← Book details Fyade Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 67

Sashe 62

Fyade Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhamdulillah ido fa ya bude kullum itama A'ishah bata da Aiki sai tambayar likitocin Ya Aaryaann ,wanda a haka suke rarradhin ta tare da sanar mata Sai nan da Kwana ki uku zuwa hudu zasu hadu .

A ranan da A'isha ta cika kwanaki biyar ne Aaaryaan yasa aka saki su Haali da Bie-bie .

Kamin ya cigaba da Rayuwar sa tattare da kewar Matar sa .

Yau Alhamis tun da Safiyar ranan ya kimtsa yana karin kumallo hankali kwance don yau ne ranan da zai ga A'isha kuma su dawo rayuwa a tare ,don a yau za'a Bata sallama .

Fitowa yayi cikin shigar Cort yana
arin shiga moto ne suka yi ido biyu da Naawaaz da Aaslaam da suke kokarin shigowa .

Tsayawa yayi yana kallon su fuska babu yabo babu fallasa .

Cikin nuna farin ciki da ganin Aaryaann suka nufe shi Aaslaam na Hugging din shi tare da Cewa " miss my best friend .

Ok yace Yana cigaba da Cewa" Ya akayi me ya kawo ku?.

Ina A'isha?

Nawaaz yayi Maganan kan sa tsaye .

Wani irin kallo Aaaryaan yayi masa kamin yace " Me kake neman matata da shi .?

Laifi ne da muna yayin ta mun tambaye ta ?.

Mama ta damu tana son Ganin ta .

Pls Aaryaann ku dawo Gida .

Wani irin kallo Aaaryaan yayi masu kamin yace " Dama munce ba zamu dawo bane ?

Shiru suka yi basu kuma ce masa komai ba ,don sun lura har yanzu kishin bai sake sa ba ,bai kuma daina jin Haushin su ba .wanda sune ya kamata ma suyi masa ,amma da yake yafi su iya masifa sai cika wuya yake yi .

Shiga moton sa yayi kaman zai bar su anan sai kuma yace ku shigo Mu tafi ."
Zaune take tana duba Wani hausa Nobel da wata nurse ta aje mata .

Don yar Africa ce nurse din aiki ya kawo ta America .

Wannan yasa yasan littafin Hausa iri da kala .

Littafin MR.XXX take karantawa tana murmushi tare da yaba basirar da haza
ar Marubuciya mmnteddy , Murmushi tayi tana cewa " Wooiuuu Ai Wannan badon badon ba da nace yafi Ya Aaaryaan ,Humm wake magaanan Ma Sir Umair na littafin sexxy Boss, bare kuma Muhammad na littafin Bafullatanan Ruga .

Humm ai wannan ya wuce yanda kake zato .ko Aliyu na cikin littafin
warton manya albarka , bare kuma Umar na cikin siyasata ,Humm bare Jarumin Sojan mu Farouk na littafin Yar Aiki na .

Tana tsaka da Wannan tunanin ne taji an budo
ofan mai dauke da Glass ta ko ina ana shigowa .

Tsayawa tayi tana kallon su cike da mamaki .

A hankali take tuna farkon Ganin su a rayuwar ta kaman yanda suke a yanzu a haka ta gansu.

Aaryaan ,Aslaaam Nawaaz....!
#Mamanteddy.

E...
75-76
Bin su da Kallon da ta tsaya tana yi ne yasa Nawaaz cike da Tsokana yace " Kina Mamaki ne A'isha , Ai mutumin bai so mu zo ba .

Aaslaam ne yace " Kuma bayan ba shine da ita kadai ba .

Idan yana mijin ki ai mu yayyun ta ne baka isa ka hana mu zuwa inda A'isha take ba .

Dariya A'isha tasa tana cewa " Ya Nawaaz Ya Aaslaam Sannun ku da zuwa .

Inda take suka tako yayi da Nawaaz ya daura Hannun sa a saman kan ta yana
an ta
a saman Goshin ta tare da cewa " Komai naki yana lafiya .?

Babu abun dake Miki ciwo?.

Juyawa A'isha tayi da idanun ta tana kallon Inda Aaaryaan yake yana jikin Windown wurin .

Duk da yaji Kishin taba masa A'isha da yayi amma sai ya dake tare da nuna ko in kula , a karkashin zuciyar sa kuma tafasa yake yi .

Kallon Sa A'isha tayi yana sakin mata Murmushi tare da lumshe mata ido Alamun ta amsa sa .

Wannan yasa Ta Kallon Nawaaz tana cewa " Ina lafiya lau Ya Nawaaz .

Yanzu kina gani Har a duhu .?

Dariya tayi tana amsa masa da eh .

Aaslaam ne yace " Ko da An kashe hasken nan zaki Gani .?

Eh mana Ya Aaslaam ai yanzu idanuna sun koma tamkar na Jaririyar da aka haifo ta yau .

Kaga ko ma na fiku Gani da kyau .

A wannan karon ba su Aslaam kadai ba , har Aaaryaan sai da ya dara .

Mashaallh yau zamu tafi kin sani.?

Kallon Nawaaz tayi tana juyawa tare da kallon Aaslaam kamin cike da farin ciki tace " Ya Aslaam da Gaske yau zan ga Mama .?

Murmushi Aaslaam yayi yana furta " Inshallah ,yanzu zasu zo su shirya ki , sunce zaki zamana da medicated Glass na tsawon 2 to 3 month daga bisani zaki iya Cigaba da fita ko babu .

Cike da
oki tace " Sun fa
a mun tun safe.

Ok Bara yanzu Aaaryaan idan Kun shirya muna jirar ka a moto kasan daga nan direct airport zamu wuce .

