← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 43

Sashe 17

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malama ki fito kije kiyimin abinda na ce."

Fitowa na yi jikina na rawa aikam Aunty Nafisa takawomin cafka na kwalla ihu tare da komawa cikin motar na kulle.

"Nafisa wallahi zan sab'a miki gaban ma'aikatanki.."

"Wallahi baku isa ba ku ci amanata ace bazanyi magana ba sabida mulkin mallaka, na rantse yau sai na lahira ya fita jin dad'i."

"Kika sake magana billahil azim saina baki mamaki, in kuma kince wasa ki sake furta kalma kigani."

A fusace Aunty Nafisa ta bar wurin.

"Fito muje ciki."

"Uncle dan soyayyarka da Manzon Allah ka barni inyima girkin a gidanmu."

Shiru ya yi na sakonnni sannan ya ce "Ok fito ki tafi can d'in."

Motsa kai na yi tare ficewa rik'e ledar da ya siyomin turaruka da wasu kayan da banfahimci meye su ba.

"Bakiji ba."

Cak na tsaya.

"Ki had'omin da zob'o drink d'in nan mai d'and'ano kinji?."

"Insha Allah."

Ina amsawa na yi gaba dama ban juyo ba koda na tsaya, ina ji ajikina kallona ya keyi shi yasa har na fice ban waigo ba.

"Tana da kyawun sura dana zuciya da yardan Allah ke d'in uwar 'ya'ya na ce."

Ya ambata cikin murmushi, ya juya ya nufi ciki, kafin ya shiga falon ya sauya yanayinsa zuwa fuskan shanu saboda tuno 'yar darun matarsa.

Nafisa na tsaye goye da hannayenta cike da masifa tana jiransa, yana shigowa kuwa ta nufesa cikin da baka'i ya yi hanzarin d'aga mata hannu cak ta tsaya tana kallon fuskansa sai jikinta ya yi sanyi bai kalleta ba haka bai furta mata kalma ba ya haye sama cikin sar-sarfa.

"Thank you Beebah da kika kawomin shawara mai kyau, insha Allah Azumin bana dake zamu tafi Umrah dan kin can-canci tukuici."

"Wato da jinina ka had'a baki ake son ganin bayana ko Abban Hafiz?"

"Zato zunubi koda ya zamo gaskiya dan haka ki kyautatawa 'yar uwanki zato."

"Bazan kyautata ba, wallahi sai naci ubanta shi yasa ta maida gidan tamkar gidan Ubanta a she tasan munafuncin da ta ke k'ullawa kenan? Shi yasa d'azun ta yi ta bani hak'uri to yanzu bata isa hanani zuwa na tijara Uwar Deejah ba, munafukan banza da wofi masu shiffan 'yan wuta kawai."

Ta kai k'arshen maganar cikin sauke nunfarfashi tamkar wacce ta yi gudu.

"Nafisa wallahi tallahi kinji na rantse idan kika kuskura kika fita gidan nan bada izinina ba sai kin tafi Maiguduri komin dare a yau d'in nna."

A razane ta ja baya tana kallon idanunsa ya kuma zare matasu cike da b'acin rai, kafin ta furta kalma ya shige bathroom tare da bugo k'ofar.

"Me suka bawa mijina ya daina lallab'ani? Me na ke shirin ji da gani idanuna biyu ba mafarki ba? Kalman saki fa ke shirin samuna dik akan wannan shegiyar yarinyar wacce bata isa komi ba. K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un!  Kishiya ni Nafisa zan zauna da ita? Kai wallahi sam ba zai yiwu ba, dik abinda zanyi sai na yi dan ganin ban zauna kishi da ko wacce d'iya mace ba."

A fusace ta fito d'akin ta shiga nata ta kulle ta d'auki waya rubutu ta yi na sakonnni ta tura tana ganin ya tafi ta cillar da wayar gefe ta mik'e tsaye ta soma kai da kawo tamkar mai nak'uda.

"Kai Nafisa matsala ce na yarda da zancenki Beebha ita d'in zuma ce shanta saida wuta, daga yanzu na sanja miki Nafisa, dik kika b'atamin zan rama dai-dai da abinda kikayimin na daina yi miki uzuri wanda sam bai amfanamin komi, ina kuma gode miki Beebah dan kin haskamin hanyar dawo da 'yar uwanki tunaninta."

