Sashe 2
Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Najiyo sautin kiran da Baba ya kwallamin da k'arfi, ban samu amsawa ba ya kuma kwad'amin wani kiran da yafi na farkon k'ara, da sauri na fito ina hard'ewa.
"Dan Uwarki ki amsamin kinfi k'arfi?"
"Kayi hak'uri Baba."
"Dalla rufemin baki sokuwa kawai wacce bak'in jini ya k'are akanta ba mashin-shini, ai wallahi sai kin tsufa a gaban Uwarki ba aure tunda ta zab'i b'atamin rai a kanki."
Wani kuka ne ya zomin domin na tsani a hantareni, dik da na nasaba da hantarar Baba hakan baisa ya zamemin jiki ba dan kullum ya tozaratani sai na zubda jirwaye.
"Au ban ci Ubanki ba kikemin kuka sabida Hurera ta gama sangartaki?"
Matsawa gefa na yi da sauri saboda nasan yanzu zai iya kawomin duka.
"Tashi ki wanke wake alale nakeson karyawa da shi yau saura kuma ki tsaya sanyin jikin nan da kika kwaso a can duniya dan Hurera kam ita macece mai zafin jini."
Tashi na yi ina cigaba da kuka mara sauti.
"Uhm ko da ya ke meye gamin kifi da kaska da za...
"Ya isheka haka nan Malam, maza tafi Uwata kije ki kwanta dan ina jiyowa a jikina barcin nan bai isheki ba."
"Mama aiki zanyi in na gama sai in kwanta "
"Na ce ki tafi zanyi masa dik abinda ya keso domin samun ladar aure."
Ban sa ke magana ba na bar wurin amma ba d'aki na koma ba kamar yarda Mama ta umurceni, wake na tafi na d'ebo na jik'a na d'auka na koma can wurin rijiya sabida bana son jin zancen da su Mama zasuyi wanda bana dad'i ba ne kuma nasan duk a kaina ne.
"Wallahi bana son wannan takun sak'ar da sukeyi sabida ni, anya zan gama lafiya kuwa idan har ban kawo k'arshen samun sab'anin mahaifana a kaina ba? Tabbas dole na san abinyi dan kawo k'arshen rashin jituwarsu ta sanadina."
Ina wanke waken sai sabbatu na ke yi cikin muryan kuka domin ta wannan haryar nafi jin dad'in amayar da dukkan DAMUWATA.
****
Malam na sha gayamaka bana son abinda kakeyiwa Uwata, raina na b'aci ainun, wallahi duk in ka tozarta Uwata ji na ke tamkar ni kake tozartawa afakaice saboda baka tashi zaginta sai in munsami sab'ani."
"Au Allah."
"Eh, ina jin zafin abin matuk'a."
"To yanzu kika fara ji kuwa."
"Malam kenan, wallahi Allah kaji rantsuwar d'an musulmi, inda ace igiyar aure nan a hannuna ya ke na rantse da girman Allah da tuni na sallameka na huta da ganin tashin hankalin Uwata ta dalilinka."
"Duk sabida na tab'a Uwani kike yimin wannan kalaman Hurera? Shin ke da Uwani ina ce duka mallakina ne?
"Naka ne amma sai ka gyara mu'amalanka da ita sannan zan amince da kalamanka."
"Ya yi kyau Hurera, zan d'au mataki na k'arshe in Allah yaso."
"Malam tafi ka cigaba da laziminka kafin ka fito na tabbata Uwata ta gama alalen."
Mama ta sauya zancen domin tasan nacin mijinta, sam bai gajiya da ririta zance. Shi kam jifarta kawai ya ke yi da mugun kallo ba tare da ya sake yin magana ba.
Aikam kafin ya furta kalma ta bar masa wurin zuwa d'akin tumakanta ta janyo wacce maciji ya halaka daren jiya ta fito da ita waje ta koma d'akinta ba jima tafito rik'e da mayafi ta dubi Baba da ke tsaye har lokacin na harare-harare ta ce "Zan lek'a gidan Malam Habu mai macizai dan yazo ya ciremana kada ya dawo daga baya ya illatamu."
