Sashe 27
Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi Yaya nafiki bak'in ciki da ganin albarkansu haka nafiki son Hurera da wannan shegiyar su mace muci gado a bulis."
"Ki bari kawai Hinde ai ni a duk kwanar duniya sai na yi fatar samuwar sanadin macewar tumakan nan da lalacewar duk k'addarorin Hurera amma abin takaici tamkar taki ake yayyafa musu, ni lamarin har tsoro ya ke bani."
"Ai itama a tsaye ta ke bata gidan Boka bata gidan mugayen Malamai shi yasa duk asiran da muke b'atar da kud'ad'e wurin yi mata ya kasa tasiri akanta."
"Ai yanzu gashi muna zaune tasu tazo k'arshe, insha Allah Hurera bata warkewa haka wannan shegiyar daga wannan sumar sai dai ta jita cikin k'abari, rayuwar barzhu ya tabbata garesu."
Wani shewa suka tare da tafawa suka juya suka buga duwawo cike da farin ciki.
"Ai Yaya suna mutuwa kafin a kaisu zan tura Anas ya sungumomin uwar garken in kaita k'auye wurin Kaka na yi ta cin amfaninta hankali kwance."
"Nikam buhunan waken suyar nan na ke hari dan ko daren jiya na tura Kamalu ya haura ya satomin su sai wannan banzan Alhaji Muhseen d'in ya zo ya kwafsa dan iya mugunta har da saka 'yan sanda gadi wanda har yanzu zancen da na ke miki basu bar gidan ba."
"Oh ni 'ya su kajimin dan wahalar makwafci dai, ko ina ruwansa da lamarin gidanta?"
"Oho masa, amma ai ya tab'o Malam, ina mai tabbatar miki sai yaga bayarsa, duk dukiyarsa sai ya zamo tarihi, kuma ina bayarsa ya makashi a Kotu tunda banga dalilin shiga lamarin iyalinsa da ya yi ba yana k'aton baligi."
"Uhm Yaya ina tsoron kada Malam ya janyo mana fitina muna zamanmu lafiya kinsan dai yafishi kud'i da sanin manya."
"Ke dalla can matsoraciya kawai wallahi ni burina a kulleshi tare da manna masa kazafin yana lalata da Deejah kinga tunda yana da mata jefeshi za'ayi mu kuma mu tik'i rawarmu da shewa."
Wani dariya suka kuma kwashewa da shi tamkar tab'abbu.
Turo k'ofar akayi suka juyo idanu waje, tsira musu ido ta yi duk sai suka daburce, rashin gaskiya ya baiyana karara a tare da su
"Nagode zaku iya tafiya tunda kun gama nishad'in."
Hijabansu suka sanya suka fice kansu k'asa irin na munafukai.
"Mama wad'an nan mutane basu da gaskiya, rawa da guda fa nagansu ta window sunayi tamkar suna gidan biki, dalilin da yasa kenan na kirawoku dan ku gani."
Nurse da ta rakosu ta ambata cike da takaicin.
"Bakomi sunma kansu ne ai ciwo na kan kowa."
"Allah dai ya kyauta, wallahi dana san ba mutanen kirki ba ne bazan yi musu jagorar zuwa ganinta ba."
"Kada ki damu, koma bakin aikinki sai dai gaba a kiyaye wad'anda zasu nemi ganinta."
Uncle ya ambata a hankali.
"Insha Allah, Dr. Jalal ma ya saka wanda zasu kula da wanna gefen."
"Da kyau, hakan ya makata kam."
Kujera Uncle ya matsawa Mama da shi bakin gadon ta zauna idanunta cike da hawaye.
"Kada kiyi kuka addu'ar samun waraka zakiyi mata kamar yarda ta rik'a yi miki sadda kike kwance."
"To Alhaji amma kukan ne yakeyin kansa duk yarda na koreshi yak'i tafiya."
