← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 43

Sashe 30

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ambata tare da mik'ewa ya k'ara fesa turare, ya fito ya sami Hajiya ya russuna cikin tarbiyya ya yi mata sallama ta rakashi da addu'ar dawowa lafiya.

Tafe suke a Napep sai runtse ido ya keyi saboda yarda keken ke motsi yana jin inda ya bugu na yi masa zafi.

"Sannu Yaya, jikin ko?"

Da kai ya masa yana cije lips.

"Ba dan soyayya ba na tabbata ba mai fito da kai waje ko zuwa gobe ne saboda son jikinka ko mace albarka."

"Kin raina ni ko Salma?"

"Sorry big Brother."

"Idan kinga Mall mu tsaya asiya musu wani abu."

Ya ambata tare da kulle ido.

"To mijin Khadija."

Kunninta ya ja ta k'ank'ame hannunsa cikin yin k'ara.

"Idan mun koma gida ki tanadi abin fad'awa Hajiya domin ba ruwana ban san inda kikaje ba."

"Bakomi zanyi mata bayanin gaida maman surikarta mukaje."

"Da na yanke bakinki kuwa."

"Wai Yaya me yasa bazaka sanar mata da ka samu Mata ba?"

"Zan sanar mata amma ba yanzu ba."

"Uhm wallahi ina guje maka samun matsala tunda gida bai...

"Idan kina son komawa gida da lafiyayyun hak'ora kada ki sake maganar Amira ya had'anu."

"Insha Allah bazan sake ba"

"Hakan ya fi Miki."

"Yaya ka...

"Keep silent Salma, surutunki ya yi yawa."

Cikin hanzari ta kulle bakinta, girgiza kai ya yi tare da lumshe ido surar Deejah na yi masa gizo.

'Ina son Khadija haka ina jin dirin k'aunarta har cikin tsokar zuciyata.'

Ya ambata cikin zuciyarsa fuskansa cike da murmushi. Salma dai idanu ta tsira masa ga magana tana son yi ba halin furtawa sai ta kuma gyara zama tana k'arewa duk kan motsinsa kallo cikin yabawa tare da addu'ar itama Allah ya had'ata da maiyi mata k'auna na hak'ik'a irin wannan.

Ajikinsa ya ji kallonsa ta ke yi ya bud'e ido ta yi hanzari kauda kai rankwashi ya sauke mata ta kyal-kyale da dariya, shina dariya lamarin ya bashi, hatta da mai Napep sai da ya dara duk da bai san abin da sukeyiwa dariya ba.

***
Aunty ga mai fruits in tsaya a siya
ne?"

Beebah ta ambata cikin kallonta ta mirror.

"Ki dai tsaya ki d'auki mai saida fruits din duka yafi"

Dariya su Bintu suka kwashe da shi.

"Kun soma haukacewa ne!?"

Nafisa ta daka musu tsawa.

Tsit sukayi, kowacce na tura baki cikin k'un-k'uni.

"Kufuto fili ku zagene da wannan na zuccun da kukeyi."

Ba wanda ya amsa mata ta ja dogon tsaki tare da cewa "Bazan siya musu komi ba wanda ya basu maula ya wadatar."

"Maula kuma?"

"Eh maula, ko kuna zaton ban san komi ba ne?"

"Baki sani ba gaskiya."

Bintuvta amsa kaitsaye.

"Uwar kini-bini to sanar da ni."

Yi ta yi tamkar bata ji ba.

Ya ja kwata cikin watsowa Beebah harara "Saura kuma inji gulman ban siya ba tare da kalman maula wallahi inci uban mutum ba mai hanani."

"Amma Aunty ba girmanki ba ne hakan, tunda Allah ya hore miki ko Uncle bai bada kudi ba ke ya kamata ki siya da naki."

Fiddausi ta ambata cikin tsare gira.

"Na ce bazan siya ba da baki kamar siyad'in!."

"Jikin ya motsa kenan."

"Wallahi Beebah zan ci k'aniyarki domin ba ki wuce in lakad'a miki duka ba kin dai san dai wacece ni, wato ga mmahaukaciya ko?"

"Uhm Aunty Nafisa kenan ni bakiji na kiraki da kalman hauka ba."

"Kina buk'atar dukan kenan?"

