← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 43

Sashe 5

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban san sadda na diro ba na fice zuwa d'akina na kulle k'ofa na jingina da shi na saki kuka jikina na mazari tamkar wacce aka watsawa ruwan k'an-k'ara.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure.)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/13, 10:47 AM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Mrsjmoon

*Shafin sadaukarwa ne ga Rahma Kabir (Mom Sultan) Allah ya albarkaci rayuwarki tare da zuri'arki baki d'aya, Amin.*

Page 03.

"A wacce duniya na ke ni Nana Khadijatu? Wacce kalan rayuwa ce  haka? Wani irin bak'i dare na fad'o cikinsa mai mugun duhu? K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un!, Allahumma igfirli war hamni. Lahaula waka quwwata illa billahil aliyul azim. Shin Baba wani kalan mutum ne? Shin haka keyiwa sauran d'iyoyinsa ko ni kad'ai ya ke b'e ke yiwa hakan? Hakik'a Baba bakayimin adalci ba, ba ka kyautata min, ka tozartani tozarci mafi muni, wallahi  na tsane...

"Allaha natuba ka yafemin fushin zuciya ne amma bazan tab'a tsanar wanda ya yi silar kawoni duniya ba."

Na ambata tare da tura kaina tsakanin cinyoyina ina girgizawa, kuka na kuma fashewa da shi cike da jin matsanancin tausayin kaina tare da Mama, kimanin mintoci goma shabiyar saanna na tsagaita da kukan domin ya kasa yimin maganain zafin da na ke ji a ruhina sai ma k'aramin rad'ad'i sa ke yi.

Cikin layi na mik'e zuwa toilet na d'auo alwalla na zauna saman darduma domin bazan iya tsayuwar gabatar da sallar nafila ba. Istiggifari na soma ja batare da nasan yawan adadinsa ba domin saida nayi iya yina sannan na koma kan yiwa Annabi S.A.W salati shima nayi bakin yarda ya samu sai na cike da hailalah, na d'ora da ambatar sunar Allah AL-DAFI'U. Na sami awa biyu a zaune cikin amincin Allah na somajin natsuwar jiki da ruhi na samuwa gareni, Alhamdulillah na kama ambata a fili ina jan hanci ruwan hawaye kuwa wannan ba'a maganarsu domin jin natsuwa ya soma rab'ata sai wani rauni na daban ya nashe ruhinta tare da k'arin zubar ruwan jurwaye, tausayin kaina na ke ji tamkar irin wacce ta rasa kowa a duniya.

Gyara zama na yi na soma tashibi na musanman ga Allah S.W.A dan samun cikar mizani da ayyukan alkhairi ranar sakamako wato _Subbahanallahi wa bi hamdihi wa Subbahanallahil azim._ Ban san adadin carbi nawa na ja ba amma na san dai natsuwa ya gama nashe ruhina da dukkan gab'b'aina.

Samun kaina nayi da sakin murmushi, idanu na lumshewa cike da jin matsanancin barci. Barcin ne ya soma fizgata na tsuke baki na cigaba da ambaton addu'ar tafiyar da k'uncin zuciya a'a asirce duk dan na k'ara samun natsuwa, ba jimawa kuwa barci ya d'aukeni batare da na sani ba.

A firgice na farka jin muryan Mama na kirar sunana. Rik'eni tayi ganin yarda nake zaro idanu cike da tsoro.

"Uwata koma barcinki banzo dan na tasheki ba, nazo duba yarda kika kwana ne, kuma alhamdulillah tunda alamu ya nuna kin sami barci mai dad'i."

Shafo fuskata na yi na ce "Mama rana ta fito banyi sallar subahi ba."

"Garin ya hakan ya faruwa uwata?"

"Mama bari inyi sallah dai."

"To maza tafi kiyi dan yanzu kusan k'arfe takwas na safe muke ciki."

Da sauri na mik'e na fad'a bayi. Bayan na idar da sallah Mama ta sake shigowa d'auke da jug tare da cup ta ajiye a kusa dani ta kuma fita ta dawo rik'e da madaidaicin kula, murmushi na yi na rik'o hannunta na ce "Mamana Allah ya biyaki da dubun alkhairori, ina sonki Mamana sama da son da na ke yiwa kaina."

"To Uwata nagode, yanzu maza ki karya kizo ki wuce wurin walimar Fanta dan ta shigo har sau biyu duk kina barci."

Idanu na zaro domin na manta da saukar Fanta. A hanzarce na kammala karyawa inda banci wani abin kirki ba duk kuwa da magiyar da Mama keyimin da na cinye. Wanka nayo na shirya dik a cikin gaggawa na fice da d'an gudu Mama ta rakani da addu'an alkhairi.

Ina fitowa waje Baba na isowa, wuce shi nayi tamkar ban gansa ba duk kuwa da na gansa tare da abokinsa hakan bai sa na tsaya gaisar da su ba saboda hakanan naji tsanarsa danake kaucemawa ya dira a ruhina, mutuncinsa na son samun nak'asu a idanuwana.

"Malam wancan ba Khadija ba ce ta gidanka?"

"Ita ce."

"Yaushe ta koma mara tarbiyya da har zata iya wucemu bata gaishemu ba."

"Mallam Ilya wannan ba komi ba ne da alama hankalinta ne bai wurinmu."

"Anya kuwa?"

"Malam Ilya shigo kayi aikin dana rok'i arziki kawai yafi wannan zantukan d'iyoyin zamanin wanda in baka dasu a gidanka to danginka basa rasawa."

"Oh to yanzu na gane gori kake son yimin akan...