Yana maganar ne cikin fesa turare a kan yallabiyarsa, yana gamawa ya sakko falon k'asa ya kunna TV ya kamo world sport, kwallaon da suke haskawa ya d'auke masa hankali, ya gyara zama cike da jin natsuwa domin ya sami bakin kashe rigimar Nafisa cikin ruwan sanyi.

***
Ina shiga gida kiran Aliyu ya shigo wayana da kallo nabi number har ya tsinke ban d'aga ba, wani ya sake shigowa sai na maida wayar silent, na iso gaban Mama na russuna wacce ke yanka alaiyahu.

"Sannu da dawowa Uwata."

"Yawwa Mama sannu da aiki."

"Yawwa."

"Ina Beebah?"

"Daf da zaki shigo ta fita."

"Ok, bari in hanzarta na samawa Uncle abinci dan ya rok'eni da in dafa masa wani abu."

"Me zaki dafa masa?"

"Ban sani ba Mama sai na shiga kitchen d'in tukunna zan duba."

"In zaici Tuwon Shinkafa da miyar Agushi da sai ki d'iba masa wanda na ke yi."

"Zaici bari in watsa ruwa nazo, zuwa lokacin miyar ta yi ai."

"Insha Allah ta kallama kam."

Daga haka na shige d'akina.

"Uwata manya, komi naki a tsare yake, rayuwarki abar koyi ne ga dibban Mata, Allah ya zab'a miki miji na gari wanda zai baki kulawa fiye da wanda na ke yi miki fatan samu."

Mama ta ambata cikin murmushi.

Saida na gabatar da sallar azuhur sannan na zauna shafa mai, na yi kyalliya kamar ko yaushe mai sauk'i na sanya gown na yi rolling da k'aramin gyale na fito na samu Mama ta kammala har ta killace na Uncle a kula mai kyau, jug na d'auka na zuba masa zob'o wanda Mama ta dafa ta saka a fridge kafin ta zuba a robobi. Kayan da zai k'ara masa d'and'ano na zuba na jerasu a kwando.

"Mama bari in mik'a masa."

"Tam ki dawo lafiya."

Baba maigadi na bawa ya tafi kai masa, ina tsaye ya dawo na yi masa godiya na juyo idanuna ya sauka kan Aliyu zaune a saman lipan d'insa sabuwa dal, nuno shi na yi da yatsa ina murmushi ya ko zabgomin harara dafe bakina na yi ina dariya k'asa-k'asa.

"Nagode Khadija."

Da sauri na kalle shi jin voice d'insa irin na mai fushi.

"Na kiraki baki d'auka ba, na zo gidanku kin sanyani gaba kina dariya saboda ni talaka ne banda mota da kyau, balle uwa uba kud'i to nago...

"A'a Aliyu kada kayimin wannan fahimtar tun bamuyi nisa ba."

Na katse shi cikin tsare gira.

"To wacce kike so inyi miki Khadija?"

"Ta karamci mai cike da yarda, ban son sake jin ka ambatamin kalamai masu nuni da bambanci tsakanin talaka da mai kud'i saboda ka san dukkanninsu bayin Allah ne, ba wanda yafi wani a gurinsa sai wanda yafi jin tsoronsa. Sannan kiranka na gani ban d'auka ba ne sabida ina son kammala aikin dake gabana yanzu kuma ina yiwa fushin da kayi dariya ne sabida baiyi maka kyau ba amma duka Ina neman affuwa insha Allah zan kiyaye gaba."

Murmushi Aliyu ya saki cike da samun natsuwar ruhi.

"Ya wuce dama ruhin Aliyu batayi fushi da abincinta ba."

"Ka ganka da iya tsokana."

"Ba tsona ba ce Matar Ali ke abaincin ruhina ce."

"Uhm ka dai bani kunya please."

"Kunya adon Mata, right?"

Harara na cilla masa batare dana amsaba.

"Affuwan na daina baki kunya kinji matar Ali?"

"Aliyu bakajin magana ko?"

