← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 43

Sashe 33

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya kwashe da dariya. Yana kammala shan tea ya kulle gidan ya nufo gidansa cike da tarin masifa, duk wanda ya gaisar da shi hannu kawai ya ke d'aga masa sai in anyi masa sallama ne ke amsawa saboda sanin muhimmancinta. Kafin ya isa gida Uncle ya kirasa ya sanar masa da farfad'owar Deejah wani burki ya ja ya yi dif, Uncle ganin kamar da matsalar network sakamakon jin shiru ba amsa sai ya datse kiran da nufin anjima zai sake kiransa.

"Wanna d'iya anyi mai taurin ran tsiya, bari in hanzarta zuwa Asibitin kada Hurera ta mannamin hauka ta ce ina farin ciki da ciwon ne dan na hango abin da ta ke burin ambata kenan gaban jama'a."

Ya tari mai Napep tare da sanar masa da inda zaije. Ana Napep d'in sai tsaki ya ke ja.

***
Aliyu.

"Aliyu ka natsu ka san inda kanka ke ciwo."

"To Hajiya na ce zan duba buk'tarki."

"Bana son ka duba Aliyu, burina ka tafi zance gidansu saboda ita mai sonka ne da gaskiya domin da bakinta ta furta tana son ka aureta."

"Hajiya ina da fa wanda na ke so."

"Wacece ita?"

"Khadija."

"Wacce Khadija?"

"Wacce mukayi walimar haddar Qur'ani da ita."

"Oh jikan Alhaji Umaru surikin Zainab?"

"Au Hajiya a she kin san Khadija na da alak'a da su Yaya Habibu?"

"Sosai kuwa domin lamarin aurensa da Mamanta akayi mace mai karamci."

"Shi kenan fad'uwa tazo dai-dai da zama."

"A'a bata zo ba saboda gida bai k'oshi ba'a kai dawa ba sannan ka tuna Amira k'anwar Zainab ce ta jini dan haka batun Khadija babu shi kaji dai na gaya maka."

"Hajiya dan Allah ki...

"Zancen kake so Aliyu."

Tana ambatar haka ta bar mishi wurin.

"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, wallahi ina son Khadija DAMUWATA duk na mallaki Khadija ce, ya Allah ka kawomin mafita cikin sauk'i."

"Amin Yaya."

"Salma kina jinmu da Hajiya ko?"

"Eh Yaya amma ina baka shawara da ka nuna tamkar ka amince amma a wurin Amira ka sanar mata da gaskiyan zuciyarka insha Allah zata fahimta tunda nasan tasha jin labarin illar auren mijin da bai son mace."

"Nagode k'anwata."

"Bakomi damuwarka tawa ce Yaya."

"Anjima zan lek'a Asibiti."

"Zan bika."

"Islamiya zaki sarkin yawo."

"Kai Yaya ziyarar maralafiya zani ba yawo ba."

"Baza ki je ba."

"To shi kenan ranar alhamis na je."

"Yawwa na amince da wannan kam."

"Yaya Deejah na da kyau tamkar shuwa ko 'yar k'asar turawa."

"Tubarkallah Masha Allah."

Dariya Salma ta kyal-kyale da shi, ya murmusa tare da ficewa. Gyara d'akin ta soma yi tana 'yan wak'e-wak'enta cike da nishad'i.

***
Hinde wai lafiya kuwa su Kamalu shiru basu dawo ba?"

"Nima zancen da zanyi miki kenan Yaya."

"Kada fa mafarkina na jiya ya tabbata."

"Na me fa?"

"Wai gini ya fad'o ya halaka su Kamalu, aka kawo mana su cikin jini tare da rakiyar 'yan sanda."

"Innalillahi, aiko da wuya ba an kamasu ba ne domin tun daren jiya gabana ke fad'uwa, wallahi cike na ke da fargaba kada asirinmu ya tonu abin da bamu samuba ya tabbata wato amsar takardan saki.

