← Book details Fyade Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 67

Sashe 30

Fyade Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bin ta yayi da Lulun idanun sa kaman mai mata kallon
urulla , sai kuma yayi Murmushi yana tashi daga Zaunen tare da kallon Inna Hansai yana cewa " In ba damuwa ina Son magana dake .

Tom Dan nan mu je ko?.

A tare suka fice daga
akin yayi da A'isha Farida tayi Saurin matsawa kusa da Mama Lantana tana cewa " Mama kin gane shi kuwa?.

Murmushi Mama Lantana tayi tana gya
a Mata Kai .

Mama To A yanzu Meye mafitan mu?.

Gidan Baba na zaki koma Ko kuma Gidan Daddyn Aaaryaan?.
angaren Hajiya Kubrah kuwa Ana Wannan Tsaka da Faruwar wannan Al'amarin ne Marshal Abdu Kareem ya iso Gidan , dai dai yana shiga Hajiya Lubnah na kokarin Barin cikin gidan .

Tsayawa Yayi yana jin na bakin ta tare da mamakin faruwar Al'amarin .

Cikin wani irin murya yake fadin " Aaaryaan yana Wurin a lokacin faruwar Al'amarin kuwa?.

Amsa Momy Lubnah ta basa da cewa " Eh yana Wurin .

Amma yanzu Kuma Ban san a inda yake ba , hankali na a tashe yake , ban san inda ya nufa ba a halin yanzu .

Shiru Daddy yayi na yan mintuna kana taga yayi Murmushi irin tasu ta manya kamin daga bisani yace " Kar ki tada Hankalin ki , a ko ina Aaaryaan yake a halin yanzu baya Wuce dayan biyu.

Ko yana neman mahaifiyar sa ko kuma a yanzu haka yana tare da Hadiza .

Shiru Mommy Kubrah tayi tana Goge
wallahn idanun ta ,kamin tace " To Allah yasa ."
Rahmatu kuwa sai da tayi kwana uku a jejin nan sannan boka ya sallame ta , tare da cewa " aiki anyi an gama tun ranan da ta kawo kanta.

Jiki babu kwari tamkar an mata duka ta koma Gidan mijin ta , Wanda Tsawon kwana ki uku suke neman ta , har an fara sakawa a tv da wurare.

A Farfajiyar gidan ta ne ta fara Ganin Jiri dai dai Kishiyar ta na fitowa wanda ta zama da ita da banza a wurin mijin babu Maraba.

Hajiya ...!

Ke ce?

Yaushe kika dawo..?

Daga Jeji nake.?

Rahmatu ta bata amsa a buge tamkar mashayiya....Jeji kuma Hajiya?.

Eh Daga nan Nake Uwar ki zaki mun ko uban ki?.

Shiru Hansa'u tayi tana kama bakin ta don tasan bata da Karfi a cikin gidan , Don a kwanaki da tanemi kwatar yan cin ta , budan bakin mijin nata cewa yayi tabi Rahmatu su zauna lafiya , Amma ta nemi Yin sa
ani da ita to zai sallame ta daga Gidan shi , wannan yasa Hansa'u duk Wani cin kashin da Rahmatu zata yi mata take dannewa ta rabu da ita .

Ita dai kullum tana kai kukan ta ga mahalicci .

Allah ya baki Ha
uri Abin da Hansa'u tace kenan tare da Ra
ata tana wucewa , itama Rahmatu na nufar
akin ta .

Bayan tafiyar Rahmatu ne Hansa'u tayi shiru tana tunanin irin zaman da take da mijin ta , Rabon ta da kwana a dakin mijin ta su hada shimfi
a tafi shekaru goma .

Girgiza Kai tayi tana jajanta ma kanta kamin ta kalli
asa .

Saurin
arikawa Wurin tayi ganin Wasu irin tsutsotsi dake bin
asa Farare .

Ikon Allah me ya kawo Wannan Abin kuma nan ?.

Sani...!