"Bari in wuce zuwa yamma zan dawo dama yanzu na biyo zuciyata ce kuma na gamsu da abinda nagani, bye."

Da kallo na raka shi har ya b'acewa ganina.

"Uhm Aliyu kenan, shima salonsa kusan d'aya ne da Uncle, oh ni Nana Khadijatu ta haka soyayyar ta zomin? Allah ka zab'amin mafi khairan cikinsu."

"Amin Aminiyata."

Na tsinkayi muryan Fanta daf da kunnina, juyowa na yi ta saukemin duka a shoulder cikin cewa "Baki da kirki Deejah."

"Me na yi kuma?"

"Wato maimakon ki kawoma Uncle abinci da kanki sai kika aiko masa Baba maigadi."

"Fanta tsoron had'uwa da Aunty Nafisa na ke yi."

"To ai ko yanzu baki tsira ba dan shi ya aikoni da kizo da kanki."

Idanu na zare ta kwashe da dariya.

"Dalla matsoraciya, Allah ya ceceki ni Baba ya gani na amsa na kai masa falonsa saida na zuba masa ya soma ci sannan na fito."

"Nagode Aminiyata."

"Bakomi, muje na ci nawa dan ina zubawa Uncle ina had'iyar miyau."

Murmusawa na yi muka jera, muna shiga da Beebah mukayi arba zaune saman tabarma tana cin tuwo.

"Dama ba gida kikaje ba?"

Na jefo Mata tambayar.

"Eh naje layin baya ne na siyo mana fruit, ai ina kallonki kina soyayya na yi hanzarin shigewa gida dan bansan ya ganni."

"Saboda me?"

Cigaba da cin tuwonta ta yi kamar batajini ba. Wanke hannu Fanta ta yi da zauna sai nima na wanko, Fanta ta zubo mana muka soma ci, ina hankalce da Beebah yarda ta ke kallona ta gefen ido tana sakin murmushi.

"Da alama sister Beebah na son in daina kulata."

Na ambata cikin doka mata harara.

Dariya ta kyalkyale da shi wanda ya janyo hankalin Mama tafito a hanzarce.

"Me ya faru Habiba?"

"Mama bakomi kawai nishad'i na ke ji."

"To Allah k'aro nishad'i mai sanya nutsuwan ruhi."

"Amin Mama."

Fanta da Beebah suka amsa yayin da ni kuwa na yi tamkar bana wurin.

"Uwata ya dai?"

"Lafiyalau Mama."

"Anya? Nasan kina tare da damuwa."

"Mamana ina sonki matuk'a."

"Uwata kenan mai wayon sha-shantar da abinda na ke son ji."

Tashi na yi na kama hannunta muka shige d'akinta, cikin bedroom muka nufa na zaunar da ita a bakin gado ni kuma na janyo stool na zauna a gabanta, na marairaice fuska sannan na soma magana "Mamana bisa alamu hasashenki akan Uncle zai tabbata, ina jin tsoron abinda zai biyo baya gashi ruhina ta kamu da son Aliyu kuma bana son in bijirewa buk'atan Uncle ko dan tarin alkhairorinsa garemu sannan ina matuk'ar tsoron zaman kishi da matarsa. Mama dan Allah ki taimakeni ki sanar da Uncle ya yi hak'uri, nasan idan kika fad'a masa zai fahimta sama da ni."

Tsawon mintoci uku Mama ba ta yi magana ba.

"Mama nasan tunaninki Uncle zaifi Aliyu rik'eni tunda ya fisa sanin waceceni sai dai ina son kiyi nazarin rayuwar da zanyi a gidansa na rashin 'yanci da tarin fargaba."

"Uwata ko shi Alhaji Muhseen baisan komi akanki ba, abinda na ke so da ke shi ne ki barwa Allah zab'i wata k'ilama ba mijinki cikinsu.

"To Mama."

"Uwata ki kulasu duka, ki basu soyayyarki dai-dai misali, kada ki zafafa son wani cikinsu wanda rabuwarku zai zame miki k'alubale. Aliyu da kike ambata kina sonsa ban amince ba."

"Mama ban fahimta ba."
Chapter 17 · 0% Book details