← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 43

Sashe 41

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Why Hajiya? Kin san yarda na ke jinta a ruhina kuwa? Wallahi ba zan auri wacce kike muradi ba domin ban tab'a kallonta a matar da zan aura ba sai k'anwa."

"Zakata tabbata ba aure kenan in har baka auri d'iyar d'an uwana ba wallahi ba zanyi kaffara ba kai da aure sai in anayi a lahira sai dai kuma in zakayi ba da sa albarkana ba wannan kam sai ince na barwa duniya kai babu ni babu kai har abada."

"Hajiya me yasa kika sanja daga mai k'aunar farin cikin 'ya'yanki zuwa kishiyarsa?"

"Son k'ulla zumunci ya sanjani kuma ba zan tab'a dawowa ba dan haka zab'i ya rage ga mai shiga rijiya, walau kayimin biyayya ka auri jininka Amira ko ka band'aremin na barwa duniya kai tare da yima tofin jeka ka gani."

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un! Hajiya wai me ye haka kikeyi?"

"Idan ka gama yanke shawara ka sanarmin wallahi ba zan matsa maka sai ka so cikar burina ba amma dai ka tuna zab'i biyu na baka kuma duk wacce ka d'auka zan amsa da hannu biyu."

Tana fad'ar haka ta fice daga d'akin.

Kuka ya fashe da shi mai sauti baya ko jin kunyar k'anninsa su jiyo shi.

"Zainab!."

Ya ambata cikin kaushin murya. Wayarsa ya laliba ya doka mata kira bugu d'aya ta d'auka cikin karad'in cewa "Angon Takwara my in-law kana  lafiya?"

"Abinda kikayimin Allah ya yi miki fiye da shi, Allah ya sanyo k'unci a ruhinki sama da wanda kika jagoranci dasamin, Allah ya kawo sanadin da mijinki zai gano b'oyayyen halinki na raina masa Mahaifiya, Allah ya karya k'adarinki ki gamu da gamonki ta hanyar da bakiyi zato ba."

"Me ke damunka Aliyu?"

"Allah ya isa tsakanina da ke kuma k'anwarki ba dai taji dad'in zama da ni ba, wawiya kawai bulutu mai saka khairan da sharran."

Kafin ta sake furta kalma ya datse kiran.

Sai numfashi ya ke saukewa cikin furzar da huci, key d'in mashin nasa ya d'auka ya fice tamkar zai kifa.

Zainab kam kuka ta fashe da shi cikin durawa Aliyu zagi tamkar ba yayata ba, ganin hakan baiyi mata ba ta kira Hajiya ta rattafa mata k'arya da gaskiya.

Shiru Hajiya ta yi bata da niyyar cewa komi saboda yarda ranta ya b'aci.

"Hajiya wallahi in wani abu mara kyau ya sameni bakin Aliyu ne."

"Zaizo har gida ya baki hak'uri d'iyata, ki daina kuka insha Allah ba abinda zai sameki sai alkhairi."

"To Hajiya nagode."

"Na ce ki daina kukan nan."

"Na bari."

"Da kyau, ki shafamin kan jikalleta."

Bata amsa ba Hajiya ta kashe wayar tare da neman Aliyu aka sanar mata wayar a kashe ne. Tsaki ta ja ta cije leb'en k'asa cike da takaicin rashin samunsa.

Aliyu kam na fita gidan su Deejah ya nufa sai dai ya aika yara har uku ana dawo masa da amsar bata nan alhalin duk in ya tambayi yaran sun ganta suna amsa masa da ita ce ta ce a ce masa bata nan. Garin yaji na juya masa ya samu dakali ya zauna ya tsirawa bishiyar ced'iya da ke nesa da k'ofar gidan ido tamkar mai irga rassanta nan kuwa lulawa ya yi cikin tunani.

"Kai! Me kakeyi a nan?"

Muryan Baba ya katse masa tunani.