"Haba Hinde wai me yasa duk zantukanki ba na arziki ne ciki? To wallahi mugun bakinki ya k'are a kanki."

"Yaya wallahi ina jiyowa a jikina ba nasara a wannan tafiyar nasu."

"Bazan gani ba, mai bakin baki kawai."

"To shi kenan Yaya na yi shiru."

"Shi dai yafi."

Suka cigaba da aiyukansu na safe duk jikinsu a sanyaye.

"Hinde wai in tambayeki, da wa Kamalu suka tafi?"

"Kinsan Anas bai da lafiya shi ne K'asimu ya ce zai bishi sai shima Garba ya ce zaije naso hanashi amma ya kafe sai ya je, Kamalu ya cemin zai d'auki Isyaku Jagwa tunda yana da motar d'aukan kayan sai su loda a ciki."

Wani ihu Asabe ta kwalla wanda saida Hinde ta zabura.

Wani mugun ashariya ta watsowa Hinde tare ta cukumeta, suka soka kokuwa fad'i Asabe keyi "Kin kasheni da raina Hinde, duka 'ya'yana kika tura yo sata, wallahi mai rabani da ke sai Allah."

"Usaman (k'anin Baba) da matarsa suka zo rabo. Suka saki juna suna huci tamkar zakaru.

"Me ye haka kukeyi dan Allah, haba Innar Kamalu da Innar Anas, kunfa girma, kuna da surukai amma baku daina d'abi'an yara ba, to wallahi wannan abin Yaya kuke zubdawa da mutunci ba kowa ba a matsayinsa na babban Malami a garin nan."

"Usman wallahi wani abu ya sami 'ya'yana sai naga bayan Hinde koda zan tafi tsirara ne."

"Zakuwa ki tafi tsirara domin inda kika kwana na wuce da tafiya mai nisa"

"Haka kika ce?"

"Hak'k'un domin nasan da b'acin ranar nan na turasu kinga na rama lak'awa Kabiru satan kwan kajinki da kikayi shekaru goma da ya wuce inda kika janyo Malam ya illata masa kunni d'aya ya zamo baijin magana da shi."

"Tana nan dama kika b'ullo min Hinde?"

"Eh, dan ki sani yanzu raina tangaran."

Wani duka Asabe ta kaiwa bakin Hinde ta ke leb'enta ya fashe. Cikin gigita ta rarimi murfin tukunya ta wurgo mata ya sauka a gyeyar Usman wanda ya nemi janye Asabe. Ihu ya kwalla ya zube k'asa dafe da wurin, kuru-ruwa Matar ta sanya tayo kan Hinde suka rintsab'e da dambe.

"Innarmu! Ga 'yan sanda nan cikin mota tare da K'asimu fuskanci duk ta kumbura."

Atiku yaron Hinde ya shigo a guje yana fad'a.

Tamkar walk'iya haka Usman da Matarsa Mairo suka b'ace zuwa sashinsu ya yin da Hinde ta ruga d'akinta Asabe ta biyota ganin haka ta tureta da k'arfi ta fad'i k'asa ta kulle k'ofar da sakata.

Asabe ta mik'e cikin zundumawa Hinde zagi, ta nufi kofarta sai dai tana  saka k'afarta a d'akin ta tsinkayi muryan K'asimu na cewa "Ga d'aya can."

Da sauri ta waiwayo ta yi arba da macen 'yar sanda, K'asimu d'aure cikin ankwa.

Cikin zafin nama tayo kan 'yar sandan ta cukumeta da dambe bisa tsautsayi tAsabe ta ture 'yar sandan da k'arfi sai ko ta zame ta yi cikin rijiya wanda ke tsakar gidan.

