← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 43

Sashe 20

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannan kiyi tunani akan zuwa wurin danginki domin shekara ashirin da d'aya ba kwanaki ashirin da d'aya ba ce."

"Insha Allah Inna zanje domin har da maganar nazo sanarwa Baba amma sai na soma zuwa Kwara naga zuri'ar Baba Abdul Ganiyu."

"Masha Allah Allah ya ida nufi."

"Amin."

Ina tsaye ina saurarensu farin ciki ya gama cikani jin zamuje wurin dangin Mamana abin da najima ina mafarkin zuwan lokacin.

"Uhm inda rai da rabo."

"Tabbas haka nr Uwata."

Kallon Mama na yi a she zancen zuccin da na yi ya fito fili.

"Idan kin gaisar da Baba ki fita in mungama zan kiraki."

Ta sanarmin daf da zamu shiga falon Baba Umaru.

"To Mama."

Da sallama muka shiga falon dattijon ya amsa mana tare da cillomin tsokana irin ta jika da Kaka.

"Matar b'oye yau ta bayyana to ki koma bana yi dan ban rasa mai neman ladar ba, gasunan buhu-buhu sai wanda naga damar ansawa gaisuwa tare da sakawa aiki."

Dariya na sanya saboda yarda yake maganar cikin zare idanu cike da barkwanci.

"Alhamdulillah yau na saka mai fuskan shanu dariya."

Nan ma wani dariya na kuma sanyawa cikin kulle bakina, hatta da Mama dariyar ta ke yi. Bayan mun gaisheshi na fito na bar Mama zaune gabansa cike da ladabi.

D'akin Hajiya Inna na dawo muka soma hira cikin maida zancen halayyan Baba wanda na fahimci na b'ata mata rai ainun. K'aran wayata ya katse mana hiran ganin Aliyu ne sai na kalleta ta sakarmin murmushi tare da mik'ewa ta fice tana cewa "Takwarata ba dai kunya ba to na bar miki d'akin, a ci soyayya lafiya."

sunkuyar da kai na yi, ina jin ta fice na gyara zama tare da d'aukan wayar wanda kiransa na biyu kenan, yi masa sallama na yi cikin laushin murya fiye da wanda Allah ya horemin.

*Affuwan 'yan uwa l ina cikin uziri ne shi yasa jiya kuka jini shiru.*

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/24, 11:20 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)

By Safiyya (Mrsjmoon)

E.W.F.

Page 12.

"Kayi hak'uri mantawa na yi in sanar maka da mun fita tare da Mama."

Na ambata masa bayan ya amsa sallamar.

"Kada kidamu Habiba ta sanarmin yanzu suka shiga gida ai sun fansheki musanman Fanta da ta ce zatayi miki hiran tare da yin recoding idan kinzo ki saurara."

Dariya muka sanya daga nan muka cigaba da hira inda na dage ina maida masa da martani amma duk da haka wani kalman tanayimin nauyin ambata. Kimanin mintoci goma shabiyar muka d'auka sannan mukayi sallama, sosai zantukan Aliyu suka sakani cikin nishad'i. Kwanciya na yi a saman kushin ina doka murmushi.

"Hak'ik'a ina sonka Aliyu."

Na ambata a fili sai kuma na yi saurin kulle bakina tare da kife fuskata a filon kujerar saboda da yarda kunya ya ziyarce ni.

Misalin k'arfe tara da mintoci bakwai kiran Mama ya shigo wayana ban d'auka ba sai na tashi na nufi falon Baba Umaru dan nasan tafiya zamuyi. Ina shiga idanuna ya sauka kan Kawu Habib b'ata rai na yi cikin kauda kai aikam ya kyal-kyale da dariya su Mama na tayashi dan sunga abin da na yi.

"Ko kuka kika fasa ba zai hanani na kiraki da Dije ba."

"Ni ba Dije ba ce, Hajiya Inna kina jinsa na b'ata miki suna ko?"

"To Takwara ya zanyi da d'an neman zance, ai inda kara ke d'in Mama ya kamata ya kiraki."

Kallonsa na yi ya murgud'amin baki kamar mace sai na sanya dariya ya ko taho kamar zai dukeni na manne jikin Hajiya Inna.

Gaisar da shi na yi ya amsa cikin kamala tamkar bashi ba.

"Khadijatu Mamanki ta yi miki kyauta amma ta ce kada a sanar miki yanzu amma dai mune shedu dan haka ki kasance wurin yi mata addu'ar gamawa lafiya domin samun uwa kamarta sai antona."

"Nagode Mama Allah ya sa kifi haka, Allah ya baki kyautar Aljanna ranar sakamako."

"Amin ya bamu baki d'aya Uwata."

"Amin."

Habibullah tashi ka maidasu gida tunda hanyarka ce."

"To Baba."

"A'a Baba kabarshi ya tafi wurin iyalinsa sabida zan biya gidan Malam kafin mu isa gida."

"Yaya Hurera muje in kaiku inba dai kina son bambance matsayina gareki ba ne."

"Shi kenan Habibu muje, dafanta zakayi dariya ka daina cin maganin."

Ficewa ya yi cikin murmushi. Muma sallama mukayi da su Baba muka sameshi har ya kunna motar.

"Dije zaki zo taron suna gobe ko?"

"Sunar wa?"

"Kar dai ince bakijemin barka ba?"

"Ya Salam Aunty Zainab ta haihu ne?"

"Uhm ba laifinki ba ne na mamanki ce, yanzu na yarda da zancen Hajiya Inna sam baki d'aukemu a danginki ba kamar yarda muka d'aukeke."

"Habibu kayi hak'uri ni kaina banje barka ba dan namanta amma zamuje taron suna insha Allah."

