garin Jos da Maiduguri da sauran arewacin k'asarnan.

Duk masu ta'addancin nan tun daga duniya zasu fara ganin sakamakonsu,da izinin ALLAH fashewar kwai a saman kwalta za suyi,mutuwar kare a saura.Tad'an kalleshi"dan ALLAH kayi hak'uri ka saki ranki muyi rayuwar aure kamar yadda sauran ma'aurata suke yi cikin nishad'i da karsashi.Yasauke numfashi"Ruqayya ke macen alherice...ALLAH yamiki albarka.Tagyad'a kai"amin,shukran jazilan...Qad uhibbuka...yatari numfashinta kafin ta k'arasa furucinta"hubban jammahhh...sukayi murmushi"to yanzu muje ki bani abincin yunwa nake ji cikina ba kome sai yan hanji.

Bayan ya gama cin abincin yasha magani yad'an huta,sannan tafara mishi bayani a kan gidauniyar"D'ansarai da Me-Lambu Foundation"da suka kafa musamman dan taimakon marayu da zawarawa yan gudun hijirar Zonkwa da ta samar da kud'i me tarin yawa,d'azu bayan tafiyarka masallaci Maman Hasan ta kirani tafad'a min.Baba Alhaji ma (Alhaji Hafiz) ya sake bamu gudummawa kamar yadda yasaba,sai dai wannan karan kayan masarufi muka samu kasancewar watan ramadana yanata matsowa.

Abbana ma zakkarshi ta bana daya fitar d'ungurungum yabamu kud'in,shi tun jiya bayan tafiyarka Gidan-Waya yakira yafad'a min idan ka samu lokaci kaje ka kar6o dan ya kira lambarka bata shiga.Jikinshi yai sanyi "Ruqayya Ubangijine kawai zai saka muku,ina kuma rok'onshi yasaka muku da mafificin sakamakon shi. Yaciro wasu kud'ad'e masu yawa yana mata bayani "wad'annan farfesa Maimun AbdulQadir ne ya aiko dasu.Tagyad'a kai"mungode kwarai ALLAH yasaka mishi.Amin.Bayan la'asar sai inji in kar6o na wajen Alhaji zuwa jibi sai mutafi Mando mu raba musu,tunda kowa kika gani a wajen yana cikin halin ha'ula'i ne.

"Julaib...wai har yanzu gwamnatin jahar nan ba wani tallafi da zata bayar ne? A yanzu dai kam babu amma bamu san a gwamnatin gaba ba tunda wannan ai kinga saura shekara d'aya tak'are tenure,ke dai Ummi Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira wanda yasamu kud'i ko yaya sai yafara sana'a kome k'ank'antarta yacigaba da addu'a ALLAH yasa mishi albarka sai kiga kome ya wuce,ai da rarrafe yaro yake tashi.
Chapter 73 · 0% Book details