Ta amabata cikin muryan kuka.
Sauke kai kasa Uncle ya yi yana jin wani kalan tausayinsu na kuma nashe kirjinsa.
"Komi mai zuwa da wucewa ne Hajiya, ki daure kina ambatar addu'ar dana sanar da ke d'azun insha Allah dakiya zai rab'eki."
"To Malam, hak'ik'a bani da bakin gode maka sai dai na dauwama cikin nemawa rahmar Allah har zuwa ranar da ruhina zai bar gangar jikina zuwa ga mahaliccinsa."
"Ina godiya da wannan karamci, Allah ya sa damu da Rahmar Allah baki d'aya."
"Amin."
Uncle ya amsa ahankaki idanunsa na kan Deejah.
"Na k'ara yarda da addu'a takobin mumuni ne domin a dazun idan ancemin zan iya takawa da kafafuna zuwa nan zan musanta amma da zuwar Malam bayan ya gama yimin addu'a ina shan Zam-zam d'in nan sai narika jin tamkar ana kwanceni daga mugun d'auri, cikin amincin Allah na rikajin kuzari na kuma nashe duk kan gab'b'aina, kai madalla da samamuwarka cikin rayuwarmu, ina mika dubun godiya a gareku Allah ya rubuce zuwa gaban Ma'aikin Allah."
"Amin."
Suka amsa shi da Uncle.
"Itama yanzu zan jaraba sa'ata insha Allah bazata kai kwanakin da Likitoci suka ambata ba duk da nata ba nindaren aljannu."
"Allah ya taimaka."
"Amin Mamanmu."
Kallon Uncle Mama ta yi sai taji kunyar sunar ta sauke kai k'asa, shima kunyarta ce ta kamashi ya juya baya yana sosa sajensa.
Malam ya matsa gaban gadon Deejah ya ja addu'a mai tsawo ya tofa a robar Zam-zam ya guntsa ya fesa mata a fuska, bata motsa ba ya kuna fesawa duk bata motsa ba haka ya cigaba da yin addu'a yana fesa mata ruwan Zam-zam a fuska har sau bakwai sannan ya dakata yana sauke numfashi tamkar wanda ya yi gudu zuwa 'yan sakonni sai ta d'aga hannunta na dama da k'arfi ta maida ta kuma motsa kai cikin cije leb'e daga haka bata k'ara motsi ba, ta koma yarda ta ke tamkar gawa.
Hamdala Malam ya yi, ya juyo ya fuskanci su Mama da jikinsu ya gama yin sanyi da lamarin.
"Alamun masara kenan dama k'a'idar addu'ar idan ta motsa aiki ya yi kyau idan kuwa bata motsa ba har tsawon mintoci goma to koda ta tashi zata iya gamuwa da wani lalurar daban to sai gashi ta motsa ko minti d'aya ba'a samu ba, tabbas dole mu k'ara godewa Allah, domin mun rok'esa kuma ya amsa mana nan ta ke, Allah Alhamdulillah."
"Alhamdulillah."
Mama da Uncle suka ambata a tare.
"Hajiya anjima bayan la'asar Alhaji zaiyimin jagora zan shiga gidanki in sake yin saukar Alqur'ani da yarana sai mu rufe da rokon Allah akan ya baku kariya daga duk kan sharrin jinsin mutum da aljan duk da munyi hakan to zamu karayi akaro na biyu bayan kwana biyu sai mu zauna zama na k'arshe wato na uku inda zamuyisa kafin a sallamoku. Da yardan Allah kunyi ban kwana da duk kan sihirce-sihirce da akeyi muku a gida kuma idan Khadijatu ta warke zan rubuto mata addu'o'i wanda zaku rik'ayi bayan sallar subahi da magriba domin kara samun kariya daga mugaye."
"Nagode Malam, Allah ya biyaka da khairan."
"Amin."
