← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 43

Sashe 21

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh ke Auntynmu ce tunda Uncle Muhseen ya fad'a fagen yak'in nemna mallakan ruhinki."

Toilet na fad'a batare da na biye mata ba, dariyar danaji an kwashe da shi yasa na fito da sauri Bintu ce kwance saman katifa sam ban lura da ita ba.

"Ke ma kina bayansu Fanta ko?"

"Eh kuma ki sani har k'anwar Uncle ta Sami labari cikin satin nan zata shigo Kaduna may be time d'in mun wuce dan jibi kamar yanzu kowa na kwance saman gadonsa yana huce gajiya."

"Nikam me yasa kukeyimin haka ne? Yanzu kunsa zata zo idan ta sami labarin ba haka bane me zaku ce da ita?"

"Nufinki wancan yaron kike so wanda bai wuce sa'arki ba?"

"K'anina ne kin manta."

"To wallahi kada ki bashi lokacinki a banza da wofi domin baku dace ba sam."

Banza na yi da ita na koma toilet.

Har na kwanta na jiyo maganar Bintu.

"Deejah kada kiyi Wasa da damarki domin samun miji kamar Uncle Muhseen rabo ne, tun kafin kuyi nisa ki sallami Aliyu dan wallahi indai muna raye baki da miji sai Uncle Muhseen."

"To Baba da Mama."

"Zancen gaskiya ne dan nasan Baba da Mama suna ganin Uncle wanda ya mallaki komi bazasu amince su bawa wanda ke neman na siyan sutura ba."

"Kinga Bintu ki kyaleni inyi barci tam."

"Bazan bar kiba sai kin san waye Uncle."

Banza na yi da ita, Ina jin Beebah na dariya k'asa-kasa bisa alamu ita ta kunna wutan ta koma gefe.

"Ai kin shiga uku tunda Bintu ta ke yin lamarin fiye da kowa."

Tashi zaune na yi na zubawa Beebah idonu ta gyara zama cikin cewa.

"Ni da Bintu da Aunty Nafisa dakinmu d'aya. Fanta d'iyar k'anwar Momy ce. Safina da firdausi su kuma d'iyoyin yayyun Momy ce. Iyayenmu kansu had'e shi yasa muka taso da son juna dan duk gidan da mukaje ba'a nuna bambanci, abu d'aya muke."

"Da kyau."

Na ambata tare da komawa na kwanta.

"Kada ki yi mamakin yarda dukkanmu muke son ki auri Uncle sabida ke ce zaki iya zama da 'yar uwanmu ba cuta ba cutarwa."

"Ni kuma ta cutar da ni ko?"

"A'a fa, Uncle zai baki kariya fiye da tunaninki."

"Shi kenan na amince soyayyarsa amma bance zan auresa ba saboda zab'in Allah na ke kan nema."

"Masha Allah, yanzu kuwa zan sanar masa dan ya soma zuwa zance Kai tsaye kafin Malam Ali ya mallake zuciyarki."

Bance komi ba haka banji fad'uwar gaban da na ke ji ba dyik in anayimin zancen auren Uncle Muhseen.

Wayata ce ta yi k'ara na duba sak'o ya shigo.

"Ina godiya da wannan aminci."

Kallon Beebah na yi ta jinjinamin kai.

"Tukuicina kujerar Umrah a wannan Azimin ya tabbatarmin na can-canci hakan saboda na d'orashi akan hanyar gyarawa matarsa zama tare da yi masa jagorar mallakan tauraruwan taurari Nana Khadijatu."

Ware ido na yi. Ta tashi ta soma rawa cikin ambatar "Khadija haske ce a ko ina." Abinda ta yi ta ambata kenan Bintu na tayata, saida suka gaji sannan suna zube suna maida numfashi.

"Deejah Uncle maraya ne Babansa ya rasu tun yana d'an shekaru biyu. Mamansa ta raine shi na shekaru uku k'anin Babansa ya amshe shi lokacin yana da shekaru biyar kenan, kulawansa ya dawo hannunsa inda ya fuskanci k'alulabe da mafi aka  sarin marayu ke fuskanta ko ince wad'anda suka taso ba tare da maifiyarsu ba.  K'an warsa Hafsat mamansu ne d'aya, tana tare da k'anwar Mamanta a garin Abuja saka makon rasuwa da mahaifiyarsu ta yi sanadin haihuwar k'anin Hafsa wanda shina kwanarsa biyu a duniya ya bi mamnsa. Su biyu  ne rak mamansu ta Bari wato Hajiya Madina.