Firgigit ya yi tare da zubewa yana gaisheshi.

"Lafiya, daga ina?"

"Abokin karatun Khadija ne."

Ya sami kansa da furta hakan.

"Oh bari aturo maka ita dan nasan kazo gaisheta sa jiki ne ko?"

"Eh, Baba."

"To jirata."

Da idanu ya raka Baba yana zabga masa albarka a cikin ransa. Yana tsaye na fito fuska a had'e. Wawan ajiyar zuciya ya sauke ya taho da hanzari tamkar zai rungumeni na koma da baya cikin zaure da sauri ya rufa min baya, ganin zan koma cikin gida sai ya rik'o hijabina na juyo idanuna na zubar hawaye na had'e hannayena alamun rok'o na ce "Dan soyayyarka da fiyayyen halitta Aliyu ka rabu da ni rabuwa ta har abada."

"A'a Khadija, kada kiyimin haka, ruhunanmu bazasu d'auka ba dan Allah ki saurareni."

"Aliyu lamarin mahaifiya dabanne da na kowa dan haka na ke baka shawara da kayi mata biyayya tamkar yarda na yiwa tawa Mahaifiyar na tabbata zamuga haske cikin rayuwarmu."

"Khadija kin amince zaki iya rabuwa da ni?"

Shiru na yi masa saboda bakina ya yi nauyin amsawa Amma ba wai dan bazan iya amsawa da a'a ba ne sai dan ina ganin cin kuska ne na amsa masa kai tsaye.

"To ni bazan iya hak'ura da ke ba ki rubuta da k'aunarki zan koma ga mahaliccinsa."

Kuka ne ya kufcemin ganin yarda ya ke furta kalamin da iya kacin gaskiyarsa.

"Koma ciki kai kuma tafi kayiwa mahaifiyarka biyayya dama Uwani ba sa'ar aurenka ba ne Allah ne ya baka ita har ta soma kulaka sai kuma somuwar Uwarka ta yi sanadin b'ata komi saboda son zuciya."

Tsit mukayi muna kallon Baba da ya shiga tsakiyarmu ya raba tsakaninmu yana mazurai.

Hannun na d'aga masa alamun bye na shige gida da gudu shi kam zubewa gaban Baba ya yi ya ce "Baba kayi wani abu akai wallahi jna sonta, itama tana sona."

Mik'a masa hannu Baba ya yi Aliyu ya zaro idanu kai Baba ya gyad'a.

"Ban fito da kud'i ba Baba kayi hak'uri zan kawo maka."

"Zaka iya tafiya kuma wannan shi ne rana ta k'arshe da zaka sake zuwamin k'ofar gida tunda matsiyaci ne kai."

"Baba kayi hak'u...

"Kaci Uban Uwarka mataccen nan na ce kaji ko?"

Baba ya gabgowa Aliyu zagi cikin nad'e hannun riga, alamun zai bugeshi.

Da gudu Aliyu ya fito zauren ya kunna mashin d'insa ya bar unguwar amma yana jin aransa ba zai iya rabuwa da Deejah ba.

*Assalamu alaikum, 'yan uwa Barkanmu da warhaka ga wata dama ta samu mai burin dogaro da kansa. Shahararren kamfanin nan na oriflame na yin  registration kyau a wannan wata duk mai burin a dama da ita ko shi a harkan siye da siyarwa na kayan kamfanin a samu riba Mai yawa ko yin amfani da kayan domin jin dad'in rayuwa to wannan babban damace a gareku, maza ku garzayo ayi muku register kyauta kafin wata nan ta November ya k'are domin in ya k'are sai kun biya kusan 5k kafin ku samu damar zama 'yar kamfanin masu 'yanci dan haka ku taho dan zama masu 'yanci a kyauta. Domin k'arin bayani ku tuntub'i wannan number 08131166848.*
[11/7, 2:06 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Safiyya (Mrsjmoon)

E.W.F.

