← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 43

Sashe 26

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/27, 8:16 PM] 💘: DAMUWATA
BY MRSJMOON

E.W.F.

PAGE 15

K'arfe biyar da mintoci goma Sha biyar Alhaji Muhseen ya fito zuwa masallaci kamar yarda ya saba saboda shi mutum ne mai rik'o da addini in kaga jam'in sallar subahi ya kubce masa to baida lafiya ne ko ya fita k'asar. Fitowarsa ya tuna da police da ya d'auko gadin su Bintu.

Wurinsu ya nufa suka gaisa tare da tabbatar masa da babu wanda ya dawo dan yunk'urin shiga gidan, godiya ya yi musu suka jera zuwa masallaci saboda musulmai ne, bayan an idar da sallah suka fito har cikin gidan ya yi musu jagora suka ga abin da akazo sata suka kuma duba ko ina ko zasu sami shaidan da zaisa agano barawon amma basuga komi ba, sallamarsu ya yi ya dawo cikin gidan ya sami su Fanta tsai-tsaye cike da tsoro jin barawo ya shigo suna barci.

"Ku shirya ku kulle ko'ina ku dawo gida 'yan sanda zasu cigaba da saka ido a gidan daga nan har zuwa sadda masu gidan zasu dawo."

"To Uncle."

Suka amsa atare.

Ya fice cikin tako mai cike da natsuwa. Yana shiga gidansa mota ya d'auko ya nufo Asibiti cike da burin son sanya Deejah a idanunsa, yana sanyo hancin motarsa a cikin Asibitin Baba na fitowa, horn ya yi masa dan ya tsaya su gaisa amma yana kallonsa ya kauda kai gefe ya yi gaba tamkar zai kifa saboda sauri.

Raka bayan Baba da kallo ya yi cike da mamakin baudadden halinsa na rashin fahimta.

"Ikon Allah sai kallo da alama taimako na son zama matsala, ko jiya badan na kai zuciya nesa tare da tuna cewa ni ke neman had'a ziri'a da shi ba tabbas da mun raba abin kallo a bainar jama'a."

Ya ambata cikin dafe gefen kansa da ke yi masa ciwo tun daren jiya. Ya jima zaune cikin motar kafin ya fito jikinsa a sake ya nufo ciki. Nurses din da ya gani sun shige d'akin da Mama ke kwance a guje yasa shima d'iba da gudu ya rufa musu baya. Saidai kafin ya isa sun kulle k'ofar wayar Deejah ya kira tana ringing ba'a daga ba ya sake kira akaro na biyu ya ji akashe.

"Me ke faruwa?"

Fitowar Likita daga d'akin ya yi hanzarin shan gabansa.

"Dr. Jalal me ke faruwa?"

"Biyoni office Yaya, dama kai zan kira yanzu."

Saida Dr. Jalal ya b'acewa ganinsa sannan ya bi bayansa.

"Yaya Muhseen yarinyar nan tana cikin wani hali domin ta shiga coma farfad'owarta zai d'auki d'an lokaci saboda firgitan da ta yi da ganin halin da Mamanta ke ciki."

"Jikin Maman ya kuma tashi ne?"

"Eh dan har munyi zaton rai ya yi halinsa wanda ya kai Dr. Salim ambatawa Khadija rasuwarta dalilin fad'awarta doguwar suma kenan."

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un."

"Relax Yaya insha Allah ba zata wuce sati d'aya ba zata farfad'o."

Dr. Jalal DAMUWATA Mahaifiyarta ce kadaiga halin da ta ke ciki shin ya zata koma idan ta sami labarin?"

"Zanyi mata bayanin yarda zata fahimta, insha Allah abin da kake gudu bazai tab'a faruwa ba."

"Allah ya so hakan."

"Amin."

"Ina ita Khadijatun?"

"Tana nan a cikin d'akin."

"A sanja mata daki please."

"Hakan dama zamuyi, mun barta ne zuwa anjima."

"Dr. A sanja mata yanzu dan Allah."

