← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 43

Sashe 15

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Muje na gaisar da Mama tare da kammala ayyukan gida idan mun gama sai muyi maganar."

"Motsa kai ta yi ta fice ni kuma na yi hanzarin kashe wayoyina gudun kiran Uncle sannan na biyo bayanta.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/20, 12:07 AM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Safiyya (Mrsjmoon)

E.W.F

*Shafin na aminai ne My Jamee, (Mom Aysar), dear Mamie waru, Mom sayyid, my sis VC, Oum Abdul A'had, My Fauxah and Dear Safiyya Abbas Gambo (Maman Mama) Allah ya bar k'aunarmu tare da albarka ga zuri'a duniya da lahira. Amin.*

Page 09.

Ko da na fito har Beebah ta shige d'akin Mama rufa mata baya zanyi Baba ya kirani da hannu na isa gabansa na durk'usa.

"Wannan wacece mara tarbiyya ce?"

Ya ambata cikin rad'a.

"Yayar K'awata ce Fanta."

"Shi ne Fanta tafita aiki da hankali?"

Shiru na yi dan bansan abinda Beebah ta aikata masa ba.

"Tana kallona ta kasa gaisar dani ta shige d'akin Hurera sabida da ita fitsararra ce, ni da gidana wata 'yar zamani ta shigo ta maidani ni da banza duk d'aya."

"Kayi hak'uri Baba taga kana lazimi ne."

"Bata dai da tarbiyya kuma zanci mutuncinta domin bata isa ta shigo muhallina ta wulak'antani ba."

"Bazata sake ba insha Allah Baba."

"Naji amma magiyanki bai isa dakatar dani daga k'udirina ba dan sai na cimata mutunci domin gaba ta kiyaye aikatawa wani irin hakan."

'Ya Salam Baba bazai tab'a sanjawa ba dai.'

"Ya kukayi da Hurera jiya?"

Da sauri na kallesa sabida hankalina ya nausa cikin zancen zucci.

"Na ce ya kukayi da Mamanki akan maganar yafemin dukiyanta?" Ya sake cillomin tambayar ganin na k'i cewa komi.

"Bata kulani ba."

"Kamar ya?"

"Ko da na yi mata magana kallona ta yi batare da ta ce komi ba."

"Hurera akwai bala'in wayau, ta gano ni na tursa-saki kenan? Shi kenan muzuba mugani shege ka fasa kud'i dai nacisa ba zan biya ba."

"Kudai sami masalaha Baba."

Harara ya cillomin na sunkuyar da kai.

"Iskancin banza, ko in na biyata uban wa zai gajesu in bani ba."

"Me kace Baba?"

A hanzarce ya kalleni sai kuma ya watsomin harara na yi saurin matsawa ya nunoni da yatsa cikin muryan gargad'i "Wallahi kika kuskura naji zancen nan a bakinta sai na lahira yafiki jin dad'i dan sai na il...

"Wallahi Baba ba maijinsa."

Na katseshi jikina na rawa.

'Dagamin hannu ya yi alamun in tashi, na mik'e nashige d'akin Mama da sauri. Beebah na hango tana gyarawa Mama zaman labule ita kuma Mama na zaune ta jingina da kujera tana karanta Hisnul Muslim. Wurin Beebah na nufa nasoma tayata ba jimawa muka kammala gyara d'akin ciki da falon sai lokacin Mama ta idar da karatun ta kirani na iso na zauna gabanta tare da gaisheta, amsawa ta yi cikin kallon Beebah.

"Sannu Habiba Allah ya baki miji nagari."

"Amin Mama."

"Baki da kunya Beebah."

"A'a Uwata barta ta amsa a fili domin addu'ar alkhairi abar amsawa kowa yaji ne."

"Mama ki rabu da ita, k'ila kowa irinta ce mai kunya har dana rashin hankali."