Bai tanka ba itama bata jira amsawarsa ba ta fice, tana shigewa zaure ya gyad'a kai cikin jan k'wata ya shige d'aki a fusace.
***
Kafin k'arfe Takwas da rabi na kammala dafa Alalen itama Mama ta gama dama kunun tsamiya tana soya fanke saboda Bata cin Alale dan yana b'ata mata ciki. Muna gama karyawa Malam Habu ya iso cikin mintoci goma da shigowarsa ya kama macijin kato da shi, duk tsoro ya maga cikani dan yinin ranar manne da Mama na yi domin Baba ya koma d'ayan gidansa sai na sami sakewa na yi ta zuba mata shagwaba tamkar k'aramar yarinya, ita kuwa ta yi ta biyemin tare da bani labarai masu saka nishad'i.
Ni da Mamana aminan juna ne DAMUWATA na ta ne haka nima damuwarta nawa ce.
A ranar Mama ta sanya aka cire k'ofar d'akina da aka karya aka sanja wani mai k'arfi tare da inganci sannan ta sanya aka soma ginamin k'amin bayi na wanka ta waje wanda za'a shigo da shi cikin d'akina. Da yake ta saki kud'i kafin yamma angama ginin floor da sauran gyaran bayi ya rage wanda suka ce washe gari zasuzo su k'arasa.
Washe suka dawo suka kammla komi bayina k'arami mai kyau dan har da tayis aka sakamin a k'asa da jikin bango tare da yimin cabinet na ajiye kayan wanka. Iya farin ciki nayisa, k'awata Fanta na ta tsalle tare da janyoni wai sai na taka rawa ni kuma ban iya rawa ba sam, Mama na gefe sai dariya ta ke yi mana ganin yarda Fanta ta dage tana ta kwasan rawa wai Mama ta maidani yar gayu, kuma Abin k'arin farin ciki har aka gama aikin nan Baba bai lek'o mu ba, faruwar hakan yafi komi farantamin rai sama da ginin bayin, rashin sanya Babana a ido yafimin kwanciyar hankali da samun natsuwar ruhi dan ko Mama na fahimci tafi sakewa idan bai ziyarcemu ba.
Sanjamin k'ofa ya bani damar samun barci cikin natsuwa batare da fargaban komi ba, damuwata ya zamo tarihi indai akan gadin kaina ne yayin da d'aukakin bil'adam ke samun hutu wato cikin dare. Sannan na lura Mama ta sanya ido a game da shiga da fitar masu kawo mana ziyara musanman 'yan samarin unguwarmu masu shigowa siyan Zob'o da kunun Aya wanda ta ke yinsa duk ranakun Litini da Labara dan takance jiki da jini Uwata dole mu huta tunda Allah ya bamu rufin asiri dai-dai misali. Duk in ta ambaci haka na kanyi murmushi.
Hak'ik'a Mama jarumar uwa ce mai kula da kiyon da Allah ya bata akan 'ya'yansu, shi yasa alfaharina da ita ba mai musaltuwa ba ne, abinda na sani dai ina k'aunar farin cikinta matuk'ar k'auna.
Bayan sati biyu.
Sai murmushi na ke dokawa Mama na gefena tana dura kunun Aya a robobi. Ina lura da kallon da ta ke saukemin na son jin abinda ke sanyani murmushi amma dai bata tofa ba, sai lamarin ya k'ara sakani nishad'i na yi ta doka murmushina tare da motsa kai lokaci zuwa lokaci tamkar mai sauraren wak'a. Ba komi ne ya sanyani farin ciki nan ba sai ganin mun sami sati biyu cif Baba bai zo gidanmu ba wanda muka sami labarin wai ya yi tafiya zuwa maiduguri ta'aziyyar Malaminsa da ya rasu ta bakin babban yayanmu Auwalu.
'Allah yasa ya yi wata biyuma a can mu huta da sababinsa.'