Ta kwa
a Kirar Sani mai ba flowers Ruwa .

Cikin Azama Sani ya
ariko kana tace " Me yakawo Tsutsa wurin nan .?

Saurin kallon inda take nuna masa yayi ganin wasu irin tsutsotsi masu tsawo da bai taba Ganin irin su ba .

Ikon Allah Hajiya Ai Wannan Abin mamaki ne kwarai .Wallahi ban sani ba .

Ok to a gyara wurin da Sauri Don Allah .

An gama Ranki Yada
e .

Juyawa tayi jikin ta na mata Nauyi don fiye da shekaru a haka take cikin ciwon jiki da na kai ,kullum a mariranci take .

Kallon Inna Hansai Aaryaan yayi kamin yace " Inna Don Allah ki fa
a mun Wacece A'isha Farida?

Mama ce ta haife ta ko kuwa?.

Girgiza Kai Inna Hansai tayi tare da cewa " Aaaryaan tun da ka matsa Zan fa
a maka Gaskiya wanda ko ita A'isha ba tasani ba...A'isha ba Lantana ce ta haife ta ba .

Hasali tsintar ta tayi nan take Inna Hansai ta bashi labarin komai na Rayuwar Mama Lantana da kuma A'isha Farida har da labarin
oyayyen masoyi wanda ta
are da cewa " Ta dauki Soyayya ta daura mawa Aljani , Dalilin da yasa na fa
a maka Wannan Sirrin shine ko bayan Ranmu don Allah ka dauki A'isha Yar uwar ka ,kar ka bari wani Abu ya same ta ,ka kula da ita tamkar yanda mukayi mata a rayuwa ko ma fiye .

Shiru yayi yana juya maganan nata kan sa na masa zafi .

Inna inshallah nayi Miki alkawarin kulawa da A'isha har
arshen Rayuwa ta .

Nufar
akin Mama Lantana suka yi dai dai A'isha na fitowa daga Dakin ...ke koma ki saka hijab yanzu zamu bar Gidan nan .!

Wani irin kallo tayi masa cikin sauri tana kallon Mama Lantana wanda kamin tayi magana Mama Lantana tace ' Babu inda zamu je Aaryaan ,Ni da Gidan mahaifin ka har Abada .

Mama ..!

Ya isa ta katse shi tana daga masa hannu .

Ganin haka yasa A'isha ra
a shi tana ficewa tare da
aukar buta tana nufar ban
aki.

Tun kan ta isa ban
akin idanun ta suka fara zubda Zafafan Hawaye .

Don duk Maganan da Inna Hansai suka yi da Aaryaann taji , A kunnen ta ,don a lokacin ce mawa Mama tayi zata dauki buta a waje daga Hakan ne ta ji maganganun da Inna Hansai ke fada masa .

Wanda ko mafarki bata ta
a tunanin ita din tsintacciya bace ba sai a yau .

Kuka take sosai tamkar ranta zai fita .

Kamin ta fara magana kaman zautacciya tana cewa " ina iyaye na suke?

Me nayi masu suka Wula
anta mun Rayuwa?

Kuma suka so rabani da Rayuwar bayan Wula
anta Ni da suka yi har suka so kuma kashe Ni?.

Ni yar zina ce ko kuma mene sanadin Faruwar haka?

A iya sanina Wanda aka haife su a hanyar da bata Allah ba sune ake Wurgarwa a hanya walau su rayu ko kuma su mutu .

Kusan mintuna Goma sha biyar ta diba a hakan tana tunanin Abubuwa mabanbanta abun kaman Almara take ganin sa .

Kamar kuma a mafarki .

Bayan ta gama kukan ta ne ta goge Hawayen ta tana dauka ma kanta alkawarin ba zata ta
a fa
a mawa Mama Taji komai ba ko tasan gaskiyar ita ba mahaifiyar ta bace .

Wanke fuskar ta tayi tana fitowa tare da
aura Alwala .