"Uhm gaibu."

"Zaki ramane in na bugeki?"

"Ni bance ba amma duka yanzu ai sai su Hafiz."

"Au kinfi k'arfin hukuncina kenan?"

"Ni bance ba fa."

"To me kike nufi da kalamanki?"

"Dan Allah Aunty Nafisa kiyi hak'uri tunda dai kince bazaki siya ba ai shike nan."

Safina ta ambata a hankali.

"Eh bazan siye d'in ba, munafukan banza kawai, ai wallahi da Kaka Alhaji zan had'a ku duk ya cimin k'aniyarki."

"Damu kayi miki me?"

"Kinga Safina idan kika sake yin magana wallahi sai na sumar da ke."

"Abin azimun ne."

Firdausi ta furta tana kauda kai gefe.

"Wai kuna son maidani mahaukaciya ce ko me?"

Shiru ba wanda ya tanka mata, tsaki ta ja Mai sauti, har suka iso Asibitin fad'a ta ke yi. Gyara parking Beebah ta yi ta dubi Bintu ta ce "Idan da kud'i a hannunki ki samo masu fruits a bakin gate bama shiga hannu sake ba domin ba girmanmu ba ne."

"Babu sister."

"Muje da shi a wurina."

Firdausi ta furta tare da bud'e k'ofar motar ta fice

"Wallahi kuka siyo sai na ci ubanku."

"Wai Aunty ina ruwanki ne? Ba fa kud'inki zasu tab'a ba."

"Eh ko ba nawa ba ne ai na isa in bada umurni abi."

"Idan ya kaucewa shari'a, Allah da kansa ya yi hani da bin umurnin na gaba."

"Beebah billahil azim zanci Ubanki a motarnan."

"Allah huci zuciyarki Aunty, uwar gidan Uncle mai kirki."

Tana ambata ta fice da sauri Safina ta rufa mata baya tana dariya ya yin da su Bintu suka wuce bakin gate batare da sun saurari masifar Nafisa ba.

"Wallahi yaran nan duk saina gyara muku zama ba dai ni kuke wulak'antawa kan wata banza ba, uhm ai zaku gamu da Kaka Alhaji ni kad'ai nasan tuggun da zan k'ulla muku, duk ku bar garin nan ba shiri."

Tana nan tsaye jikin mota su Bintu suka dawo. Ba suyi mata magana ba suka wuceta tamkar basu santa ba, bayansu ta bi tana zabga musu harara.

'Idan na b'atawa wanda kuke rawar k'afar nunawa k'auna sama da jininku fuska da ruwan batir ta koma dodanniya abar tsoro ga kowa ai kwa dawo hayyacinku, shegun yara kawai.'

Murmusawa ta yi cike da jin kwarin guiwar aiwatar da k'udirinta wanda shi ne dalilin zuwarta Asibitin.

***
*Baba Umaru.*

"Baba ga wata shawara akan zantukan Malam Hadi."

"Ina saurarenka Habibullah."

"Idan zaka yanke hukunci ka saurari duk bayanen kowa sannan kayi nazarin dukkansu sai ka yanke hukunci bisa tunaninka ba na wani gefe ba."

"Hakan na ke da niyyar aikatawa Habibu."

"Yawwa Baba kuma wallahi na gano rashin gaskiya a lamarin Malam Hadi."

"Habibullah kenan, wani haline na Hadi zaka tusamin da ban sanshi ba? Ai ina kallonsa ne kawai domin na gano Alhaji Muhseen yana taimakon Hurera ne shi ne ya ke bak'in ciki amma na tabbata da zarar ya manna masa kud'i zaiyi tsit kasan indai akan kud'i ne komi zai iya aikatawa."

"Allah ya shirya shi kam."

"Amin. Amma ina cikin nadamar amincewa da auren Hurera ga Hadi, aure rai ne da shi da kuma Allah na fushi da mai guntileshi amma da wallahi Hurera bata kuma zama da Hadi."

"Muyi ta binta da addu'a Baba domin aurenta ya zamo auren k'addara."

"To Allah ya iya mana dace da khairan ba dan halinmu ba."

"Amin Baba."

"Bari inje na gaida Hajiya Inna tare da sanar mata ta shirya cikin lokaci."

