← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 43

Sashe 34

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Deejah har da ke ko?"

"A'a fa kawai dai naga ya kamata ki sani ne duk da ni fadar Abdul Abbas na ke."

Mik'ewa ta yi Bintu ta janyo hannunta ta koma zaune.

"Kinga idan kina sonshi ki bada kai muna bayanki saboda wannan gayen samunsa sai mai sa'a."

"Ban son shi, shi kenan zaku bar kunnuwana su huta?"

"Eh amma sai na sanar da Uncle kin kamu da son k'aninsa."

"Wa kenan?"

"Sa'ad."

Kama baki ta yi cikin ambatar Innalillahi.

Aikam na fashe da dariya mai sauti, su Bintu na tayani.

"Kinga k'awata ki daina dariyar nan domin baiyi miki kyau ba, gara kiyi murmushin da kika saba."

"Alamun samun natsuwar ruhi kenan Fanta "

Beebah ta ambata hankalinta na kan wayarta domin ko murmushi batayi ba tun soma hirarmu.

"Wai ita nan zata layance ne ta kori zancen Sa'ad."

Fad'in Safina ckin dariya.

"Ai sai kiyi ta yi tunda kin sami karatun sallah."

"Kinga malama bamu san gulma, ko ba maganarsa kika ishemu da shi jiya ba, to zamuce Uncle ya had'a zumunci, hakan ya yi miki ko?"

Cewar Fiddausi.

"Wallahi zan kai k'ararku wurin Uncle in baku daina yimin sharri ba."

"Ya isa haka, kun cika mana kunne da hayaniya alhalin ance mu bar Deejah ta huta."

"K'yalesu Sister Beebah, lamarin na bani nishad'i ainun."

"To nikam sun dameni."

"Munyi shiru Babban Yaya."

Fiddausi ta ambata cikin murgud'a baki. Beebah ta kawoma bakin duka ta sunkuya, suka sanya dariya.

Shigowar Baba yasa duk suka natsu saboda sun sanshi yanzu sai ya korasu waje. Suna gaisar da shi ko kallo basu ishe shi ba, ya buga babban rigarsa ya nuna Mama da yatsa cikin tijararsa na fama ya ce "Hurera in na isa da ke ki tashi yanzu mu tafi gida tunda kun sami lafiya kuma in Allah ya so ba mai sake zuwa wannan matsiyacin asibitin ko da ciwon mutuwa ne ya kamaku gara ku mace ina kallonku da dai zuwa shegen Asubiti nan mai kama da na yahudawa."

"To ta Allah ba takaba ciwo da mutuwa na kan kowa kuma Asibitina ba matsiyaci ba ne balle ya zama na kafurci saidai kai ne matsiyacin, fitinannen mutum kawai, Malamin bai kaiba, wanda baisan darajar iyalinsa ba, zalaman kawai ya ajiye, mai fuska biyu kawai. Wallahi ba dan Yaya Muhseen ba da banga wanda ya isa yasa ka sake shigomin Asibiti ba."

"Jalal ban isa da kai ba ko? Shin ba na ce kada ka sake magana ba?"

"Kayi hak'uri Yaya amma wallahi wannan makwafcin naka ba dan arziki ba ne saboda na gano yana da sa hannun a ciwon matarsa har da 'yarsa, shi ne ke son kashesu lokacinsu baiyi ba."

"K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un! Ni Malam Hadi zakayiwa kazafi Likitan fanko? To wallahi bani yarda sai na d'au mataki ba dai tak'amarka jama'ar da sukeyima tururuwa ba to sai ka koma kare bai...

"Dan soyayyarka da Ma'aikin Allah Baba kada tayi masa baki, shi d'in mai taimakon al'umma ne."

Na furta cikin kuka. Kallona ya yi sai naga ya tako ya iso daf da ni cikin cewa "Uwani ke ce haka cikin k'oshin lafiya, murya ras?"

"Eh, Baba."

"To madallah, sannu fa, kin tsallake rijiya da baya domin irin wannan ba'a cika tashi da lafiya ras irin haka ba."