"Walalhi Malam Ilya ka yarda ba gori na ke yi maka ba kuma dan girman Allah ka bar zancen nan kada ta koma ta wani sigan da rayuka zasu ba'aci."

Daga gaka Malam Ilya bai sake furta kalma ba ganin haka sai Baba ya ja hannunsa suka shige cikin gidan domin bawa Mama hak'urin abin kunyar da ya aikata daren jiya wanda son zuciya yayi masa jagora, shi ne dalilin gayyato abokinsa.

****
Ina shiga gate d'in gidan su Fanta na hango Aunty Nafisa tare da Uncle sun jero cikin shigar alfarma, da alama wurin walimar zasu tafi. Na k'arasa na russuna cikin ladabi na gaisar da su. Uncle ne ya amsa tare da tambayata dalilin da yasa na makara zuwa wurin taron.

Kasa amsa mishi na yi saboda da yarda jikina ya d'auki rawa sakamakon ganin yau ya tsaya yimin magana mai tsayi abinda baitab'a yimin ba tun sanin da na yi masa, maganarsa gareni bai wuce amsa gaisuwa shima atak'aice.

"Oya taho muje dama can muka nufa."

"No, bata kudin Napep kawai Abban Hafiz ta wuce"

"Ba zan bata ba."

"Me ye haka Abban Hafiz?"

"Mele ne, kuma ki fita idanuna wallahi ko ranki yafi na d'azun baci, kin daiji na gaya miki, sokuwar banza kawai wacce ta girma amma tamkar ana k'ara mata rashin tunani, mitchew!!"

Ai ko da Uncle zai duba na kusa kaiwa k'ofar k'aramin gate domin ina jin kalma Aunty Nafisa na bar wurin a hanzarce dan na san waye ita ba abin damuwarta ba ne ta rufeni da duka ta barni da ciwon jiki dan tasha dukan Fanta a gabana shi yasa na ke jin tsoronta ainun. Ina tsoron dik abinda zanyi atabamin lafiyar jiki shi yasa ita kanta Mama bata iya duka ba sam.

Sai dai duk abin da Uncle ke fad'awa Aunty Nafisan sun shigo kunnuwana saboda ya bud'e murya, jin fad'arsa ya kuma rud'ani na k'ara sauri.

"Khadijatu!"

Na tsikayi muryansa na kwalamin kira ai a guje na fice wajen gate, cikin sa'a ina fitowa Napep na sauke fasinja na fad'a tare da sanar da shi inda zai kaini. Shima ganin yarda na ke bai tsaya b'ata lokaci ba ya fizga Napep d'in muka tafi. Sai sauke numfashi na ke yi tamkar wacce ta yi gamo da dodo sai lamari ya bani dariya na sunkuyar da kai na yi ta sauke murmushi. Taka burki da mai Napep ya yi ba shiri ya saka na d'ogo a  hanzarce cikin ambatar sunar Allah AL ALIMU.

"Fito na ce ko in sab'a miki!."

Fitowa na yi jikina na rawa zatona marina zaiyi sai ya nunamin motarsa na tafi cikin sanyin jiki na bud'e gidan baya na zauna tamkar munafuka.

"Malama ki saki jikinki kada wannan munafuncin naki ya kuma janyo hankalinsa kanki abinda faruwar hakan zai iya janyo miki matsala da ni."

D'agowa nayi ina kallon cikin idanun Aunty Nafisa tako zabgamin harara murmushin yak'e na sauke mata tare da maida fuskata gefe.

"Wallahi sai naci ubanki bokan nan."

Da sauri ya kalleta, ta kuma gabgamin harara, na b'ata rai tare da cewa

"Babana ba boka ba ne."

"Ubanki! Me ye shi, in ba Boka ba?"

Sunkuyar da kai na yi sabida ban saba maidawa wanda ya girmeni da magana ba amma na k'udurta zanyi mata nasiha akan kada ka sake ambatawa mahaifina kalman Boka.

Motsin tafiyar motar ya sanar dani Uncle ya shigo motar.

"Khadija idan nakuma baki umurni kika tsallake to har gaban Malam zanje na baki kashi."

"Kayi hak'uri Uncle."

Bai tankamin ba sai nima na tsuke bakina ina cigaba da kallon gefen titi sannan inaji a jikina Aunty Nafisa kallon banza take watsamin tamkar yarda ta saba yiwa kowa.

"Ke da Fanta abu d'aya na ke d'aukanku, wato k'annin matana dan haka kada ki sake aikata min abinda Fanta bazata iya yimin ba."

"To Uncle, inshs Allah zan kiyaye."

"Hakan yafi."

"Abban Hafiz wai...

"Nafisat idan kinsan kalman ki ba ta arziki bace to ki barta a ranki zaifi."

Kallonsa na yi fuskan nan tasa a had'e tankar yarda na sanshi a baya. Ware min idanu ya yi ta mirror alamun me ye? Na sunkuyar da kaina k'asa a hanzarce cike da jin kunyar abinda na aikata wato kallo abin da na tsani ayimin.

Daga haka ba wanda ga sake magana har muka iso harabar makarantar. Na kama k'ofa zan fita na tsinkayi muryansa cikin kaushi

"Wait! Khadijatu."

Komawa na yi na zauna ina wasa da zobben azurfan dake yatsana.

Magana naji yanayi a waya bisa alamu da malamin makarantar ne, yana ajiye wayar nawa ta d'auki k'ara fito da ita nayi daga cikin pose d'ina mai kyau ainun wanda Mama ta yomin tarabar shi data shiga kasuwa.
Chapter 5 · 0% Book details