← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 43

Sashe 8

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bintu ta ambata idanu waje.

"Sosai kuwa dan kawai yanzu Uncle ya saka mata doka ne mai tsauri shi yasa ta daina amma ko 'ya'yan bata barinsu Shan iska da bala'inta."

"Ikon Allah amma in haka ne Aunty Nafisa ta fiye fad'a tare da saurin hannu."

"Kema kya dai dawo rakiyarta domin ni ce zan bada shaidan haka saboda har yanzu bayana da shedan dukanta."

Dik shiru sukayi suna kallon Beebah domin sun tuno lokacin da abin ya faru.

Numfashi na sauke a hankali idanuna kulle domin magan-ganun nasu ya isheni saboda bana son kojin sunar Aunty Nafisa balle labarin muguntarta. Jin sun cigaba da tattauna zancenta sai na haye katifana na juya musu baya cikin fatar samun barci ya d'aukeni. Ba jimawa Mama ta shigo ta sanar musu da sutafi gida dare yasomayi, sallama sukayi mata tare da yimin addu'ar samun lafiya suka fice.

Jin fitarsu na tashi zaune na tsirawa yatsuna ido ina jin kwallah na cikomin.

"Aunty Nafisa bakiyi ba wallahi, Uncle Muhseen bakayi dacen mata ba, Allah ya had'aka da ta gari."

"Amin ya rabbi, wata k'ilama kece."

Kallon k'ofa na yi idanu waje, Beebah ce tsaye ta sakarmin murmushi tare da k'arasa shigowa ta zauna gefena ta ce "Nadawo in kwana da patient d'ita ce."

Kauda kai nayi ina hasko rashin tabbaci akan zance ta.

"Hak'ik'a abinda na fad'a bashi ne dalilin dawowata ba, sanin dalilin da ya saka Aunty Nafisa ta k'ona ki ya dawo da ni dafatan zaki sanarmin da gaskiya ba dan na isa ba sai girman Allah."

"Waya sanar miki da cewa ita ce ta k'ona ni?"

"Babu kowa amma na rantse da girman Allah ko kaffara bazanyi ba ita ce sanadin k'onewar yatsun k'afafunki, in kuma ba ita bace kema ki rantse da girman Allah kamar yarda na yi."

"Ita ce, shi kenan kin samu amsan?"

Na ambata da sauri cikin kauda kai gefe.

"No, ina son sanin dalilin faruwar hakan daga nan ni kuma zan sanar miki da abinda na hasko har ya janyo afkuwan lamarin."

Tsirawa Beebah idanu na yi na wasu dak'ik'u, ita kam sai dokamin murmushi ta ke yi, zuwa can na sauke numfashi ta tashi ta isa bakin k'ofa ta kulle tare da tofa addu'a ta juyo muka zubawa juna idanu.

"Sanar dani sanadin Deejah."

Labari na bata daga sadda suka fice ni kuma na tafi d'ora girki har zuwa inda na farka na sami Beebah rik'e da k'afana.

"A she abinda na hasko gaskiya ne to in haka ne ina addu'ar Allah ya tabbatar da shi ko Aunty Nafisa ta yi hankali sanadin rab'arta da zakiyi, dan walalhi Allah d'abi'unki sun burgeni, musanman rashin son hayaniyarki ga uwa uba aiki da ilimi, shi yasa na ce bazanbi su Safina Kano ba zan zauna tare da ke suje su dawo ta nan sai mu wuce gida."

"Kai amma nagode da wanna k'auna."

Na ambata cike da murna matsananci, wanda naga mamakin faruwar hakan a fuskan Beebah.

"Sister Beebah dole inyi murna da ganin mace 'yar uwata a karo na biyu tun mallakan hankalina ta nunamin k'auna cikin kulawa managarci."

"Ban gane ba Deejah."

"Beebah, idan aka cire Mamana da zuri'ar Baba Umaru to Fanta ce ta farko da na had'u da ita ta k'aunace ni ba tare da yimin kallon banza ba tun mallakan hankalina a matsayin mace baliga haka ita ce ta bar abu mai mahinmanci na rayuwarta sabida ni, kamar yarda kika bar zuwa ziyara domin ki kasance tare da ni, kai wallahi nagode sosai, Allah ya faranta miki sama da wanda kika yimin."

"Amin, amma kalamanki sun sakani a duhu zan so sanin labarinki."

"Wannan a bayyane ya ke Sister."

"To ina saurarenki."

Zama na gyara tare da rungume filo sannan na soma cewa...

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/15, 4:59 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin a dona)

By Mrsjmoon

EWF.

*Shafin naki ne Dear Khadija candy  Allah ya tabbatar da nasarori a duk kan lamuranki, Amin.*

Page 05

"Gani nan kin ganni gaban Mamana da Babana sai dai ina da 'yan uba masu yawa dan haka 'ya'yan Baba mun kai ashirin da shida amma maza sunfi yawa, mata mu hudu ne kacal kuma dik sunyi aure saura ni na rage banyi ba. Baba na da gida wanda ya kasance na gado inda sauran matarsa biyu suke zaune tare da matan k'aninsa Baba Usman. Nan gidan mallakin Mamata ce domin ta sanarmin ita ta siya kayanta domin gujewa tashin hankali da abokanan zamanta.