"Lahaula... Kinjita ko Mama? Kunya adon Mata ne kuma tana daga cikin Imani."

"Ya isa haka nan d'iyoyin albarka, ku muje ku samawa kanku abinda zakuci  ni kuma nayiwa Malam abincin gargajiya."

"Me zakiyi dafa masa Mama?"

"Tuwo miyar kuka."

Matsawa kusa da kunninta na yi na ce "Wai Mama me ya kawosa gidan nan alhalin ba girkinki ba ne?"

D'an tureni ta yi Beebah ta sanya dariya b'ata rai na yi tare da ficewa suka rufamin baya suna dariya.

Kafin k'arfe Takwas ta yi mun kammala komi na shiga wanka ina fitowa Beebah ta shiga, ko mai ban shafa ba na zira doguwar rigar shadda na fito na sami Mama zaune a baranda tana cin tuwon da tayiwa Baba.

"Mama kice dama ke ce zaki ci tuwon ba wani Baba."

"Gaskiya ne ni ce na yi marmarinsa amma ganin Malam yazo sai na ce bari inyi mana sai gashi ya fice batare da yaci ba."

"Mama dama ba'a nan ya kwana ba?"

"Eh, ina fitowa bayi dan yin alwalaln subahi na tsinkayi bugan gidansa."

"Ikon Allah Baba kenan sanin halinsa sai shi kad'ai."

"Zauna ki karya dan zaki rakani gidan Baba Umaru."

"Aikam dama na kwana biyu ban kai musu ziyara ba, dik na yi kewar Hajiya Inna."

"Itama ta yi kewarki, shiyasa na ce muje tare sabida jiya ta yi ta fad'a wai ban barinki kinayin zumunci da su kodan basu suka haifeni ba."

"Kai Hajiya Inna ba ruwanta da b'oye-b'oye."

"Hakan shi ne dai-dai Uwata, a duk inda kike to ki zamo mai gaskiya da fad'ar gaskiya komin d'acinta, domin gaskiya ita ce jigon tsanin ginuwar Imani a Ruhi."

"To Mama, Allah ya kara mana Imani."

"Amin Uwata."

"Mama bamu sami damar yin Azimin ba."

"Zamuyi dama kinsan komi nufin Allah amma tunda munyi alk'awari zamu cikashi insha Allah."

"Allah ya bamu iko gobe mu wayi gari da shi."

"Amin."

"Insha Allah zan tayaku domin aikin neman lada ba'a sanyin jiki."

"Godiya muke Habibatu."

"Mama babu godiya tsakaninmu sai sanya albarka domin tamkar Deejah na ke gareki."

"Madallah to Allah ya yi muku albarka."

"Amin."

Muka amsa a tare.

Muna kammla karyawa Beebah ta koma d'akina ta kwanta ni kuma na fice zuwa yiwa Uncle godiya. Ina zuwa bakin get d'in gidan naji k'irjina ya harba wani tsoro ya jiyarceni sai na soma karanto addu'a, na koma da baya na zauna a k'asar bishiyar dake fuskantan gate d'in na tsirawa bencin da Baba maigadi ke zama ido, tunanin yarda Aunty Nafisa taza kalleni na ke yi saboda babban abinda na tsana kallon banza wanda ya zame mata tamkar ibada. Kimanin mintoci goma ina zaune cikin nazari sai kawai na tashi cikin kuzari na doshi gate d'in domin yanzu na sami natsuwa sama da d'azun. Ina tura k'amin k'ofa Mai gadi na bud'ewa Uncle gate ganina sai ya fasa fita ya kashe motar na k'araso na russuna gefen da yake zaune na gaisheshi, bai amsa ba ya bud'e motar ya fito ya jingina da jikin motar, kallonsa na yi ta gefen ido, idanunmu ya had'u da juna sai na yi sauri sa ke russunawa kafin inyi magana na tsinkayi muryansa.

"Lafiyalau Khadija mai gudun makwaftanta."

