← Book details Gwajin Dafi Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 74

Sashe 62

Gwajin Dafi Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaujiii...kayi kyau,sai ka zama wani d'an matashin saurayi.

Yayi yar dariya"wani saurayi kina ganin Zaujiii...gemu da k'asumbarshi duk furfura...Ni dai a ah ai bawani tsufa kayi ba gaskiya,kai dai girman kawai kake so.Sudaida ai ko girma ya zo gasu Baba ga ku ga sauran bataliyar daza ki haifamin...Yaran suka shigo da gudu dawowar su daga makaranta kenan,suka haye jikinshi suna mishi surutu.Tace"Oya to muje ku canja kaya...sai suka dad'a mak'alewa a jikin Julaibib "ku tashi mana.Julaibib yad'aga mata hannu"kyalesu sai sunyi wanka zasu canja kaya. Tagyad'a kai tatafi tacigaba da ayyukanta.

Tana aikin abincin dare Bilkisu tashigo D'akin-girkin tasha kwalliya da wata yar rigar turawa mara nauyi ruwan hoda da dogon wando da d'an k'aramin hijab ruwan hoda,tanata k'amshin arabi'an perfume d'in Julaibib fuskarta shar da kwalliya,tayi murmushi kawai dan ta san aikin shine,haka yake zama yamata wannan kwalliyar musamman idan tamata laifi tace baza tayiba,shi kuma zai rarrasheta yamata.

Tafara ta6e-ta6e irin na yara"Mama in dai tuwo za kiyi ni bazan ci ba na fad'ama Baba yace to ki mana doya da kwai da nama,kuma ki had'a mana lemun citta da karas,ni natsani tuwo tana wani yamutsa fuska.Sudaida tajuya takalleta"ALLAH Hajiya Bilkisu?Bilkisu tagyad'a kai tana sake fuska 6ata ALLAH kuwan Mama.Tayi yar dariya"Hummm wato ke dai kullum aci me dad'i ko?Kalleki kamar za ki fashe duk kin fi kowa na gidan nan ki6a,toh yau tuwon dawa miyar kuka nake yi,kuma ba lemu tuwo za a ci asha ruwa.Tad'an buga k'afa cikin shagwa6a "ni dai ALLAH bazanci wannan bak'in tuwon ba,gidan Inna zan ce Baba yakaini ai ita zata bani nama,Baba yace ni ce amaryar shi tana nufin Alhaji Abdullahi,shi kuma zai bani madara da yoghort da biscuit short cake.Tagyad'a kai"toh a sauka lafiya ni dai yau d'an gado nake yi.

Tagama kome tagyara D'akin-girkin sannan tafito tasame su yana koya musu aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta amma Bilkisu tanata ta6ara shi kuma yana wani lalla6ata,suka bata haushi kamar ta dake su.Bata dai kula suba itama ta zauna tana nazarin wani project...Basu gama aikin ba amma da Bilkisu tamatsa a tafi sai kawai yabiye mata taje tad'auko mukullin mota yakalleta"Megado nan da gidan Inna sai munje a mota? Tawani shagwa6e"eh Baba.Yakar6i mukullin to shikenan.

Zaujatiii...Za kije ne?Idanun ta na kan Laptop d'inta ta bashi amsa"uh uh adawo lafiya. Yakalleta na wucewar wasu yan dak'ik'u" Sudaida yakiraya.bata amsaba tad'ago suka kalli juna said yawani kashe mata ido d'aya,takauda da kai kamar bata gane me yake nufi da hakan ba.Yayi d'as da yan yatsunshi"kin ci bashi wallahi.Tagyad'a kai"eh ba kome bashi ai hanji ne yana cikin kowa,kafad'i ko nawane zan biya.Yajuya ba fashi kuwa ina dawowa za ki bani.

Tana jin barar"Allazi wahidin...tabud'e k'ofa takar6i robar almajirin tajuye mishi tuwon tunda d'uminshi dan ta san ko sun dawo shima ba wani ci zaiyi ba,wanda za taci kawai tabari,yakar6a cikin rawar jiki data murya"Iya ALLAH yabiya buk'ata duniya da lahira.

Har bayan sallar Isha'i shiru basu dawo ba, taja tsaki ranta ba dad'i abinda yake ma yaran nan yana neman wuce makad'i da rawa fa,haka Bilkisu take mata wannan iya shegen k'auri da kare in dai tayi tuwo kai bama tuwo ba ko menene in dai bata ga dama ba to baza taci ba,sai tace ita wani abu na daban take so,tana ganin ya dawo zata fara shagwa6a ita yunwa take ji Mama bata ba ta abinda take so ba...