"Shi kenan bari in sanarwa Nurses su kaika private room."

"Yawwa, nagode Doctor."

"Bakomi Yaya, fatarmu dai su sami lafiya."

"Allah ya basu lafiya."

"Amin."

***
Uncle Muhseen ne zaune gaban gadon ya tsira mata ido hankalinsa ya yi nisa  cikin tunani, sam baiji motsin bud'e k'ofa ba sai maganarsa ya ji.

"Yaya tunani ba shi ne mafitar lamura ba, kayi musu addu'a shi ne sukafi buk'ata."

Ajiyar zuciya ya sauke tare da mik'ewa ya rik'o hannun Sa'ad.

"Nagode da tunatarwa Brother."

"Bakomi magajin Abba."

Murmushin ya ke ya yi tare da komawa ya zauna a inda ya tashi ya dora hannunsa kan na Deejah ya kalli inda Sa'ad ya ke tsaye.

"Brother ka zamo shaidana akan k'aunar da na keyiwa Nana Khadijatu, wallahi ina sonta, so mai tsafta wanda na ke hasko kwanciyar hankali a cikinsa domin ina fatar zamanta a karkashina ya sanya gidana ya gyaru wanda dangi zasu cikamin shi ta hanyar sada zumuntar da suka yanke saboda mugun halin Nafisat."

"Allah ya cika maka wannan burin."

"Amin."

"Yaya Abokina Dr. Jalal ya sanarmin dalilin tashin ciwon Mamanta guba aka shafa mata a lips domin sunyi buncike sun gano hakan amma bai shiga bakinta ba ya k'i sanar makane saboda yarda yaga kana cikin damuwa."

"Innalillahi wa Inna ilaihin, waye ya shiga d'akin bayan Khadijatu?"

"Bansa ni ba kam."

"Zauna da ita ina zuwa."

Yana ambatar haka ya fice Sa'ad ya rakashi da ido daga bisani ya zauna ya kafe Deejah da ido cike da tausayi, siririn tsaki ya ja tare da mik'ewa ya fito ya kira Nurse ta kula da ita.

"Abokina ya kamata ku gano wanda ke son kashe matar can."

"Engineer lamarin a rikice ya ke kaga dai d'aga yarinyar sai Babanta suka kasance a cikin d'akin kaga ba wanda zamu zarga cikinsu."

"Haka ne."

"Sannan matar kamar lamarinta da junnu dan ko su zasu iya had'a wannan kaidin dan su had'a rigima domin a d'orawa wani laifin su koma gefe suna dariya."

"Eh da wannan kuma dan a yarda aka kawota alamominsu ya nuna duk da hawan jini shima na sanya fad'awa yanayin."

"Haka Engineer kuma mai shirin zama Likita."

"Be serious Malam."

"To Yallab'ai yanzu abinda zamuyi shi ne hana kowa ganinsu sai wanda aka yarda da shi kuma tare da amintattun Nurses wanda zasuyi masu rakiya har zuwa sadda zasu fito."

"Good job Abokina, Allah ya k'ara fasaha."

"Amin."

"Bari in koma gida domin daga Masjid na taho nan."

"Allah sarki, hak'ik'a Engineer kai da d'an uwanka kuna da hali mai kyau, Abba ya yi dacen samun 'ya'ya masu albarka."

"Uhm abin da Momy ta kasa ganowa kenan."

"Kai ne ka kasa fahimtarta Abokina."

"Jalal me kake son inyi wanda zata fahimceni?"

"Nuna mata ka daina aikata sab'on Allah tare da bin umurninta kuma ka amince da zab'in ta."

"Ban aikata komi Abokina, nasha sanar da kai amma ka kasa aminta."

"Wallahi na aminta abin da Momy ke zargi ba gaskiya ba ne domin Abokina tsoron mata ya keyi."

"Uhm nagode da fahimta kuma abin da na aikata ai kuskure ne sannan natuba ina da tabbacin Allah ya yafemin."

"Insha Allah Abokina."

Furzar da iska ya yi idanunsa jajur.

