← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 43

Sashe 19

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk abinda Fanta ta sanar miki gaskiya ne illa abu d'aya shi ne da ta ce halin Mas'uda d'aya da na Aunty Nafisa, sam halinsu ya sha bamban saboda Aunty Nafisa bata tsafi haka tana shakkar Uncle Muhseen sakamakon da ita Mas'uda mijinta bai isa da ita ba hatta da mahaifiyarsa sai taso yake zuwa gaisar da ita, k'anninsa kuwa ta haramta musu zuwa gidanta, tun abin na damunsu har yanzu ya daina. Shin ta ya ina kallon wannan lamari zan amince na zama matar shige wacce bata tab'a yin daraja."

"A gaskiya Mas'uda bata da hali amma duk da haka ina ganin aurensa zai baki damar kwatosa daga halaka, domin zaki nusar da shi hakkin uwa kan d'iyoyinta, kiga kenan tamkar kinyi jihadi ne."

"Ada naji zan iya yin hakan amma tunda na had'u da burin zuciyata duk da shima tamkar son maso wani na keyi masa wanda masu iya magana kan kirasa da k'oshin wahala, naji gara in hak'ura da shi na kama na gasken a haka nan."

"Son maso wani bana gaske ba ne Sister, kidai yi hak'uri ki kama Yaya Abdallah please."

"Ko mu biyu muka rage a duniya ba zan aureshi ba."

"Me ya yi zafi?"

Banza ta yi da ni na rik'o hannunta "Beebah walalhi Abdallah ya bani tausayi yana cikin matsalar rayuwa gashi kin kasa fahimtarsa."

"Shi kuma baisan da yana cikinta ba domin duk wanda ya nusar da shi illar rayuwar da a keyi a gidansa sai ya k'ulla gaba da shi nima dan na nuna masa illar watsi da goggo da ya keyi shi ne ya soma zagina tamkar ya sami d'iyarsa har da cewa bashi bani shi ne na nuna masa nid'in 'yar halas ce na datse dik wani hanya da zai sadani da shi domin na fahimci gani yake bazan iya rabuwa da shi ba saboda kud'insa tare da kyawun da Allah ya bashi sai dai ya makaro domin ni una sonshi ne domin Allah badan wani abu nasa da Allah ya yi masa baiwar samu ba kuma kinji na rantse wallahi har ya koma ba zaiga dariyana ba, zai san ya zageni, zai san ya kirani da wawiya, banza, wofi mara tunani."

Innalillahi wa Inna ilaihin, a gaskiya Yaya Abdallah bai kyauta ba, zagi na zubda mutunci duk kuwa yarda kake d'aukan mutum."

"Ai kam ya zubar masa a idanuna, zubewa na har abada."

"Please Beebah ki sassauta hukuncin da kikayi masa, ki tarbesa in yaso da ya tafi ki watsar da shi."

"Ai na rantse kuma bazanyi kaffara ba, walalhi zai san ni 'yar hakas ce gaba da bayana."

"To Allah ya kyauta, abin ya girmama."

"Amin."

Shiru mukayi zuwa can na ce "Tashi kiyi wanka tunda kin koramin Aminiya, idan kin fito sai inyi."

"Na fasa."

"Duk saboda jin Ab...

"Deejah dan girman Allah kibar zuciyata ta sami natsuwa da kiramin sunar mara hankalin nan."

"Na shiga uku ni Nana Khadijatu."

"Ki tafi kiyi wankanki."

"Ok bari na fita na samo musu drinks saboda ba abasu Zobo da kunun Aya kawai ba tunda gasu tafe da babban bak'o."

Harara ta zabgomin na murmusa tare da ficewa.

"Walalhi sai na ciwa su Safina mutunci musanman Bintu dan nasan itace uwar kaud'in ingizashi ya zo."

"Ba ita bace sister Beebah, goggo ce da kanta ta ce ya dawo dasu kuma shi ba danke zaizo ba ni ce na ambaci hakan amma dan Allah kiyi hak'uri bansan haka ranki zai b'aci ba."

"Bakomi Fanta ya wuce."

Ta ambata cikin sakin fuska tamkar ba ita ce ta murtukesa ba.