"To, Allah baku iko.

Shiru ya ratsa motar zuwa can na ce "Kayi hak'uri Kawu Mama zata zo   goben amma ni bayan sunar zanzo."

"Saboda me?"

"Kasan Uwata kifin rijiya ce data shiga taro sai taga kamar ita kowa ke kallo shiya bata son shiga taron jama'a sai dole."

"Da gaskiyanta tana da abin kallo musanman ga maza."

Da sauri na kalleshi ya murmusa tare da maida hankali kan titi."

"Habibu kaifa Kawun Uwata ce amma na lura kana son maida ita abokiyar wasanka."

"Yaya Hurera wallahi gaskiya na ambata Deejah na da abin kallo kamar ilimi, hankali, natsuwa da uwa uba hak'uri, shi yasa mazaje zasu so mallakanta a matsayin uwar 'ya'yansu, na tabbata duk wanda ya aureta ya yi babban dace tare da rabon na samun mace ta gari wanda Manzon Allah S.A.W ya ce dace da samunta shi ne mafi jin dad'in duniya."

"Zancenka gaskiya ne Habibu."

"Kinga kenan dole ta rik'a killace kanta ba ko wani kucaka da gara ya kamata suna kallonta arhaba."

"Kai Kawu dan Allah kadaina fasamin kai."

"Yabon gwani ya zama dole Deejah, ke dai ki godewa Allah da kika tara baiwa wanda ba kowa yake samunsa ba."

"Nagode Kawu."

"Godewa Allah 'yar Kawu."

"Habibu hoo, ba dai tsokana ba."

"Yaya haka Allah ya halicceni ya zanyi."

"Sai hamdala ga Allah."

Na ambata a hankali.

Sadda muka isa k'ofar gidan Baba k'arfe tara da rabi saura mintoci biyar.

"Ku shiga ina jiranku."

"A'a Habibu ka wuce kada mu b'ata maka lokaci."

"Bakomi ina jiranku."

Shigewa mukayi ina jan addu'a saboda nasan ba zamu fito lafiya ba batare da an b'atawa Mama rai ba.

"Mama wai me yasa ba mu bari mun zo da safe ba?"

"Yanzu Allah ya nufa muzo. Kayan auren Khamila aka kawo."

"Oh an dai-daita kenan?"

"Oho musu nidai an sanarmin an kawo kayanta bisa alamu wani ne dan wancan anmaida masa nasa tunda makashin mutane ne."

"To Allah sanya khairan."

"Amin."

Dun zancen cikin rad'a mukeyinsa har muka shigo tsakar gidan inda muka sami mutane cike ana ta kallon kayan cikin mutunci Mama ta gaisar da su suka amsa nima na gaishesu suka amsa tare da zubomin idanu abin da natsana kenan shi yasa ban son zuwa gidan sai suyi ta kallona tamkar sunga sabon halitta.

Baya na juya musu ina latsa wayata inda na ke hira da su Beebah a wani group danaga an sakani.

"D'iyar golden ko sai yaushe mijin da ake jira zai fito?"

"Lokaci dai, zab'in Allah bana mutum ba na nan tafe."

Juyowa na yi jin amsar da Mama ta bawa Uwar gidan Baba mai suna Asabe.

"Uhm wai ba, ko sai an tsufa ba zab'in Al...

"Kada ki sake kiyi sab'o Asabe domin shi zab'in Allah ba wanda ya san sadda zaizo saboda cikin rashin tsammani ke zuwa dan haka ki sanya ilimi kafin ki furta kalami."

Tsit wurin ya yi zuwa can jama'an wurin suka soma yiwa Asabe fad'ar rashin dacewar abinda ta yi tare da bawa Mama hak'uri, ganin abin na son zama rigima babba sai Mama ta yi musu sallama tare da yiwa maman Kamila fatan alkhairi muka fito Kawu Habibu ya ja muka tafi amma ina lura da yarda Mama ke ta sauke ajiyar zuciya alamun ranta ya b'aci hatta da Kawu ya fahimci bata cikin wal-wala shi yasa bai nemi maganaba har muka isa gida.

Abin mamaki Aliyu na gani zaune saman lifan nasa, yana ganinmu ya diro ya zube gaban Mama ya gaisar da ita cikin girmamawa sannan ya koma wurin Kawu ya gaisar da shi. Sunarsa Kawu ya kira ya amsa yana sunne kai.

Mama da Kawu ciki suka shiga ni kuma natsaya wurinsa.

"Dare fa ya yi Yallab'ai."

"Alk'awari na yi sai na gaisar da Mama yau tunda kuma na cika burina  sai ince Allah tashemu lafiya."

"Amin, nagode da k'auna."

"Ba godiya tsakaninmu Matar Ali."

Girgiza kai na yi, ya kunna mashin d'in ya tafi cikin d'agamin hannu.

"Dujengala kice in-law shi ne jarimin?"

Kauda kai na yi, ya sanya dariya.

"Sai da safenku Yaya."

"Aha mungode Habibu, agaida masu jegon kafin muzo."

"Zasuji."

"Allah kaika gida lafiya Kawulle."

Na furta masa cikin tsokana.

Duka ya kawomin na gofce ina dariya dan nima na sami sunar kiransa.

"Wannan yarinya zata haukatani fa, to na wuce dai."

"Da dai ka zauna neman magana."

Cikin dariya ya fice na kalli Mama ta nunamin d'akina "Tafi ki huta da safe zamuyi magana nasan son sanin inda Habibu ya san Aliyu kike son ji."

Da sauri na fad'a d'akina, ina jiyo dariyarta.

"Sannu da dawowa Aunty Deejah."

Idanu na ware jin sunar da Beebah ta ambatamin.
Chapter 20 · 0% Book details