"Sorry Yallab'ai, abu d'aya na ke so kayi yanzu shi ne ka amince da zab'inta tunda kai ka lalata hanyar to ya zama dole ka gyara ko dan rufuwar asiri."

"Bazan amince ba."

"Abokina zab'in Momy ne fa."

"Ko zab'in Abba ne banga mai sanyani na amince ba dan haka kada ka sake yimin zancen banzan nan sannan ka sani Momy bata da wani zab'i sai takura dan haka ka kiyayeni da kalamin nan tun ranka baifi nawa b'aci ba."

"Affuwan Yallab'ai sarkin hawa tamkar garin kwaki."

"Ai saikayi, kuma kada ka sa ran sake ganina nan kusa a Asibitin nan."

"Kaga matsalata da kai kenan saurin fushi."

"Shi yasa zan d'auke kafa ka daina ganin fushin."

"Zauna Abokina muyi magana na fahimta domin bana son fushin mahaifiya ya tab'a min kai."

Wani dogon tsaki Sa'ad ya ja tare da ficewa ya bugo masa k'ofar office d'in da k'arfi wanda saida ya razana.

"Kai anya Sa'ad shi kadaine kuwa? Tabbas ruwa baya tsami banza, saurin fushin nan ya yi yawa ga rashin fahimta, hak'ik'a bai rama mutsa-mutsai saman kansa."

Dr. Jalal ya ambata cike da damuwa.

***
Gidan malamin da ya yi saukar Alqur'ani Uncle Muhseen ya nufa sun jima suna magana kan lamarin inda ya yi ta bashi labarin yarda mugayen aljannu suke had'a fitintunu tsakanin al'umma a rasa gano kan lalura, domin kai tsaye ya karyata zancen guba, ya ce siddabarun mugayen aljannu ne da akayi mata turensu suka juya lamarin da guba dan had'a fitina asoma zargin da babu makama.

Uncle kam ya gamsu da bayanan, a k'arshe suka fito tare zuwa Asibitin. Sun sami Baba da matarsa kewaye da da Mama, k'iri-kiri Baba ya hana su isa wurinta duk kuwa da suna kallonta tana magana akan ya barsu amma ya rufe ido ya yi ta fesa bala'i tare da ik'irarin samuwar alkaba'i ga Uncle wanda tashin harshensa ya janyo Likita ya shigo ya koresu tare da bawa Uncle damar ganinta shi da Malam wannan abu da Likita ya yi ya bakanta ran Baba ainun inda ya k'ara kullatan Uncle domin bai jira komi ba ya fice tare da matarsa suka bar Asibitin baki d'aya, ya tarar musu Napep suka tafi gida shi kuma ya nufi gidan Baba Umaru wanda har zuwa lokacin bai sami labarin lalurar ba.

Saida suka tabbatar Baba ya b'ace sannan suka juya da mai Napep zuwa Asibitin suka sallameshi suka shiga suka zauna suna raba ido, zuwa can suka tambayi wata Nurse d'akin da Deejah ta ke ba tare da tunanin komi ba ta yi musu jagora zuwa d'akin. Zama sukayi a kujerun roba da suka samu a cikin d'akin suka tsirawa Deejah ido, suka kalli juna sai suka kyalkyale da dariya har da yin k'aramar gud'a cike da nishad'i. Bincike suka somayi ko zasu sami abin kwalam amma basu sami komi ba cike da jin haushi Asabe ta nufi inda Deejah ke kwance ta falla mata mari wanda saida yatsunta suka fito ta kai hannu ta shak'e mata wuya da iyakacin k'arfinta duk, ita kam Deejah bata san anayi ba.

"Kul! Yaya barta kada ki k'arasa gawar da banaki ba."

Cikin huci ta juyo "Wallahi Hinde ji na ke tamkar in kashe su na wataya cikin  dukiyar tumakan can wanda kullum sake tunbatsa sukeyi, hassada da kushe basayi musu komi sai ginuwa"
Chapter 26 · 0% Book details