Murmushi suka sakarwa juna. Tafi na soma daga bakin k'ofa sannan na shigo muka had'a ido da Fanta na kanne mata ido d'aya ta yomin jinjina da babban yatsarta amma a wayance gudun kada Beebah ta harbo jirgin domin plan muka had'a dan ta sakewa Abdallah fuska.

"Kin san Allah Deejah sister Beebah tana da gaskiya dan Yaya Abdallah mijin ta ce ne na gaske, hatta da unguwa in zaije idan matarsa bata gamsu ba fasawa yakeyi wai baya son barinta cikin tunanin inda ya je."

"Ikon Allah amma kam ta sami miji mai gaskiya."

"Uhm na banza da wofi ba tunda na b'atawa mahaifiyarsa raina akanta."

"Kuyi masa addu'a wata rana sai labari."

"Idan sister Beebah ta amincewa aurensa ba."

"Ba sai Beebah ce zata saitashi ba ko matarsa zata iya nusar da shi illar b'atawa iyaye rai."

"Banjin hakan zai faru ba tunda akanta komi ke faruwa, ita ce silar faruwar komi dan ance tunda ya soma neman aurenta halayyansa na kirki suka sanja zuwa na tsiya."

"To Allah ya shiryata."

"Amin, shi yasa na ke ya bawa Uncle wallahi domin shi jajirtacce ne domin duk son da ya keyiwa Aunty Nafisa tana sab'awa umurninsa zai hukuntata musanman da yanzu sister Beebah ta kuma d'orashi akan hanyar saita mata tunani wanda muke fatar halin rashin kirkinta ya zamo tarihi."

"Ku ne kuka ambata masa ya nemi aurena kenan? Shin kuna tunanin tahanyar yi mata kishiya ce zai dawo da ita hanyar gaskiya?"

"A'a shi da kansa ya ambata yana sonki wanda najima da fahimtar d'abi'unki na burgesa bai furta miki kalman k'auna ba ce sai yanzu, kinsan komi lokaci ne. Sannan Aunty Nafisa kuwa muna fatar ta dalilin zama dake ya saka ta yi koyi da halinki nagari ta dawo mai kyakkyawar mu'amala da kowa musanman mu jininta."

Shiru na yi na kasa sake cewa komi saboda yarda nake jin fad'uwar gaba.

Gyaran muryan Beebah ya sanya muka gane ta fito wanka, da sauri Fanta ta shige toilet dan gabatar da wankan itama.

"Insha Allah tsoron da ke ranki zai zamo tarihi sabida muna kanyi miki addu'ar samun rayuwa mai inganci a gidan Uncle."

"Ke da su wa?"

"Mama da Sisters d'ina."

"Shin da gaske su Bintu sun san da maganar nan?"

"Eh dan aminiyarki ta fesa musu kuma sunyi na'am da lamarin saboda zamansu da ke na kwanaki biyu sun fahimci bakya da matsala zaki iya hak'uri da halayyan 'yar uwanmu."

"Uhm har yanzu kuna kan bani mamaki wai ace kuna 'yan uwar Aunty Nafisa na jini amma kuna murnan da ayi mata kishiya."

"Ke ba kishiya ba ce Deejah, abokiyar zamace tagari mai tarin nagarta wanda muka tabbatar bazata iya bin hanyar banza ba dan ta cutar da 'yar uwanmu sabida kina aiki da iliminki kuma kin gama samun tarbiyya daga uwa ta gari wato Mama."

"Nagode da wannan yabawan, insha Allah zan nemi zab'in Allah cikin shi da Aliyu, duk wanda ya zab'amin zan amshesa da hannu biyu tare da mik'a godiya gareshi."

"Uwata neman zab'inki ya kasance na kan kowa da kowa ne ma'ana ki nemi zab'in Allah akan duk inda mijinki yake yazo gareki bisa amincinsa idan kuma yazo to ki amshesa da hannu biyun da kika ambata domin yanzu bana goyon bayan Alhaji Muhseen ko Aliyu saboda zab'in Allah shine sama da komi haka yardansa babban alkhairi ne ga rayuwar bayinsa dan haka ked'in alluran cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka, ina fatar managarci, jajirtacce, mai tsoron Allah S.W.A da son Manzon Allah S.A.W zai d'aukeki ku rayu cikin inuwar aure na har abada."