"Ita dai sumul ta tashi soi fatan samun kwarin jiki wanda shima zuwa anjima zata koma tamkar taba tab'a kwanciya ciwo ba."

"To Hurera da fatan kema kin gama warwarewa?"

"Alhamdulillah ala kulli halin."

"Da kyau."

Kowa sai kallon Baba ya keyi tamkar ba shi ne ke fesawa Doctor Jalal ruwan bala'i ba, ya koma kamar wanda junnu suka shafa yana masifa lokaci d'aya ya koma maganar arziki.

"Baba kayi hak'uri yarinta ce ke damun Dr. Jalal kuma bai san alak'arka marasa lafiyan ba sai yanzu amma da duk haka bata faru ba, dan Allah ya ci albarkacina ka mance lamarin ya zamo tamkar bai tab'a faruwa ba."

Uncle ya katse shirun da rarrashin Baba.

"Alhaji Muhseen ban sanka da k'arya ba amma sai gashi yau kana yimin ba kunya balle tsoron gamuwarka da mahaliccinka, yaron nan ne baisan alak'ata sa iyalina? Sai dai ka fad'awa yaron goye amma ba Abdul Hadi ba mai hak'ora talatin da biyu cik."

Wani kunya ne ya kama Uncle ganin yarda kallo ya dawo kansa sai kawai ya juya ya fice batare da ya sake furta kalma ba.

"Amma kai ba mutumin arziki ba ne, to ka sani hukuma ce zata rabani da kai ba dai haka ka ambata cewa kare ba zan sake gani a cikin Asibitina ba, ni kuma zan nuna maka ni d'in jinin malamai ne kuma wanzamai masu tutuniya da yardan Allah ba bokanci da buge-buge k'asa ba, ni Abdul Jalal sai na baka mamakin da duk wani bil'adam bai tab'a baka shi ba tsawon rayuwarka, mu zuba mugani shege ka fasa."

Dr. Jalal na gama ambatar haka ya fice a fusace.

D'akin ya Kuma yin tsit baka jin motsin komi sai sautin kukana saboda lamarin ya b'atamin rai ainun.

"Ka kyauta Hadi sai ka tafi tunda abinda kazoyi ka gama."

Kallon Hajiya Inna ya yi wacce ke zaune gefe d'aya a saman sallaya, sai ga Baba ya sunkuyar da kai domin sam bai lura da ita ba saida ta yi magana.

"Ayi hak'uri Hajiya wallahi rai na ne ya b'aci na ganin da girmana da komi masu gad'i sun hanani shigowa duba iyalina har saida na kira Alhaji Muhseen sannan suka barni na shigo sai ga wannan yaron ya tareni da zantukan banza har da zagi tare da mannamin k'azafin iska da wofi."

"Ko me ya yi maka kaika siyo da kudinka Hadi."

"To Hajiya ayi hak'uri dai."

"Ni bakayimin laifi ba amma dai zan baka shawara agame da wannan halin naka wallahi ka kiyayi furta kalamai marasa dad'i a duk yarda suka zo maka domin in kasan wani baka san wani ba sannan ik'irarinka na alkaba'i ka bari ko masifun da kake ambatawa mutane ya koma kanka."

"Insha Allah zan kiyaye."

"Allah yasa mudace."

"Amin."

"Takwarana daina kukan nan kada kanki ya yi ciwo, kinba ba gama samuwa kikayi ba."

Sakkowa na yi zuwa gaban Hajiya Inna na russuna kafin in furta kalma ta janyoni zuwa jikinta ta kai bakinta kunnina tana mai cewa "Kada ki furta komi ni ne maganin Babanki ki zuba ido kiyi kallo domin na fahimci shi d'in zuma ne shansa saida wuta."

Motsa kai na yi, ta d'ago fuskata ta soma sharemin hawaye wanda tana sharewa wasu na biyowa.

Uncle ne ya dawo ya sanar da ansallameni, su Beebah suka soma tattara kayanmu, Baba na tsaye yana kallosu takaicin Dr. Jalal da Hajiya Inna cike da ransa domin nasihar da Hajiya Inna ta yi masa ya d'aukeshi cin fuska ne ba komi ba, kawai ya bada kai ne saboda girmanta da ya ke gani.