Page 23

"Ina uwani ta ke? To maza kizo ki bud'e kunnuwanki da kyau ki saurari kalamina akan matsiyacin yaron can."

Ina jiyo Baba daga cikin uward'akan Mama amma ban motsaba saboda wani haushin shi na ke ji duk kuwa da yarda na ke korar lamarin amma sai k'ara nitsawa ciki raina keyi. Jiyo sabon hargaginsa yasa na tashi daga kwancen da ni ke na tallabe kumatuna hawaye na cigaba da wankemin fuska tamkar an fud'e famfo.

"Narabaki da wannan matsiyacin yaron na fad'a na k'ara tabbas na rabaki da shi domin baida komi sai k'wambon banza da k'arya da ganinsa ba zai iya rik'eki ba balle har mu sami ihsani daga gare shi, d'an gidan matsiyata ne wanda ke neman cin yau babu na gobe dan haka nima ina bayan Mamanki ki fita sabgarsa ki auri mai arziki wanda zan fanshe rainonki da na yi, a yau ina bayan cikar burin Hurera wato auren mijin da ya kerewa sa'a wato d'aya tamkar da million ba dubu ba, kamar dai Alhaji Muhseen ko ma wanda ya zartashi inda darajana zai k'ara hauhawa duk inda na ratsa ayimin fad'anci tamkar basarake dan ina da suriki ishasshe wanda ya kama k'asa, gagara badau wanda arziki ya yiwa mayafi ya barranta da talauci."

"A'uzubillahi! Malam me kake ambata haka? Dama jari muke nema da ita ko me? Wani talauci garemu da zamu jira sai mijin Uwata ya bamu abin duniya? Malam dan Allah ka sanja sam wannan son abin duniyar naka bai da kyau, ba haka musulunci ya tsara mana da mu nemi duniya ba, wallahi ina jiye maka fad'awa halaka akan wannan makauniyar d'abi'a naka wanda baka bar kowa ba tamkar ba masanin illimin addini ba."

"Na fahimci bak'in cikin da kikeyimin ya wuce iyaka Hurera, bayan kina son amshe dukiyanki ki mallakawa Uwani ta yi arzikin da kikeyi mata fata shi ne ni kike son na talauce tamkar b'eran masallaci, to wallahi baki isa ba, kinyi kad'an ki zamenin inuwar giginya na nesa kasha dad'i, na rantse da Allah sai Uwani ta zamemin jari kamar yarda ta zame miki hanyar bud'ewar k'ofofin samu tun bata san kanta ba wanda kike neman maida mata da kayanta na koma a huhun ma'ahu, ba wan ba wan karatun d'an kama, na yiwa duniya zuwar zomo yarda na zo a guje na koma a guje, to da sake wai anyiwa mai dami d'aya sata, dole ne ki sanja tsari a game ta amshe dukiyanki ko kuma Uwani ta zamemin jari ko zab'i na k'arshe shi ne na tafi masallaci na yi shela ga mai son sadakar aurenta na bawa ko waye ko da kuwa Makaho ne, Kuturu ne, Gurgu ne, Bebe ne kai ko duk wanda ya had'a duka nak'asar ne indai ta zamo rabonsa zan bashi ita Sadakarta."

"Malam! Kana cikin hankalinka kuwa?."

"A'a sama na ke cizo."

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, wai shin har sai yaushe zamu sami kwnaciyar hankali daga sababinka ne Malam? Shin son kud'i hauka ne?"

"Kanki akeji Hurera abinda na sani ne indai ni Uban Uwani ne dole ki barni na yi duk yarda naso da ita tunda bak'in jininta ya ta'azzara ta zama uwar mata a gabanmu muna ta ibada da haramtacce ruwa."

"Me ka ke nufi da kalamanka Malam?"

"Abin da jahilan farko sukayi ittifa'i."

"K'alu innalillahi wa inna ilaihin raji'un! Kana nufin ka zama irinsu kenan?"
Chapter 41 · 0% Book details