Na taso cikin so da k'auna musanman wurin mahaifiyata sannan ba abinda na nema na rasa amatsayina ta d'iyar talakawa masu rufin asiri.

Na kasance bana da k'awa tun bayan shigata S.S 1 domin a lokacin na soma sanin ciwon kaina kuma a lokacin na soma kasancewa cikin damuwa domin dik wata k'awa ko aboki dana ke dasu a primary zuwa j.s 3 sai suka gujeni suka daina kulani batare da munyi fad'a ba, haka nan kawai suka daina yimin magana sai bisa dole, sun maidani tamkar mai d'auke da cuta, hatta da malamai da suke ji dani saboda hazak'ana sai suka koma rashin sakewa dani sai dai na rik'a kamasu suna satan kallona wanda hakan ke jefani cikin damuwa, na rik'a tunamin cutar da na ke d'auke da shi wanda jama'a suke gudun kada in shafa musu. Na kanyi kuka duk in na keb'e kaina musanman lokacin break inda zan hango 'yan ajinmu na harkokinu da juna amma ni a ware gefe kamar mayya.

A cikin wannan hali na kammala secondary school bana da k'awa ko aboki sai wanda karatu ya had'amu ko wanda suke cewa na koya musu abinda basu fahimta ba, suma basa yarda muyi hira ta nishad'i, iyakata dasu yimusu bayani abinda basu gane in nagama suyimin godiya su tafi.

Faruwar hakan ya k'ara sanyawa na zamo mara son magana da haniya dukda dama can ina da kayana amma rashin rayuwa da k'awa ko aboki ya taimaka ainun wurin mai dani miskila domin ko a cikin unguwa bana da k'awa, ako da yaushe zaki ganni ni kad'ai ko tare da Mamana, domin hatta da 'yan uwana wanda muke uba d'aya da su basu shiga sabgata wanda wannan bai dameni ba sam saboda zaman doya da manjan da ke tsakanin mahaifanmu na tabbatar ya haifar da hakan.

Baiwata na fahimtar karatu tun daga kan na addini har zuwa na boko domin duk ajin dana shiga ni ce agaba da kowa, wannan baiwar ya taimaka sosai wurin d'aukemin yawan DAMUWATA domin duk kad'aicin da na ke ciki bai raunatamin hazak'ata ba saima sake zaburar da ni da ya yi wurin zamemin abokin d'ebe kewa.

Na shiga jami'a da burin samun sauyin rayuwa ta fannin samun k'awa ko da d'aya ce tilo domin cikar buruna samun k'awa ko aboki, sai dai anan shima bata sanja zani ba abinda na baro a secondary school da islamiyya shi ne na tarad a nan wanda zance na Jami'ar har yaso fin na can domin a nan ina fuskantan harara tare da tsaki duk in muka had'a ido da mace 'yar uwata musanman irin masu ji da kansu d'innan d'iyoyin masu fad'a aji, duk in hakan ya faru da ni murmushi na ke yi amaimakon b'ata rai hakan kuwa na tunzirasu suyi ta son na kulasu dan su tijarani a bainar jama'a ni kuma da nagane ta ke ta kensu sai na bawa banza ajiyarsu, na zame musu tamkar kurma wacce bata fahimci manufarsu ba sai dai abin na k'onamin rai.

Sai dai game da samari wannan fannin ina samun sassauci domin basamin mugun kallo sai kallo na k'urillah wanda natsaneshi ainun, wanda na ke ambatarsa da kallon hango munina domin kallo ne irin na cutarwa wanda musulinci ta yi hani da shi domin ina muzanta duk in naci karo da sunayimin sannan takaicin bazasu tab'a yimin magana ba sai isata da kallo, na kansamu wasu su rakani da murmushi wasu kuma kallon ne tsabarsa kamar tsoffin mayu.

Duk wannan Damuwar da na ke ciki na kad'aici ban zauna na sanar da Mamana ba saboda na san tafi ni Damuwa da DAMUWATA ma'ana in har na sanar mata zatafini shiga damuwa sannan idan na dawo gida tana bani lokacinta wanda ya ke wankemin Damuwar da na d'ebo a waje. Mamana itace ta zamemin k'awa, abokiyar d'emin kewar rashin k'awaye da dukkan budurwa ke burin samunsu a rayuwa.

Sadda Fanta ta shigo rayuwata sai na kuma samun k'awa abokiya ta gari duk da tasha wuya kafin insoma kulata wanda mukan had'u a hanyar zuwa islamiyya da Tahfiz, ta yi ta jana da hira ina amsawa cikin rashin sakewa har a k'arshe muka d'inke gam kamar yarda kika gani.

Lokacin dana fahimci Fanta nayimin k'auna wanda na rasa abaya wato k'awa na shiga nishad'i ainun, wanda a dalilin hakan yasa na sanar da Mama dukkan DAMUWATA tun daga lokacin dana soma fuskantan rashin abokan mu'alama a waje da makaranta sai dai abin da na ke gudu shi yafaru domin Mama tashiga damuwa inda ta d'auki kwanaki tana maganar lamarin wanda na yi danasanin sanar da ita domin ban cika son mai-maita zance ba, idan abu ya wuce to ya wuce kenan a gareni.
Chapter 8 · 0% Book details