Sautin ihunta tare da ba  fad'awarta ya janyo hankalin 'yan sandan da ke waje suka shigo a guje, Hinde da su Usman suma suka fito suna rafka salati jin abin da K'asimu ke ambata cewa Innarshi ta jefo 'yar sanda a rijiya.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[11/1, 9:32 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Mrsjmoon

E.W.F.

https://youtu.be/v9iNYDvS8JM

Pls 'yan uwa ku dannamin subcribe a YouTube d'ina.

Page 19.

Sadda na farka jikina ya yi k'arfi sosai sai dai yarda na hango idanun Mama sai na saka kuka dan sun kumbura suntum, damuwa ne kwance saman fuskanta abin da ya taimaka wurin karyarmin da zuciya. Jin kukana Hajiya Inna ta somamin fad'a, tsit na yi ina sauraren sababinta mai kama da na Baba saidai ita nata akan gaskiya ne sab'anin na Baba.

"Inna kiyi hak'uri."

"Bazanyi ba Hurera, shin abin da ya kamata ta yi kenan ko godiya ga Allah?"

"Hajiya Inna to na yi shiru dama Mama ce na hango cikin damuwa sai kuka yazomin."

"Duk shiri-ritanku iri d'aya, abu ba abu ba kuyi ta b'aran baki tamkar saunoni."

Murmushi na yi ta dunguremin kai, na kama yatsar zan tura a baki ta fizge tana dariya

"Mamana."

Na kira sunar cikin rauni ta taho a hankali ta kama hannuna kafin ta yi magana aka turo k'ofar Uncle ne da su Fanta suka shiga cike da farin ciki dan ko samun damar gaisar su Mama basuyi ba suka nufoni kowa na son isa inda ni ke. Hak'ik'a farin cikin da suka nuna na ganin samuwar lafiyana yafi gaban kwatance Mama sai sanya musu albarka ta ke yi bakinta har kunne Hajiya Inna kam fatar samun mazaje na gari ta yi musu, shi kuwa Uncle addu'ar da sukeyi masa na daban ne.

Sun sakani a tsakiya sai tsokanata sukeyi kamar yarda suka saba, duk rashin son maganarta yau kam na biye musu sai doka murmushi na ke yi cikin bawa kowacce amsa a hankali saboda yanayin k'arfiin jikina, lamarin da ya sake jefa Mama cikin farin ciki kenan domin ina hango motsa kai da ta ke yi cike da nishad'i.

Uncle na tsaye gefe daga bakin k'ofa Dr. Jalal na yi masa k'arin bayani game da lafiyar Deejah. Saurarensa kawai ya keyi ba tare da yana fahimtarsa ba saboda hankalinsa na kan masoyiyarsa shima sai murmushin ya ke dokawa yana jin natsuwa na daban na kuma nashe ruhinsa.

'Ina son yariyarnan matuk'ar so, ya Allah ka mallamin ita idan har hakan alkhairi ne.'

"Yaya inaga ka taho muje office zakafi fahimtar zantukana."

Kallon Dr. Jalal ya yi sai kunya ta kamashi ya wuce gaba da sauri Dr. Jalal ya sanya dariya mara sauti ya nufi wurin Deejah ya yi k'asa da murya ya ce "Ki rik'esa amana wallahi yana sonki da gaskiya."

Juya kai gefe na yi saboda zancen ya bani kunya.

"Dan Allah kubarta ta huta haka nan aminanta."

Dr. Jalal ya furta cikin sigan wasa. Dariya suka sanya ya fice yana murmushi bayan ya saukewa Fanta kallo na daban wanda faruwar hakan yasa ta rakashi da ido baki bud'e.

"Da magana a cikin kallon nan kenan ko sister."

Da sauri ta maida dubanta kan Safina.

"Eh da magana kam domin na hango k'auna a cikinsa."

"Kinga sister bana son kwashe-kwashe."

"Likitan ne kwashe-kwashe?"

"Ban sani ba."

"Aikam dole ki sani K'awata."

Na ambata cikin dariya ganin yarda ta tsare gira.
Chapter 33 · 0% Book details