Murmushi na yi tare da cewa "Naga sak'o nagode sosai, Allah yasa kafi haka, ya jik'an mahaifa, ya yiwa zuri'a albarka ya kayi dace da gidan Aljanna mad'aukakiya."

"Amin ya rabbi tare da ke."

Motsa yatsuna na yi suka bada sauti, ya ja fasali tare da cewa "Duka sak'on sun sameki?"

"Eh."

"Har na wajen Beebah kin karb'a da hannu biyu?"

Shiru na yi bugun k'irjina ya dawo sabo.

"Da alama Beebah bata sanar miki da sak'on nan ba ko Khadijatu?"

"Eh bamuyi maganar ba amma nasan zata sanarmin."

"Ok, shigo ki rakani yiwa su Bintu tsaraba."

"Mama zata aikeni ne Uncle."

"Ok, tafi gani nan shigowa neman alfarman ta aramin ke."

"A'a Uncle muje sai na sanar mata a waya "

"Bani number wayar nata."

Karanto masa na yi, ina tsaye ya kirata sun jima suna magana sannan sukayi sallama ya kalleni na sunkuyar da kai.

"Khadijatu mai kunya ce."

Ya ambata cikin dariya, murmusawa na yi.

Da kansa ya budemin kusa da driver na zauna sannan ya shiga muka fice. Tafiya mukeyi tamkar kurame sannan tuk'in a hankali yakeyi na gane hakan ne jin yarda ake zabga mana horn amma baisa ya k'ara gudu ba, wani d'an a daidaita sahune yazo gefena ya zabgo masa zagi, na rafka salati tare da neman masa shiriya wurin Allah.

Wani ajiyar zuciya na ji ya saki tare da k'ara gudu yana kallon titi ya ce "Ke d'in Uwa ce ta gari Khadijatu mai nemawa d'iyoyinta falalar Allah tun kafin su iso duniya."

"Uhm."

Kawai na iya ambata tare da maida fuskata gefe.

"Kina da bambanci mai tazara tsakaninki da Nafisa domin da ita ce maida masa da martani zatayi harma da k'ari dan ta iya manyan zagi tamkar jikar maguzawa."

"Ai Uncle ba kowo ne ke iya mallakan hankalinsa ba ya yin da wani ya zagesa, banga laifin Aunty Nafisa ba dan ta ramawa mijin zagin da akayi masa."

"Khadijatu shi komi na duniya d'an hak'uri, zagin nan fa bai mannewa a jiki balle ace zai zama tambo, idan kabar wanda ya aikata da halinsa kansa ya zaga kamar yarda kika aikata sai zagin ya koma masa ke kuma kika sami lada yayin da kikayi masa addu'a."

"Allah ya k'ara mana hak'uri."

Na ambata ahankali domin zantukansa gaskiya ne.

"Amin."

Shiru ya ratsa zuwa can na tsinkayiaganarsa. "Ina neman alfama idan Beebah ta sanar miki da sak'ona ki amince ba dan na isa ba."

Shiru na yi gabana na fad'uwa, nidai ban k'aunar jin sak'on nan sam. Latsa horn ya yi na kalleshi da sauri ya saukemin murmushi, ya maida hankali kan titi ya cigaba da cewa "Bazan takuraki ba Khadijatu, na bar miki zab'in ranki, dik abinda kika zanta da ruhinki ki sanar mata domin lamari ne dake buk'atar amincewar ruhi da ruhi."

Still ban ce komi ba shima ganin nak'i tankawa sai ya sauya zancen da jefomin tambayoyi game da rayuwar yau da kullum, ina bashi amsa dai-dai fahimtana, kuma na fahimci yana gamsuwa da bayanen. Da k'arfi da yaji dai Uncle ya maidani masuraciya domin bai bar bakina ya huta ba har muka iso babban kanti.
Chapter 15 · 0% Book details