← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 43

Sashe 10

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Deejah kince baki son sanin labarin Aunty Nafisa da na baki labarin fitinarta wanda ya kai mutanen gida basa murnan zuwanta ziyara itama hakan da ta lura da shi yasanya bata zuwa sai bayan shekara-shekara amma kinga Uncle yana zuwa dik k'arshen wata ko sati biyu sabida harkan kasuwancinsa yana da k'arfi a Maiduguri, haka yana kawo yaransa su Hafiz ganinmu duk in an sami hutun makaranta, yana da kyaky-kyawan fahimta da danginmu sama da jininmu Nafisa. Na ji kakarmu Hajiya Babba na cewa Aunty Nafisa irin mutanen ne da Allah ya halitta tsiya na ganiyar shed'ancinta dole muyi hak'urin zama da ita a haka."

Ban san sadda na kyalkyale da dariya ba jin abinda Hajiya Babba ta ambatawa Aunty Nafisa. Ita ma Beebah dariyar kyalkyale da shi

"Madallah da wannan safiya mai cike ni'ima."

Muka tsinkayi muryan Mama daga bakin k'ofa, cikin murya mai cike da nishad'i na ce "Amincin Allah ya tabbata ga Mamana, abin alfaharina."

"Amin Uwata farin cikin Hureratu."

Sakkowa na yi na yaye labulen na rungume Mama wacce ke tsaye a bakin k'ofa tana jiran fitowana domin lokuta da dama haka takeyimin, ta kance koyarwar Ma'aikin Allah S.A.W ta ke bi na neman izini shiga wuri kafin bayyana.

"Ina kwana Mama?"

"Muntashi lafiya Habeebah?"

"Lafiyalau Mama."

"Masha Allah, ya kuma gajiyar hiran jiya? Dan najiyo Uwata batayi barci da wuri ba."

Kulle baki Beebah tayi tana dariya k'asa-k'asa.

"Uwata ya k'afafun?"

"Sunyi sauk'i sosai Mama."

"Masha Allah, nagode Habeebah da taimako."

"Kai Mama ai Deejah tamuce tunda masoyiyar Fanta ce."

"Haka ne, Allah ya biyaku da khairan ita kuma Nafisa Allah ya shiryata."

"Amin."

Beebah ta amsa yayin da ni kuma na jefowa Mata tambayar

"Mama wa ya sanar miki da itace ta k'onani?"

"Mijinta kuma darajarsa taci wallahi da sai na koya mata hankali, ina da hak'uri amma akanki ban san kalmar ba, gidanta dai kingama shiga insha Allahu."

"Ayi hak'uri Mama kada Aunty Nafisa ta raba zumuncin nan tasu da Fanta."

"Wannan ne kam bata isa ba Habeebah, Allah da ya had'asu shi ya isa ya rabasu ba ita ba."

"Yawwa Mamanmu haka na ke son ji."

Murmushi Mama ta yi tare da ficewa, muka biyo bayanta ta shige kitchen ni kuma na soma gyara gida Beebah na tayani, muna gamawa muka koma kitchen muka amshi Mama aikin had'a abin k'aryawa. Kafin bakwai da rabi mun gama komi, mukayi wanka, na bawa Beebah kayana sabbi ta saka sannan muka zauna karyawa inda ruwan tea kawai nasha saboda ban son karyawa da sas-safe ya yin da Beebah ta baje ta cika tumbinta ba wani bak'unta.

Sake yimin dressing d'in ciwon Beebah tayi tare da matsamin nasha magani dan cewa na yi tunda ya soma k'ak'ewa ba zan sha ba.

Misalin k'arfe tara saura kwata na shirya dan zuwa makarantar Tahfiz inda na ke koyarwa, Mama taso hanani dubi da ciwona na nuna zan iya zuwa, Beebah ta biyoni muka fito muna hira cike na natsuwa. Kafin mukai Bintu ta kirata ta sanar mata da cewa sun wuce Kano ta yi musu fatar dawowa lafiya ta bani wayar nima nayi musu addu'a.

Muna shiga makarantar abokin koyarwana kuma classmate d'ina dan tare mukayi karatun hadda amma ya girmeni sosai wato Aliyu Muktar, shi ne ya dubeni cikin murmushi ya ce "Malama Deejah yau da bak'uwa kika zo mana?"

Kallon shi na yi kamar zan amsa masa sai na sami bakina da yin nauyi, jin haka sai na wuce na bar Beebah tsaye da shi.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/16, 11:08 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
Mrsjmoon

EWF.

*Shafin na my Billy Galadanci ne, Allah ya bar zumunci tare da yalwatuwar nasara agareki mara iyaka, Amin*

Page 06.

"Kayi hak'uri haka Deejah ta ke sam bata da sabo musanman ga Maza."

"Ni ne shaida akan wannan halin na Khadija, tsawon shekaru da muka shafe muna karatu a cikin aji d'aya amma bamu tab'a maganar da ta wuce na mintoci biyu ba sai ko in karatu ne ya had'amu shima sai wurin muraji'a ko amsarwa juna hadda."

"Lallai kai ne ya dace ka sanar da mutane rashin sabonta ba wai asanar da kai ba."

"Uhm k'awar malama Khadija na tsareki da surutu, gashi har ta b'ace miki."

"No bakomi, dama rakiya nayo yanzu dai ka bani wurin zaman da zan dakaci fitowarta."

"Ok muje daga can in ban takuraki ba na tayaki hira kafin lokacin shiga darasina ya yi."

"Aikam ina godiya da karamcin nan, abokin Deejah."

"Aboki kuma?"

"Eh."

"Ina, ai ban isa na zamo abokin Malama Khadija ba saboda ita d'in kayan manya ne irin Sarakuna d'in nan masu fad'a abi dole ko da rai bai so ba."