Uncle na kalla na langab'e kai ya kirani da hannu batare da kowa ya lura ba, ya fice waje na rufa masa baya ina jin kaina tamkar zai rabe biyu.

"Khadija ina rokonki da kizo muje ki bawa Dr. Jalal hak'uri saboda in har ya sakawa Baba ido lamarin bazaiyi kyau ba dan nasan wayeshi akan 'yancinsa sannan yana da k'anin Baba wanda in ya kai sunar Baba wurinsa abin sai addu'a kawai zance."

"Dama abinda na ke son in aikata kenan Uncle, kaini na rok'eshi domin bana son Baba ya sami matsala ta sanadin zuwarmu Asibitin nan."

"Ok kinyi tunani mai kyau Iyalina."

Kauda fuska na yi saboda bana cikin good mood d'in da zanyi masa murmushi wanda na fahimci shi ya ke son gani.

Yana gaba ina binsa a hankali saboda jiri da na ke gani, muna shiga office d'in na jingina da bango sakamakon jin da na yi zan fad'i, ido na ke son bud'ewa amma sai naji sunyi min nauyi sai na hak'ura na sake rintsesu, na mik'o hannu naji an kama, Dr. Jalal na ambatar sunana a hankali saidai na kasa amsawa saboda nauyin da harshena ya yi tamkar yarda idanuna sukayi. Daga nan ban sake sanin ya akayi ba nadai farka ne na ganni kwance saman gado, d'akin ba haske sosai amma na hango Hajiya Inna zaune saman sallaya. Salati na soma yi da k'arfi na jiyo muryan Mama na kiran sunana sai dai a dushe ya ke muryan nata wanda ya tabbatarmin da kuka ne ya haifar da hakan.

"Sannu Uwata, Allah dai yasa kafface, sannu kinji, jarabawar rayuwa ce ta zo mana da sauyi mai firgitarwa."

"Yawwa Mamana, zansha ruwa."

Hajiya Inna ce ta kamani na tashi zaune, Mama ta bani ruwa nasha mai yawa na koma na kwanta ina ambaton sunar Allah Al-hamidu a cikin raina domin shi ne kad'ai ya can-canci a gode masa a dukkan halin da mumuni ya riski kansa ciki.

Cikin daren Dr. Jalal ya dubani sosai bayan ya matsamin saida na sha tea, ina gamawa ya kama hannuna na kalle shi ya motsa kai cikin cewa "Khadija rayuwarki tamkar rayuwar mutane masu yaww like Mama, Yaya Muhseen, su Hajiya Inna da ma k'awayenki su Fanta tare da al'uman Annabi irinmu masu tausayin halin da kika sami kanki ciki na rashin lafiyar jiki d'an haka na ke baki shawara da ki jajirce wurin kauda damuwa a zuciyarki, ke malama ce kin san kalolin addu'o'i na tafiyar da duk kan damuwar jiki da ruhi, to ki sanya su zamo aminan zuciyarki wurin tuno da su ta hanyar ambatarsu, kada ki sake bari damuwa ya kwantar da ke akaro na uku domin banjin zaki tashi da lafiyar tunani ba ko na jiki. Dan Allah da Manzon Allah ki bamu hadin kai aikinmu ya sami nasara, lafiya ya wadaci jiki da ruhunki baki d'aya."

"Insha Allah Doctor zanyi bakin iyawata na ganin damuwa bai yiwa rayuwata illa ba."

"Masha Allah, ina rok'on sauk'i a gareki dama duk kan masu fama da rashin lafiya."

"Amin. Nagode."

"Ki kwanta ki huta kinji?"

"Insha Allah."

Bayan fitarsa Hajiya Inna ta zo ta zauna saman kujera ta dubi Mama dake manne da ni ta ce "Hurera ku kwanta ku huta dan kema ba lafiyar ce ta isheki ba."
Chapter 34 · 0% Book details