Shi kuma sarki me Bilkisu sai yafara fad'a shifa baya so ta dinga bar mishi Megado da yunwa tunda ba ta son wannan ba sai a bata wanda take so ba? Ai Bilkisu yarinyace sai da rarrashi wata rana za ta daina,wani lokacin su shiga D'akin-girki yadafa mata abinda take so baya wuce soyayyen kwai,ko taliyar yara(indomie)ko yoghort da donut, wasu lokutan kuma yaje yasiyo musu gasassun kaji ko nama,itama mayyar naman ce haka za su zauna suci su k'oshi,shi yasa kumatu a wajenta har da na sai dawa,to ganin haka itama Walida ta ara tayafa in dai tuwo ne to baza su ciba sai dai in baya gari ta musu jan idanu shine zasu d'an tsakura su bar mata..

Ita har ga ALLAH tana ganin wannan abun idan aka d'ore a haka to za a samu matsala fa,ace kome yaro yake so sai an bashi?Haka yake so su taso su basu san babu a rayuwa ba?Wasu lokutan ko fad'a take musu sai yawani 6ata rai alamar baya son hakan duk da bai ta6a furta wa ba to amma ai labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,shi yasa ita kuma in dai Bilkisu ce za tace ayi kaza to baza tayi shi ba,kamar yanzu da tace atafi gidan Inna, tana son zuwa amma tace baza taba,shi dai Bilkisu bata laifi a wajen shi kome tayi,idan tafara mata fad'a sai yayi murmushi"haba Zaujatiii...Bilkisuna guda nawa take ne? Ai za ta bari wata rana.Toh yaushe ne wata ranar bayan kullum k'ara wayau take yi,dad'a sabawa da hakan take yi?Itace dai tun yana d'anye ake tank'warashi idan ya girma bazai tank'waru ba sai dai ya karye.

Dare ya farayi tayi tsayuwar motarshi, yashigo da Walida tayi bacci ya kwantar da ita ya koma yakulle gidan sannan yad'auko Bilkisu,ai yana kwantar da ita tafara mutstsuke idanu sai ta mik'e zaune"Baba ina sauran nama na?Naman ki yana nan kuje kuyi bacci dare yayi sai gobe za kici abinki ko? Tamak'ale kafad'a ni dai a d'akin baccinka yau zan kwana...

Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba.Sudaida tayi murmushi a ranta tana fad'in"yayi kyau... Tarik'o hannunshi"Baba a d'akin baccinka zan kwana dan ALLAH.Yagyad'a kai"yashafa kanta na ji Megadona,to maza aje a wanke baki, tatafi dagudu ta d'auko brush da maclean takawo mishi, yamatsa mata taje tayi tanata tsallan murna "yau tare da Baba zata kwana, yarik'e hannunta suka tafi. Sudaida taje takwantar da Walida ta tofeta da azkar d'in kwanciya tagama abinda za tayi tanufi d'akin.

Suna kwance tamak'alk'aleshi tak'i yin bacci tana bashi labarin yan makarantarsu da Inna dasu Kawu Aminu,tabisu da kallo Bilkisu wai lallai sai ya mata tatsuniyar d'an fulani me kiwon shanu dayaje birni.Yayi hamma yasa tafin hannun dama yarufe baki yana Isti'aza"ni dai gaskiya ban iya wannan tatsuniyar ba Megadona,dan ban san abinda yayi a birni ba. Takyalkyale da dariya tana d'an bud'e idanu dan mamaki" Baba ba kace Innace Mamanka ba? Yakalleta da kulawa"eh Bilkisu itace Mamana.Yad'an yamutsa fuska"amma bata baka labari ba?To gobe zan rakaka wajenta sai tabaka labari ai muma ita take take bamu labari,har fa da tatsuniyar gizo da k'ok'i. Sudaida tace"Bilkisu surutun ya isa tashi kije ki kwanta...Julaibib yatari numfashinta"kyale ta bata jin bacci ko Megadona?Tagyad'a kai a shagwa6e"ai haka takeyi idan ba kanan wai muje mukwanta.Haushinsu yakamata kawai sai tajuya"dan ALLAH ku kwana kuna hira.