Muna da dangartaka da Uncle dan sadda yazo neman auren aunty Nafisa aka gano mahaifin Mamansa abokin kakarmu ne, dan 'yar Maiduguri ce ita Babansa ne d'an Kaduna.

Numfashi na sauke cike da jin tausayin Uncle.

"Uncle yana da burin k'anwarsa ta zauna a gidansa amma halin Aunty Nafisa ya hanata zama, duk da bata dukanta bata zaginta amma fad'a da sanya aiki kawai sun isheta ko Fanta dan tana da hak'uri ne wallahi da tuni ta gudu."

Juya baya na yi sabida har ga Allah yanzu bana son ana ambatar sunar Aunty Nafisa a gabana.

"Muna da yak'innin idan kina tare da ita zata soma koyi da halinki na hak'uri da kirki har gidan Uncle ya zamo yarda yakeso wato jama'a su cika shi ana kaida kawo cikin kulawarsa."

"To Allah yaso hakan."

Na ambata a hankali.

"Amin."

"Idan momy ta sami labarin nan zatafi kowa jin dad'i domin tafi kowa sanin kishin Aunty Nafisa wanda idan taga abokiyar zamanta na yin abin alkhairi itama zata aikata fiye da nata musanman intaga Uncle na yabawa aikin 'yar uwan zamanta to zata zabura ta aikata ko dan ya yaba mata, kinga kenan anjefi tsun-tsu biyu da dutse d'aya ."

Numfashi na ja a hankali ina k'ara fahimtar dalilin da ya sanya su Beebah ke goyon bayan aurena da Uncle sabida halaiyan 'yar uwansu ya bak'anta ransu.

'Uhm ni dai gani ga Allah, ban san me ya zab'amin ba.'

Na ambata cikin raina, a fili kuwa na ce "Ya Allah ina fatan samun zab'inka mafi alkhairi a rayuwata."

"Insha Allah Uncle d'inmu zai zab'a miki."

Suka ambata a tare, ido kawai na zuba musu. Ina saurarensu sai ambatar halin karamcin Uncle sukeyi  suna k'ara na-natawa.

A makare muka tashi saboda muka idar da sallar subahi barci muka koma. Mama ta kammala duk aikin gidan dan haka wanka mukayi muka karya na wuce Tahfiz a gaggauce dan lokacin shiga ajina ya kusa. Sadda na shigo gate ina kallon Aliyu daga nesa tsaye bakin wani aji amma ban nuna na gansa ba na shige ajin da zan soma da shi.

"Ba ko gaisuwa matar Ali."

Sak'on na karanta na maida wayar silent batare da na bashi amsa ba. Ina tsakiyan k'arin hadda ya shigo da sallama, yaran ne suka amsa masa nikam a zucci na amsa na cigaba da karatuna, tsaye ya yi yana bina da kallo dakatawa na yi na tura masa sak'on dan Allah ya fita, maimakon ya fita kamar yarda na nema sai ya tako zuwa gabana ya tsaya mik'ewa na yi ina kallon yaran na ce "Yau Malam Aliyu yazo tayamu karatu ya kamata kuyi masa wuri."

Dariya suka sanya, shima darawan ya yi ya tafi gefen wani yaro ya zauna.

"Oya ayi mana karatun."

Murmushi na yi na koma na zauna na cigaba da karatu amma duk sai naji na takura saboda yarda idanunsa ke kaina. Aya na sanya ma dubeshi kad'an sannan na ce "Dan Allah Malam ka k'arasa musu ni bari in tafi d'ayan ajin da na ke son yi masu gwaji."

Ban jira amsarshi ba na fice. Daga Ajin da na ke ina yiwo karatunsa cikin d'aga murya, murmushi na yi ta dokawa kawai ina yabawa k'aunata dana hango a idanunsa.

