← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 43

Sashe 16

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** ***
Dai-dai sadda Uncle ya bud'ewa Deejah k'ofa tashige, Nafisa na isowa volcany sam bata hango Deejah ba amma ta shiga tunanin da wanda mijinta zai fita. Ta ke zuciyarta ya hasko mata da Beebah ce ko Fanta.

"Kai amma ai ba zai bud'e musu mota ba."

Jim ta yi cikin jin fad'uwar gaba, sai ta sakko zuwa wurin Baba Mai gadi, sadda ta jefo masa tambayar rud'ewa ya yi, tsawa ta daka masa tamkar yaronta alhalin ya yi jika da ita.

"Hajiya da Khadijatu ce."

"Khadijatu kuma? Wacece ita?"

"K'awar Fanta."

Wani ashar ta zabga wanda ya firgita Baba maigadi ya ja da baya ta nunosa da yatsa idanu jajur cike da tarin masifa, kafin ta zabga masa zagi ya shige d'akinsa da sauri ya kulle k'ofa domin da jimawa kallon mara hankali yakeyi mata tun sadda ta tab'a rufeshi da fad'a har da daga hannu kamar zata dukeshi dan kawai ya bar yaronta Hafiz ya fita waje wasa da yaran unguwa bisa tsautsayi mashin ya bugeshi yasami gobcewar gashi a hannu.

"Gara Alhaji ka auro mai hankali da da sanin darajar bil'adam ko wannan sokuwan ta yi hankali ta gane me duniya ke ciki. Zan cigaba da yi masa addu'a akan Allah ya bashi Khadijatu amatsayin mata, tabbas da kagama hayewa kam, yarinya mai hankali da aiki da ilimi, hak'ik'a gidan zai gyaru idan hakan ya kasance."

Haka dai maigadi ya yi ta zancensa shi kad'ai kulle da d'aki.

Nafisa kam a tsiyace ta koma cikin gida direct d'akin Fanta ta shiga ta sameta kwance tana amsa wayar saurayinsa Abul Abbas.

"Ke tashi in aikeki wurin Uwar Deejah."

Mik'ewa tsaye ta yi jikinta na rawa tare da datse wayar, tama kasheta baki d'aya ta dubi Aunty Nafisa idanu waje.

"Yes wurinta zan aikeki, ki ce mata na ce ta datse banzan alak'ar da ta k'ulla tsakanin d'iyarta da mijina tun kafin na d'auki mataki wanda ba mai dad'i ba ne dan zan iya kashe 'yarta har lahira in har ta sa ke ta auremin miji."

Lumshe ido Fanta ta yi ta koma ta zauna gefen gado ta yi tamkar ba ita Aunty Nafisa ke bawa umurni ba.

"Fanta ko dai da had'in bakin ki cikin lamarin ne?"

"To Aunty ai ban fahimci inda zantukanki suka dosa ba ne, Deejah dai kinfi kowa sanin ta kwana biyu bata shigo gidan nan ba balle su had'u da Uncle haka kinfi kowa sanin ingantaccen tarbiyyanta amma sai naji kinzomin da zancen cin mutunci, to a gaskiya bazanje ba, kina da k'afa kije mana amma kafin nan ki sani Mama bata d'aukan raini, idan kikayi mata fitsara zata ladaftar da ke kuma ki tuna kina da tambo a wurinta, kika kuskura kika taka mata gida da tijara komi zai iya faruwa wanda na rashin dad'i ne haka Uncle ya sami labari kinfi kowa sanin abinda zai faru, at end sai ince Allah kaiki lafiya ya dawo da ke da idanu lafiyayyu."

Abin mamaki duk zancen da Fanta keyi mata kasak'e Nafisa ta yi tana kallon bakinta har ta dasa aya bata motsa ba. Ganin haka sai Fanta ta fad'a toilet da gudu domin ta kwana da sanin shirunta ba alkhairi ba ne.

"Shegiya da dai kin zauna kallona wallahi dana illata miki bakin rashin kunyar."

Ta ambata ganin Fanta ta nemi mab'oya, ficewa ta yi cikin nazarin zantukan.

"Maganar Fanta da k'amshin gaskiya fa na san wacece Mama zata iya nad'amin duka in har na rattafa mata sak'on da na bawa Fanta, yanzu me ye abinyi? Bari in jira dawowar Abban Hafiz naji abinda yake nufi da fita da d'iyar makwafta unguwa alhalin gani matarsa ta sunnah bai fita da ni ba. Kai wallahi namiji munafuki ne yanzu ya rasa abinda zai sakamin da shi sai neman wannan 'yar banzan yarinyar mai siffan munafukai. Oh ni Nafisa ina ta murna ta tsorata ta daina shigomin gida a she suna manne a waje, kai wallahi ko me zai faru sai dai ya faru amma sai na yiwa uwarta da bokan ubanta kashedi akan mijina dan su rabashi da d'iyarsu."

Tana ambatar haka ta janyo dogon hijab ta jira ta sakko k'asa cikin had'a matakala bibiyu ta fice harabar gidan a tsiyace. Bawan Allah maigadi na hangota ya kuma d'iba da gudu ya shige d'akinsa ya kulle, ganin haka suma sauran ma'aikatan, masu kula da fulawa tare da mai wanki da guga suka kwasa da gudu suka nemi mab'oya dama maigadi na tsakiyan basu labarin abinda ya faru ne d'azun sai gata da fito a fusace."

Ita kanta lamarin ya bata dariya, ta murmusa ta fice tana tsine musu a zuciyarta ganin sun maida ita mahaukaciyar karfi da ya ji.