Na ambata cikin raina ina mai cigaba da murza Fulawa wanda zanyi meetpie sabida bikin yayen Haddar alqur'anin aminiyata Fanta da za'a yi ranar Asabar.
"Uwata ko na samu suriki ne?"
Da sauri na kalli Mama ta motsa kai cikin murmushi tare da cewa "Ina burin jin wani yazo sallama da Uwata, ko nima na jiyo k'amshin samun jika na yi ta masu tawai."
Samun kaina na yi da rashin jin dad'i, sai na maida kaina k'asa hawaye na taruwamin domin abu kad'an ke sakani kuka.
"Uwata ka da ki damu komi lokaci ne, wata rana sai labari, wasa na ke yi miki amma ina son sanin abinda kike nazartawa da ya sakaki nishad'i."
Numfashi na sauke cikin rawar murya na soma maganar abinda ke cin raina kullum. "Mama na soma tsorata da lamarin, yanzufa shekaruna ashirin da hud'u zan shiga da biyar watan gobe amma ko da wasa wani namiji bai tab'a cewa yana sona ba hatta da k'awaye in aka cire Fanta ba wacce ke k'awance da ni, hakik'a zuwa yanzu na'amince maganar Baba gaskiya ne ni d'in mai bak'in jini ce na k'arshe."
"Kul! Uwata kada ki sake ambatar haka in baso kike kiyiwa Allah butulci ba, komi ya faru da bawa cikin k'addararsa ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba fa ce wanda da ya haliccesa wanda baya kuskure cikin mulkinsa, jalala da buwayarsa masu fad'i ne wanda sanin hak'ik'aninsu sai shi kad'ai dan haka bai manta da ke ba yana sane da ke in lokacin zuwar mijinki ya yi zaki had'u da abokin rayuwarki batare da zatonmu ba."
"Haka ne Mama amma fa ki duba ki gani Khamila k'anwan bayata ce sosai dan kince na bata shekaru bakwai amma gashi saura watanni bikinta ni kuwa ko wanda zaice ina son ki Kha...
Sai kuma na kasa k'arasawa sabida ni d'in mai yawan jin kunya ce.
"Ina Uwata ta ke?"
"Gani Mamana."
"Maza bani hankalinki."
"To."
"Ina son ki nemi zab'in Allah sai kiga Allah ya kawo miki miji d'aya tamkar da dubu ba yawan damuwa ba domin ba zai k'areki da komi ba sai shiga matsala sannan miji irin na Khamila wake burin d'iyarsa ta auri irinsa? Wanda kowa ya shaida baida halin kirki yawo da wuk'a yakeyi, me za'ayi da makashin mutane da tare hanya ya kwace musu hak'k'insu, insha Allah mijinki sai yazamo alfaharin dangi gabas da yamma kudi da arewa, wanna shi ne addu'ar da na ke yi miki duk in na kai goshina k'asa."
"Ba Amin ba!, har abada ita da samun mijin da kikeyi mata fata wannan a rubuce yake."
A razane muka kalli k'ofar shigowa, bakin Mama na rawa ta ce "Malam!"
"Na'am Hurera."
"Shin kai wani irin Uba ne?"
"Uba kuma?"
Mik'ewa Mama ta yi ta shige d'akinta da sauri batare da ta amsa masa ba, rufa mata baya ya yi yana gyara babban rigarsa cike da fitina.
Gabana ne ya fad'i na dafe kaina da ke barazanar rabewa biyu domin yin ido biyu da Baba ya d'aukemin farin cikin da na wayi gari da shi, cikin k'arfin hali na k'arasa mulmula meetpie d'in na tashi zuwa d'akina ina hard'ewa amma jiyo muryan Mama cikin kuka yasa na dakata a bakin k'ofarta, samun kaina nayi da yi musu lab'e abinda ya zamo bak'on lamari daga cikin halayyana.
*Ya kukaji Fans? Shin Labarin zai kayatar da ku kuwa?*
*TALLA.*