"To madallah hakan ya yi, ka sanar mata ta yiwa Hurera abu mai laushi da mara lafiya ke buk'ata."

"To Baban Hurera."

Dariya Baba ya sanya tare da watsowa Habibu dakuwa, shi kuwa ya fice yana dariya.

***
*Hinde da Asabe.*

Yaya nikam da zaki amince munbi Juma inda ta ke amso sa'a har ta mallake kowa na gidan ba wanda ke tsallaka kara duk in ta sanya, kinga da sai mu jefi tsun-tsu biyu da dutse d'aya, mu mallake Hurera da Malam hankali kwance in yaso in munje wurin sai mu raba ni na Mallaki Hurere ke kuma ki mallaki Malam."

"Zancen bur inji tusa. Kinga Hinde ki fita ido ko kin dawo miki Asabena ta zamanin baya."

"To Yaya me na yi kuma daga shawarar arziki sai tijara ya biyo?"

"Son kai dai shawarar arziki ba"

"Ta ina naso kan nawa?"

"Ta mallakan Hurera ni ki mannamin Malam mai mugun tsari a jikinsa, kinga garin neman gira sai in rasa ido a k'arshe na haukace yazamo kinci duniyarki da tsinke, to wallahi aniyarki ta biki, muguwar banza kawai wanda bak'in hali ya gama yiwa sutura."

"To ya isheki haka nan Yaya, kada abin ya koma cin zarafi."

" Bai isa ba, muguwar banza da wofi kawai."

"Duk mugunta na ban kama ko farcenki ba tunda ban tab'a yin kisan kai ba."

"Hinde! wa ya yi kisan kai?"

Muryan Baba ya ratso kunnuwarsu.

Tsit sukayi, ya k'arasa cike da masifa, suka ja baya ya nunosu da yatsa yana tattare babban rigarsa ya ce "Munafukai zaku sanarmin da wanda ya aikata kisan kai ko sai na maidaku b'eraye? Kun k'are a sata cikin kasuwa."

"Tsafi ka koma Malam?"

"Ke Hinde! Shiga hankalinki ko in sab'a miki matuk'ar kika nemi kawomin wargi, kindai san halina ciki da bai."

"Allah huci zuciyarka."

"Amin, maza sanarmin da wanda Asabe ta kashe tun ban mik'aku ga hukuma ba."

"Hukuma kuma?"

Asabe ta ambata idanu waje.

"Eh, in kaiku kuyi bayani a can ko ba dan Allah ba sai dan bak'ar azaba  domin sanyawa zanyi suyi muku dukan jakuna masu d'iban yashi da duwatsu."

K'iftawa Asabe ido Hinde ta yi ta karkace ta ce "Malam abinda ya faru kusan shekaru ashirin meye na son ta tado da shi?"

"Ban fahimceki ba uwar salo tamkar d'iyar marok'a."

Murmushin yaudara da cilka masa ya maka mata harara ta kuma murmusawa cikin cewa "Manufata Nuhu almajiri da ka duka har ya zamo sanadin barinsa gidan duniya shi ne muke maida zancen har na ke cewa itama tana da alhakin kisan kai tunda ita ya yiwa laifi ta sanar maka kai kuma ba bincike hau dukan...

"Dalla can rufemin baki, sokayen Mata kawai da iya janyo masifa ana zaune lafiya, maza ku kama aikin gabanku ban son munafunci da maido zancen da ya wuce sabo."

"Had'a idanu sukayi suka murmusa batare da Baba ya gansu ba.

Sab'a babban rigansa ya sake yi ya shige d'akinsa yana cewa "Gidan Hurerama zan kwana saboda b'arayi sun soma kaiwa dukiyarta hari, makwafcin kirki ta samu ya sanya makatan tsaro amma yau na koresu ni zanyi gadin dukiyar iyalina."

"Aikam ka kyauta."

Suka ambata a tare.

"Ko ban kyauta ba matsalarku ba ce, mahassada kawai, ai duk kallon munafuncinku na ke yi dan nasan komi amma duk ranar da kuka kaini bango wallahi sai kunga tijara ganin idanunku."

"Malam me mukayi mata kuma?"

"Farin ciki da ciwonta Mana."
Chapter 30 · 0% Book details