Rakiya Uncle ya tafi yiwa Malam abinda ya bawa Mama damar yin kuka, ta kife kuskanta a tafin hannun Deejah ta saki kuka mara sauti, ji take tamkar ta dawo da laluran kanta.
"Allah ya tashi kafadarki Uwata, ina da buri mai yawa akanki, ina son naga Aurenki tare da zuri'arki, na goyasu tare da yi musu tawai, zuri'ar da ban samu ba ina burin na samesu ta fanninki, ki haifamin na gansu suna kiriniya a gabana, ya Allah ka saukar da salama zuwa ga baiwarka Nana Khadijatu ba dan halinta ba."
"Amin ya Allah Mama."
Dagowa ta yi Fanta ta fado jikinta tare da sakin kuka mai sauti.
Isowarta kenan da abinci Uncle ke sanar da ita.
"Fanta DAMUWATA mai tarin yawa ne, idan na rasa Uwata bansan ya zanyi ba, ita ce bangon dafawana, ita na ke kallo na sami farin ciki, hak'ik'a in ta tafi ta barni nima zan bita ne domin banga amfanin rayuwa babu ita ba."
Rufe mata baki Fanta ya yi tana girgiza nata kai hawaye na kuma b'ulb'ulo mata.
"Barni in fitar da DAMUWATA Fanta ko ya taima na sami sauk'in malolon da ya tokaremin k'ahon zucci."
"Mama ki ambaci sunar Allah shi ne maganin damuwarki sannan ki kwanta ki huta domin surutun sake jefaki cikin damuwa zaiyi gashi dama ba lafiya ce ta wadaceki ba."
Hannu ta kai fuskan Fanta tana share mata hawaye cikin motsa mata kai alamun aminta da kalamanta.
"Nagode Mama."
"Hak'ik'a kunyi tarayya wurin halayya sa Uwata shi yasa k'awancenku ya yi k'arko."
"Mama dan Allah ki taho ki kwanta a nan ki huta."
Ta ambata tare da nuna mata gefen gadon Deejah, tana mai zaunar da ita a wurin cikin lallab'awa, sai lamarin ya bawa Mama dariya ta murmusa ta damk'e hannun Fanta ta d'ora a saman na Deejah, ta tsirawa hannayen idanu cikin sauke numfashi zuwa can ya ce "Ko da na rasa Uwata dan kiyimin alk'awarin zamemin tamkar ita."
"Na yi miki wannan alk'awari Mama."
"Nagode, Allah ya yi miki albarka."
"Amin."
Ta amsa cikin sakin kukan da ta ke cijewa kada ya kufce. Rungumeta Mama ta yi tana sauke ajiyar zuciya saboda sunar Allah As-saburu da ta soma ambata cikin ranta ya taima wurin sanya mata jarumtar da batayi zaton samunsa ba.
*Duk wanda ya rik'e Allah tabbas shi kuwa zai ishe masa ga duk kan damuwarsa, mu daure muna mik'a lamuranmu ga Ubangiji mabud'in taskan Alkhairori. Allah ya yayemana dukkan damuwarmu alfamann Manzon Allah S.A.W*
*TALLA.*
*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*
Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)
*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/28, 1:52 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Mrsjmoon
E.W.F.
https://youtu.be/v9iNYDvS8JM
Pls kiyimin subcribe a YouTube channel d'ina.🖕
PAGE 16.
"Muyi hak'uri dai Fanta kuka baya maganin damuwa sai ma k'ara wa, ki tuna abinda kika sanarmin yanzu, shin me yasa zaki maida hannun agogo baya?"
"Mama Deejah ce kwance kamar gawa? Jiya fa muna tare lafiya lau, shi ne abin da ya bijiromin na kasa daurewa."
"To ya zamuyi da k'addarar Allah? Sai hak'uri kawai tare da mik'a lamarin garesa domin samun d'aukinsa ba dan iyawarmu ba."
"Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un."