"Kai Abokin Deejah, duk ita kad'ai."

"Allah kuwa Khadija ta da bance, samun irinta cikin Dubban Mata sai antona domin sauraren kalaman da suke fitowa daga bakinta kawai zai bawa mutum amsar cewa ita d'in ba sa'ar zancen yara irinmu ba ce ko manyanma sai wanda Allah yayiwa gamdakatar."

Dariya sosai Beebah ta sanya wanda hakan ya janyo hankali wasu malamai tare da d'alibai.

"K'awar Malama muk'arasa wurin kada nasamu kira daga hukumar makaranta ace ina zance cikin tsakiyar makaranta."

Motsa kai ta yi tana d'auke dariyar, suka jera cike da wayewa. Aliyu ya dubeta kad'an ya ce "Sunana Aliyu Muktar."

"Masha Allah, ni kuma Habeebah."

"Wow my Aunty, domin sunar babban yayarmu ce wacce muke Baba d'aya.

"A she ina tare da k'anina"

Motsa kai ya yi batare da ya furta kalma

A k'asar bishiyar magoro ya yi musu masauki saman kujerun roba, ganyen bishiyar na kad'awa cikin fitar da iska mai gamsarwa, hira suka cigaba da yi cike da sakewa tamkar sun jima da sanin juna.

***
Misalin k'arfe shabiyu saura mintoci goma na kammala koyar da aju-juwan danake shiga, na fito ina raba ido dan neman inda zan hango Beebah.

"Malama, Malam Auwal yana kiranki."

Idanu na zubawa matashiyar yarinyar tamkar ban gane abinda ta fad'a ba.

"Malam Auwal ne ya ce in kira masa ke, yana office d'insa tare da su Malam Bashir."

Motsa kai na yi, yarinyar ta bar wurin, najima tsaye batare da na motsa ba.

"A'a Malama Khadija kina lafiya kuwa?"

Saida nayi gaba kad'an sannan ta amsa "Ina lafiyalau Malam Hassan, dafatan kaima haka?"

"Alhamdulillah"

Ya amsa cikin nufar office d'in shugaban makarantar tamkar badani yake maganar ba alhalin shi ya soma.kulani, tsaki na ja a cikin raina tare da nufar office d'in nima ina k'issima dalilin kiran da a keyi min.

Office d'in cike da malamai na samu domin malamai shida ke ciki gami da shugaban makarantar bakwai, na zauna tare da gaisar da su a jam'i suka amsa, shiru ya ratso wurin zuwa can na tsinkayi muryan mataimakin shugaba Malam ishaq ya kira sunana, ban amsa ba illa idanu da na d'ago na zuba masa gabana na fad'uwa. Sake kiran sunana ya yi alamun yana buk'atar amsawana, amsawar na yi a hankali, ya yi gyaran murya tare da cewa "Shugaba Malam Auwal ya kiraki ne domin ya nemi alfarman da ki cigaba da koyarwa regular saboda wasu daga cikin malamanmu sun sami takardan cigaba da karatu a k'asar misra, idan sun tafi zamu fusakanci karancin Malamai shi yasa mukaga dacewar ki dawo koyarwa full, dafatan zaki amsa k'ok'on bararmu da hannu biyu?."

Wani dim na ji saboda burina na bar koyarwan baki d'aya sai ga wani batu sabo.

"Dan Allah Malama Khadija ki amince sabidya muna da bukatarki ainun, d'alibanmu na gane koyarwanki haka iyayensu na alfahari da hakan makarantarmu na samun d'auka ta wannan fannin, dan Allah kada ki watsa mana kasaya idanu."

Shiru na yi ina sauraren magan-ganun Malaman wanda duk kaninsu saida suka tofa albarkacin bakinsu ta hanyar rok'on amincewana a k'arshe suka tsuke bakunnansu suna dakacen amsana. Na d'auki mintoci kusan uku kafin na ce "Zanyi shawara da mahaifiyata."

"Allah yasa muji alkhairi."

Shugaba Malam Auwal ya furta cikin saukemin kallon k'urillah wanda na tsana.

"Amin."

Duk suka amsa.

Sallama na yi musu na fito sai dai ban ga Beebah a inda na barta d'azun ba, tsayawa na yi ina nazarin inda ta shiga, maganar Malam Hassan ya sa na juyo ina nemo amsan da zan bashi akan tambayar da ya yi min.

'Me yasa bakya alfahari da abin adonki Malama Khadija?' Tambayar nasa na sake maimaitawa a raina ina son sanin ma'anar kalman ABIN ADO daya ambata. Tamkar kuwa ya shiga raina najiyo yana yimin fashin bak'in manufarsa

"Manufata shi ne me yasa ba kya danganta kanki da Mahaifinki sai dai a koyaushe Mahaifiyarki kike ambata a muhallin Mahaifinki alhalin ita d'in k'asa ta ke da shi ta kowani fuska tun daga halitta har zuwa girman matsayi wanda Allah ya bashi akan sama da nata dan mace bata tab'a jagorancin d'iyoyintaba sai da tsayayyen namiji."

"Malam Hassan kana da k'arancin sani akan muhimmancin Mahaifiya ga d'iyoyinta, tabbas Allah ya S.W.A ya fifita halittar Namiji akan Mace amma a wurin girman matsayi ta fannin biyayya sai ya fifita halittar Mace domin sai da ya ambata da abita sau uku kafin ya ambaci uba kaga kenan ba'aibu ba ne dan na ce zanyi shawara da mahaifiyata, ka san ko masu iya magana sunce ciwon 'ya Mace na 'ya Mace ce."
Chapter 10 · 0% Book details