***
"Kin ga ne Khadijatu fito mu shiga ki zab'i abinda kike so kawai na maidaki gida in yaso idan sun dawo sai suzo da kansu su zab'i abinda ransu ke so."

Na tsinkayi maganar Uncle, sadda ya yi parking a harabar Babban Kantin.

"Nikam ban son komi, nagode mutafi gida kawai."

"Ko turaruka ba kya so?"

"Uncle d'awainiyar ta yi yawa, mutafi kawai."

"Na san ke d'in mai son k'amshi ce dan Fanta tasha sanarmin da na siyo mata turare duk in na yi tafiya wanda zata baki gift lokacin birthday naki dan haka ki amince na zab'o miki."

"Shi kenan Uncle zab'o d'in."

Na furta kaina sunkuye.

"Thank you Nana Khadijatu."

D'agowa na yi na zubawa bayansa ido har ya shige cikin Kantin, sauke ajiyar zuciya na yi inajin wani kalan natsuwa na ratsa ruhina.

"Uncle ya san kansa matuk'a dole matarka ta yi kishinka."

Na ambata cikin rad'a tare da bud'e kofar motar na fito na jingina ina kallon mutanen da ke kai kawo. Lumshe ido na yi ina shakar iskan bishiyoyin da suka k'awata harabar Kantin.

"Wow gaskiya na ji wani nishad'i a ruhina tunda na doso Kantin a she dai zanyi gam da takar ne wato gamo da matar A...

Da sauri da d'aga masa hannu, na hanashi k'arasawa, langab'e kai ya yi na sauke masa murmushi.

"Ina godiya da wannan kyauta Malama Khadija."

"Na me fa?"

"Na sadakan murmushi da kikayimin yanzu."

Nuno shi na yi da yatsa ya mik'o hannu tamkar zai kama yatsar na janye ya sanya dariya, na girgiza kai tare da gyara tsayuwa a jikin motar.

"Aliyu kana da ban dariya wanda a da ban lura da hakan ba sam."

"K'auna kansa ka soma lura da d'abi'un mosoyi."

"Uhm ka ganka ko da iya salon zance."

"Gaskiya ne Deejah, ni kaina ban san kina magana mai tsayi irin haka ba sai yanzu."

"Banda sharri dai Yallab'ai."

"Allah ki yarda kawai."

"To naji amma yarda bai zama do...

Bud'e k'ofar motar da Uncle ya yi da k'arfi ya katsemin abinda zan furta. Na kalli Aliyu shima ni yake kallo cike da tambayoyi sai na yi masa bye da hannu na shiga motar, ina zama Uncle ya fizga motar a guje ya bud'e Aliyu da hayak'i, waigawa na yi na hangosa yana karkad'e fuskansa sai na ji raina ya b'aci, na juyo muka had'a ido da Uncle shima fuskansa a had'e, tura kaina na yi tsakanin cinyoyina k'irjina na harbawa da sauri da sauri.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/21, 2:16 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Mrsjmoon.

E.W.F.

*Shafin na ku ne 'yan uwa, abokai na gari, dukkan daukakin yan EXQUISITE WRITER'S FORUM. Allah ya bar k'auna mara algus. Amin ya rabbi.*

Page 10.

'Me hakan ke nufi, na jin harbawan zuciya dik in na had'a ido da Uncle? Please zuciyata kada kiyiwa first love d'ina haka, wallahi ina son Aliyu.'

"Shi ne wane?"

Maganar Uncle ya dawo dani duniyar zancen zuccin dana afka, d'agowa na yi na kalleshi kad'an sannan na amsa a ladabce.

"Classmate d'ina a tahfiz kuma abokin koyarwana duk a can."

"Only wad'annan ne alak'arku?"

"Yana s...

Sai na yi shiru na kasa k'arisawa.

Shima bai kuma cewa komi ba ya cigaba da gudu saman kwalta sai da muka sauka titi muka shigo layin unguwarmu sannan na kuma tsinkayar maganarsa.

"Yana sonki ko kina son shi?"

Idanu na tsira masa batare da na amsa ba, shima kallona ya yi ya sauke murmushin gefen baki.

"Naji dad'i da ya kasance fagen ina da d'an takara domin hakan ya alamtamin cewa mallakan Nana Khadijatu ba abu mai sauk'i bane, sai an zage dantse, sai anyi kamar anayi sannan tamkar fad'a ce a filin daga inda kowa zaiso ya sami narasa akan abokin karawarsa, dan hakan zan zamo jarimi ta ko wani fuska domin hanin na yi nasarar sunkuce Nana Khadijatu amatsayin mallakina."

Bugun numfashi ya k'aru, innalillahi wa Inna ilaihin raji'un kawai na ke ja dan ban zaci Uncle zai iya ambatamin wad'annan kalaman ba ido na ganin ido.

"Ina neman alfama da kiyimin girki dan na yi kewar abincinki, shin Zan samu?"

Motsa kai na yi kawai saboda yarda bakina ya yimin nauyi.

"Nagode."

Ya ambata cikin fitar murmushi mai sauti.

Horn ya yi a gate d'in gidansa na dubesa da sauri.

"Dan Alalh ka bari in sauka a nan."

"Ba'a nan na d'aukeki ba."

Ya bani amsa a d'an fusace.

Yana gyara Parking Aunty Nafisa na isowa wurin.

"Kagani ko Uncle da ka saukeni a bakin gate na tafi amma yanzu gashi nan matarka zata kuma il...

"Kiyimin shiru Deejah ko ranki ya b'aci."

Tsuke bakina na yi tare da zamewa na kwanta cikin seat, ina ambaton sunar Allah.
Chapter 16 · 0% Book details