Bayan ta shiga Dakin ne ta tadda har a lokacin rarrashin Mama Lantana Aaaryaan keyi ,anan kuma Taji yana cewa" Mama Ba a gidan Daddy zan kai ku ba , Gida na na Asokoro ne zan kai ku .

Kallon Mama Lantana A'isha Farida tayi tare da cewa " Mama Kiyi Ha
uri mu bishi Don Allah ,Kinga ya dade bai ganki a rayuwa bai ma sanki ba , Ki bashi lokacin nan a wannan karon ki taimaka masa ki zauna tare dashi , ko ba komai zaice ya zauna tare da mahaifiyar sa kaman sauran
Inna Hansai ne ta amshe da kwarai kuwa wannan Haka yake , Don Allah Lantana ki duba .

Shiru Mama Lantana tayi na yan dakiku kamin daga bisani tace " A'isha Kin amince zaki zauna da Aaaryaan muje Gidan sa mu zauna?.

Murmushi A'isha Farida tayi tare da cewa " Eh Mama zan So hakan Sosai .

Murmushi duka suka yi kamin Inna Hansai tace " To ai sai a fara kimtsawa tun yanzu .

Bu
e baki mama Lantana tayi zata yi magana karar Wayar sa ya katse ta .

Daga kirar yayi yana Saurin ficewa daga Dakin Ganin sunan Daddy...don Hajiya Kaka na can Hankali a tashe ta tasa su tana kuka tare da cewa duk inda Hadiza take a nemo mata ita .
angaren Hajiya Kubrah kuwa Ita dai Duk idan ta zauna babu sunan da take ji ana kira mata Sai sunan Hadiza wannan yasata
aga Waya tana kara kirar Ramatu don kwana uku kenan yau bata samun ta .

Hamdala tayi jin Wayar nata na ringing wanda bugu biyu ta
auka .

Ramatu ke wata irin shashasha ce?

Wani irin matsala kike so ki saka Ni a ciki , yanzu haka Hadiza tana tare da Aaaryaan tsawon kwana biyu kenan a gidan dake Asokoro.

Ahu'uhhhh Taji Muryar Hadiza tana fa
in haka , yayin da Hadiza ke tsalle don jin Wani irin abu na tsungulun takashin ta da Gaban ta yake yi...wanda tsawon kwana biyu ta kasa Ko da Wanka bare ta duba jikin ta .

Sai mintsini kawai take ji ta ko ina .

Sakin Wayar tayi
asa jin Wani irin mintsinan ta da ake yi ta ko ina .

Wannan yasa ta Saurin
asa da Zanin Jikin ta.

Wani irin uban ihu ta kwarma Ganin tsutsotsi daddabe suna bin Zanin da cinyoyin ta .

Tsalle ta hau tana ihu tare da fitowa daga Bedroom
in nata tana nufo falon ta cikin ficewar Hayyaci ta nufi Farfajiyar gidan a Tsirara sai tsutsotsi da suka yi mata rumfa suka zama mata zani .
ashi Allah yasa muyi karshe me kyau....!
#MAMANTEDDY
E ....!
#Romantic
#Erotic
#Symphatetic
#Story.

WRITTEN BY: MAMANTEDDY
*Littafin f
e na ku
i ne Regular group
500...

Vip group
1000 SPC
1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
23
*Vip& Special night update*
Innalillahi wainna ilaihir raji'un Kalmar da Sauran ma'aikatan suka hau fa
i kenan ." Hankulan su a tashe wasu na yin baya suna darewa Ganin Yanda Wannan halittu suke yayyame a jikin Hajiya Ramatu .

Mata biyu ne masu dauriyar Hali suka nufi inda Rahmatu take cikin Sauri suna fadin Hajiya Lafiya.?

Daya daga cikin su kuwa cikin sauri ta fice Kallabin ta tana
aurawa a
ugu zuwa cinyoyin Hajiya Ramatu wanda ko karamin yaro ya ganta yasan mahaukaciya ce tuburan .
Chapter 30 · 0% Book details