Hummm Sauke Numfashi yayi don tun da suka fara maganan har suka gama bai ce komai na sai a yanzu .

Ok yayi kyau .

Fita suka yi suna bashi Wuri don yayi magana da matan sa wanda Duka a zuciyoyin su suke jin nauyi amma a haka ba tare da kowa yace ma dan uwan sa komai ba suka ci-gaba da Addu'a a zu
atan su akan Allah yayi masu zabi da Wata bayan A'isha .

Kallon Aaaryaan tayi ganin har sun fita bai motsa daga Inda yake ba , Wannan yasa ta yi masa Wani irin kallo mai tattare da nuna kewa tana cuno bakin ta gaba tare da shagwa
e fuskan ta .

Murmushi yayi mata yana takowa inda take tare da dan sunkuyowa yana kama Kuncin ta da hannayen sa biyu .

Haka zaka ba matan naka kulawa.?

Tayi masa maganan a shagwa
e tare da yi masa kallo tana kafe shi da dara-daran idanun ta wanda yasa shi tsayawa yana kasa sarrafa tunanin sa ,kallon ta yake yi yana jin sabon yanayi na bin jinin jikin shi .

Ganin yanda ya ke bin ta da kallo kaman yaga Sabon halitta yasa ta kokarin sauke
afarta kasa wanda hakan yasa shi saurin dakatar da ita yana cewa " I'm Sorry babe , kin canja kaman ba jinya kika yi ba .?

Kina Kallon madubi kuwa , kin yi kyau tamkar ba Eashha ta dana Sani ba .

Murmushi tayi tare da cuno masa
an mitsulin bakin ta tana masa Alaman kiss
.

Murmushi yayi yana kai bakin sa tare da daurawa lab
an sa akan nata yana kissing din lips
in nata a hankali .

Shigowar wani babban likita ne yasa shi janye bakin shi daga nata , yayin da Doctor din yace " Sorry for interaction Sir Aaryaann .

Bayani ya fara masa akan Sallamar A'isha a yanzu da zasu yi .

Tare da ba Wata nurse dake bayan sa medical Glass yana cewa ta sanya ma A'isha.

Murmushi A'isha tayi bayan Nurse ta sanya mata Wani eye Glass wanda zaka dauka ba medical ba ne don kyawun shi dakuma yanda ya zauna a fuskar ta .

Yayi kama dana fation , Kallon Aaryaan tayi wanda fuskar sa ne dauke da murmushi ganin yanda Glass din yayi ma idanun ta da fuskar ta kyau .

Wow.

Ya furta yana kallon ta tana saka masa Dariya don kunsan ita din dama macece mai fara'a ga Surutu anan ne suke samun matsala da Aaaryaan don shi bai iya Wannan surutun nata ba .

Kallon ta Nurse din tayi tana cewa " Wani irin shiga kike son Ayi Miki .?

Murmushi A'isha Farida tayi tana kallon Aaryaan tare da cewa" Ki tambaye sa duk wanda yace irin zaki mun .

Murmushi Nurse din tayi don sosai sun Burgeta yanda taga suna soyayya kaman su lashe juna .

Aaryaan ne ya kalli A'isha sosai kana ya kalli nurse din yana cewa "Arabian .

Ok ku Dan bamu wuri .

Juyawa duka suka yi suna barin room
in Yayin da ita kuma nurse din ke kokarin shirya A'isha cikin wani irin Black Abaya mai masifar kyau .

Kammala Shirya ta tsaf tayi tana jan Hannun ta tare da kai gaban mirror don ta kalli kan ta kamin su fita .

Ita kan A'isha ta kusa kasa gane kan ta .

Wani irin
iba tayi mai kyau farin ta na fitowa , murmushi tayi Dimples
in ta na lo
awa .

Hannun ta tasa tana gyara zaman gilashin idon ta wanda ya fadin sa ta sauka irin na zamani ba siriri ba .

Wow thank you nurse .

Ai wannan Aiki na ne wajibi akan ki .

A tare suka fito suna barin Dakin , tun daga nesa Aaaryaan ya Hango su yanda Kasan balarabiya haka A'isha ta koma .

Kasa motsi yayi yana godiya ma Allah da ya mallaka masa A'isha Farida a matsayin mata .

Har suka iso Gaban sa bai ankara ba sai da A'isha ta kama hannun sa tana hura masa iska huuuuuu .

Murmushi yayi itama tana Dariya .

Juyawa yayi yana ma nurse din godiya kana ya Rungumo ta a tare suka fara bin lifta suna sauka Izuwa Farfajiyar Asibitin .

Kin koma tamkar Yar kasar larabawa kin gan ki kuwa , Mama anya zata gane ki?.

Murmushi A'isha tayi tana cewa " Uhmmm kai kuma wato Turai ne da kafarta gaba
aya ka saje dasu , kaman dama cikin su kake .

Sakin baki yayi yana kallon ta , yayin da ta she
e da dariya tana cewa " Muje fa Su Ya Aaslaam na jirar mu .

Kaiwa da komowa mama keyi a tsakanin Falon ta zuwa Upstairs .

Hajiya Kaka kuwa a falo ta zauna tana jirar shigowan yan jikokin nata .

Hajiya Lubnah murmushi take yi tana cewa " Na
osa naga da Wani ido mara kunyar yaron nan zai kalle mu.?

Wane ?

Aaryaan Ai ba ruwa a idanun sa ,firfirfir zai kalle mu ku tsaya su shigo ai Daddy yace " Nan da Mintuna Goma sha biyar zasu
ariko don sun sauka .

Wani irin dogon Dinning Table ne shake da cimma kala
.
Chapter 62 · 0% Book details