Sak'onshi yashigo wayarta"Zaujatiii... Kar kiyi bacci fa...ina lalla6atane.Takashe wayar tayi kwanciyarta"kai ka sani.Sai da baccin Bilkisu yayi ni sa sannan yabita...yakunna fitilar wayarshi yana haske mata fuska,tasa hannu takare fuskarta sannan ta bud'e idanu"Zaujatiii baki ga sak'ona bane? Na gani. Tafad'a a taik'aice...Sudaida ta kin fahimce ni amma kika share ni kina ji Bilkisu ta tasani agaba.Tadad'a gyara rufa"uh ai duk a cikin lokacin tane, yaushe ko za a bar ranta ya6aci sarauniya me D'ansarai.Yad'an daki bayanta yana matsa mata hannu a hankali"yau haka kike jin fad'ar sunan nawa D'ansarai gatsau ba ko sakayawa?Tayi shiru kamar ba da ita yake magana ba.

Yagewayeta"to gani na zo a bani bashi na... duk da ranta a 6ace yake amma bata hanashi abinda yake so ba...shima ya fahimci haka shi yasa yake jinta wata ta musamman a sararin zuciyarshi, Sudaida ba dama ne wallahi,ta gama lak'antar shi,a cikin ruwan sanyi take hukunta shi sai yazo yana bata hak'uri da bakin shi dan a zauna lafiya...Yawani narke kamar k'aramin yaro"Zaujatiii... Ina k'aunarki fa I can't do without you.Batace kome ba tacigaba da bashi wasu sak'onni sai shima ya biyema yarima su sha kid'a...

A safiyar asabar yara sun sami hutun makaranta Sudaida tamatsa sai sun tafi Zonkwa dan watanninsu biyu basu je,tagama shirinta tsafff sannan tashiga d'akin...baki bud'e take kallansu da mad'aukakin mamaki baccinsu sukeyi hankali kwance ya lull6esu da bargo,tun d'azu fa tahad'a ruwan wanka za ta musu yace tabari zai musu taje tahad'a musu abinda za suci suna gamawa sai tafiya amma shine bayan fitarta suka koma su kayi kwanciyarsu,wato sune masu idanun jin bacci ko? Tayaye bargon tana tashinsu ya bud'e idanu,ta6ata fuska "haba dan ALLAH Yaya D'ansarai kai bakiyi wankan ba,su baka musu ba?

Yaziro k'afafunshi k'asa"kin san akwai sanyi ban san sanda baccin yasake awon gaba dani ba barinje in yi...tunda yashiga wanka ta san ko ya fito bazai musu ba, dan haka tatashi Walida taje tamata sai da tagama shiryata sannan ta tashi Bilkisu tamata tad'auko shadda getzner ruwan makuba yasha aiki da zare ruwan zinare da wasu k'ananan duwatsu masu d'aukar idanu saboda kyallinsu riga da buje da d'an kwali,tana ganin kayan tawani shagwa6e fuska wai ita baza ta sa kaya irin na Walida ba wanda Baba yasiyo mata dayaje Umrah doguwar rigar larabawa shi za tasa.

Sudaida ta dafa kafad'arta da sigar rarrashi"kisa wannan kinga anko fa za kiyi ke da k'anwarki, yanzu zan miki wannan kwalliyar sai kuyi Selfie da waya ta.Walida tayi tsallan murna"Yehhh...ni ma na iya tsayuwa da shan baki a selfie,Bilkisu ta ta6e baki ita yar gata haihuwar samu sai kawai tafashe da kuka tana bubbuga k'afa ita fa dole rigar larabawan nan za a d'auko mata.Sudaida ta tsare ta da idanu"idan ban d'auko ba fa?Kawai sai ta kwanta a k'asa tana burgima tana k'ara fashewa da kuka dan ta san Julaibib zai shigo...Haushi yakama Sudaida tagyad'a kai "lallai mugun gata asara,rashin shi kwata-kwata illah...

Tanunata da yatsa"ke Bilkisu ki rufe min baki.Bilkisu tacigaba da ihu da burgima tana kiran Julaibib"Baba kazo ka d'auko min doguwar rigar larabawan daka siyo min,Mama wai bazan sa ba. Sudaida ta kifa mata mari ba za a d'auko ba... taduba yar k'aramar dorinar ta take musu barazana da ita tarasa kawai sai ta jawo wayar caja tanad'e ta a hannu"baza kiyi shirun ba ko?Ga mamakinta kawai sai tagyad'a mata kai alamar eh.Ai batayi wata-wata ba shaud'a mata iya k'arfinta caraf a kan idanunshi.
Chapter 62 · 0% Book details