Koda lokacin tafiyana gida ya yi Aliyu na  ajinsa dan haka baisan na wuce ba. Ina shiga gida saiga kiransa, d'auka na yi ya rufeni da tulin k'orafi akan tafiyata ban jirasa ya kawoni ba.

"Aliyu mu kame kanmu mu sani makaranta muke ba filin masoya ba, ka daina biyoni gaban d'alibaina kada su rainamu kasan sun soma girma tsaf zasu fahimci inda muka dosa, ka amince mu kasance tamkar bakomi tsakaninmu amma da zarar mun bar kamaranta mu nunawa juna k'au...

Sai kuma na yi shiru ina 'yar dariya.

"Uhm k'arasa mana Matar Ali."

Shiru na yi.

"Na amince da zancenki dear ko dan gudun sa'idanawa masu neman abin fad'a batare da ankasa da su ba."

"Nagode da fahimta."

"Ni ke da godiya, ki jirani bayan la'asar zanzo da sister na."

"Ok sai kunzo."

"Love you always Matana."

"Me too."

Dariyan da ya kyalkyale da shi yasa na datse kiran na kife fuskata a tafukan hannuna.

"Uwata kin dawo lafiya?"

Da sauri na d'ago Mama ce tsaye k'ofar kitchen, kallon da takeyimin ya tabbatarmin da ta ji wayar da na ke yi. Da gudu na kwasa zuwa d'akina. Dariyar Mama na jiyo har da tafa hannaye.

"Ikon Allah, wannan wani irin kunya Allah ya baki Uwata?"

Cukuikuye fuskata na yi da bedsheet, ina sauraren zantukan Mama. Duk yarda taso in tashi nak'i sai kawai ta fice tana dariya mai sauti. Nima dariya na sanya ganin yarda Mama ke farin ciki yafi komi sanyani nishad'i.

"Da alama Aliyu kai alkhairi ne a rayuwata."

Na furta a hankali.

"Uhm."

Beebah ta yi gyaran murya, harara na cilla mata ta kwashe da dariya cikin girgiza sumar kanta dake d'igan ruwa.

"Malama ina Yaya Abdallah?"

"Ya koma garinsu tun d'azun."

"Ayya bana nan bamu had'uba."

"Nima tun isowarsu har ya wuce bamu sake ganin juna ba."

"Saboda me ne?"

"Babu."

"Anya kin kyauta masa kenan? Ko ba dan alak'ar k'auna ba ai kya bashi kula dan zumunta."

"Deejah me kike so inyi masa? Ya zo naje mun gaisa na zauna cikin dangi yana hira da kowa bandani to akan me zan cusa kaina ya zo ya tozartani dan na hango take-takensa kenan."

"To Allah ya kyauta."

"Amin."

"Uncle yana ta kiranki, shin me yasa baki daga ba?"

"Tana silenta ne."

"To ki kirasa kafin ki kwanta dan na sanar masa da zaki kirashi idan kin dawo."

"Nikam kunyarsa na ke ji, please ki sanar masa na yi barci."

"Jibi kamar yanzu ina gadon Momyna, maga wanda zakiyiwa salo."

"Wayyo kewa zai kasheni."

"Ina kika san kewa, ai sai muntafi da aminiyarki."

"Kuna nufi Fanta daku zata wuce?"

"Insha Allah, amma zata dawo."

Kwalla naji sun cikomin na yi saurin juya mata baya.

"Mu muka matsa ta biyomu saboda ku sami fahimtar juna da Uncle batare da Aunty Nafisa ta sanya zargin cewa Fanta ce ke rura lamarin ba."

"Kuna ganin wannan matakin shi ne mafita?"

"Eh domin bazan b'oye miki ba hankalin 'yar uwanmu ya tashi duk yarda muke goyon bayan lamarin tabamu tausayi d'azun da ta ke kuka a gabanmu amma mun nuna mata Uncle mijin mace hud'u ne ta yi addu'a akan lamari shi yafi akan tada hankalinta, da alama ta d'auki nasihohinmu musanman na Safina saboda ita malama ce kamarki sannan Allah ya yi mata baiwar iya lwantarwa da mutum hankali."
Chapter 21 · 0% Book details