"Amin ya rabbi Mama."

Beebah ta ambata cikin rawar murya saboda kalaman Mama sun shigeta ainun, ita dai zuwarta garin Kaduna tana ta samun natsuwar ruhi ta kalaman Mama masu cike da fikra.

Ni kam zubewa na yi gaban k'afafun Mama ina jan numfashi. Kamo ni ta yi ta rungume tana bubbuga bayana.

"Habibatu aramin ita muje unguwa, inaga sai bayan isha'i zamu dawo sai ku kula da gidan."

"Tam Mama kudawo lafiya."

"Allah ya so hakan."

"Amin."

Daga haka muka fice Mama na rungume da ni, a d'akinta na yi wanka na shirya.

"Uwata gidan Baba Umaru zamu saboda lamarin Malam yasoma bani tsoro kada wata rana ya kasheni ya maidake marainiya ya mallake dukiyar da ke zalama akan shi."

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, Mama me ya kawo wannan magan-ganun? Dan Allah kidaina ambatarsu dan suna sanyamin shakku."

"Shakkun me ne Uwata?"

Shiru na yi ganin haka sai ta ja kunnina da k'arfi na sanya k'ara ta kuma mud'ewa rik'e hannunta na yi cikin cewa "Shakkun ganin kamar ni ba d'iyar Ba...

"Nana Khadijatu!!."

Kiran sunana da Mama ta yi da k'arfi ya sanya ni yin dif da maganar ina girgiza kai.

"Wuce muje kuma kada na sake jin wannan banzan kalamin ya kuna fitowa a bakinki.'

"Kiyi hak'uri Mamana."

"Na yi, wuce muje magriba na kawo jiki."

Tafe muke a cikin Napep ina nazarin yanayin Mama, na hango tana tare da damuwa amma tana k'ok'arin b'oyemin sai na samu kaina da jin b'acin rai abinda na ke korerarsa kullum yana neman samun muhallin zama a ruhina wato tsanar Baba domin na tabbata shi ne silar faruwar b'acin ran Mama ta dalilin shigowarsa d'azun. Sadda muka isa gidan Baba Umaru suna gabatar da sallar magrib muma alwalla mukayi muka gabatar inda bamu tashi ba muka cigaba da azkar zuwa lokacin sallar isha'i domin tarbiyyan zuri'ar Baba Umaru idan anyi sallar magrib ba'a tashi sai an sallaci isha'i sai bisa babban dalili, hatta da yara k'anana 'yan shekaru Tara zuwa sama sun san da d'abi'an, 'yan k'asa da sune kawai zakaji karad'insu suma da zarar Baba Umaru ya shigo zasu natsu saboda baison hayaniya sam amma fa ya iya jan jikokinsa da sawa kamar yarda yakeyimin.

"Jikalle kuma takwarata kin b'uya ko kuma ince Hurera ta b'oyeki, sam bata bari kiyi zumunci da mu."

"Ayi hak'uri Hajiya Inna, ai gani yau nazo a gadonkima zan kwana."

"Kamar gaske."

Murmushi na saki ina kallo idanun Mama da itama ke doka murmushin.

Surikan gidan ne sukayi ta shigowa d'akin Hajiya Inna suna gaisar da Mama ni kuma ina gaisar dasu cike da kunya saboda yarda suke ta k'orafin na daina zuwa gaishesu.

"Zata rik'a zuwa duk ranar Juma'a insha Allah."

Mama ta ambata cikin 'yar dariya.

"To Allah ya nufa hakan."

Hajiya Inna ta amsa.

"Amin."

Suka amsa tare da ficewa.

"Taho muje mu gaisa da Baba naji shigowarsa."

Mama ta ambata cikin tashi tsaye.

"To."

"Hurera abi komi a hankali banda gareje kinji?"

"To Inna."

"Alhaji ya soma sanarmin da lamarin, ina ta yaki addu'ar Allah ya rayaki ku jima da Nana Khadijatu."

"Amin ya rabbi Inna."
Chapter 19 · 0% Book details