← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 43

Sashe 24

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.*
[10/26, 10:33 PM] 💘: DAMUWATA
BY MRSJMOON

E.W.F.

Page 14.

A tare muka jera zuwa cikin asibitin duk kuwa da yarda naso ya yi gaba na biyo bayarsa ya k'i. D'akin ba kowa sai wata nurse domin na yi zaton zan sami su Baba a ciki. Nurse d'in na ganin mun shigo ta mik'e ta fice, na matsa ina lek'en fuskan Mama wacce  har lokacin barci ta ke yi, a kwana da yini har ta rame sosai sai dogon hancinta tare da fuakanta suka k'ara tsayi, haske kam wannan ba'a magana domin sai ta koma tamkar balarabiya wanda da ganinsa kasan bana lafiya ba ne. Sumba na sauke mata a goshi ina maida kwallan da ke neman zubomin.

"Ya rabbi ba dan halina ba ka bawa baiwarka lafiya alfarman Annabin karfo da k'arshe."

"Amin ya rabbi, insha Allah zata sami sauk'i burina ki cire damuwa domin ita kanta bazata so ta farka ta ganki cikin yanayi mara kyau ba."

"To Uncle zanyi k'ok'arin cirewa."

"Hakan ya kamata."

Shiru ya ratsa na minti biyu zuwa uku.

"Da alama wannan d'an ka iyan bai bar kowa ya shigo ba sai Malam."

Uncle ya ambata yana waige-waige kamar mai neman wani abu.

"Har shi ban bari ba."

Muryan d'an fitinan ya ratso, na juyo da sauri na tsira masa ido ya sanja sutura zuwa manyan kaya akan d'azun da ya ke sanye da k'anana.

"Kai wallahi Brother over acting d'in ka ne wata rana ke sanya mu b'ata da kai, yanzu har mijin nata ka hana shigowa ya ganta? To me kenan kayi fisabilillahi?"

"Eh fa har shi d'in banbari ba saboda kiyaye dokan Likita kuma a gabansu ya zo ya kuma tabbatar musu da kada wanda ya shiga ko waye nata."

"Wannan plan d'inka ne Brother domin nafi kowa sanin waye kai, inaga makaranta zaka koma ka zamo Likita akan Engineer tunda ka shiga rigarsu ta zartar da hukuncin da ko su basa yinsa wato hana murarrami ganin halalinsa."

Dariya ya fashe da shi yana rawa da kai na kuma zuba masa ido ina kallon dimful nasa da suka lotsa duka biyun.

"Yaya wallahi na yarda kafi kowa sanin halina shi yasa Abba ke had'ani da kai dan gano gaskiyan abinda na b'oye a ruhina."

"Ba dai ka kyauta ba Brother, a ce har mijinta ka hana shigowa ganin iyalinsa, haba dan Allah me yasa wata rana lamuranka baka sanya tunani cikinsa?"

"Kaima zaka fita idan ka cigaba da mita."

"Au har da ni?"

"Eh har dama Matarka mai kallon tsiya kamar goyon k'auyawa."

Uncle ya kalleni na juya baya ina mai maijin kunya.

"Kaga Brother zanci gidanku in ka ce zaka sanyawa iyalina ido."

"To ka sanar mata ban son kallo in ba haka ba zan tsire mata idanu sai ka zamo d'an jagora."

"Amsa naka na ce Sa'ad."

Jin Uncle ya ambaci sunarsa yasa na juyo da sauri na kuma tsira masa ido kamar mai son gano tawayarsa.

'Dama shi ne Sa'ad d'in?'

"Khadijatu meet my blood brother Sa'ad."

Maganar Uncle ya katsemin zancen zucci, kauda kai gefe na yi tamkar banji me ya ce ba saida ya sa ke mai-maitawa.

"Ok, ina yini?"

Na furta ina kuma kallon cikin idanunsa.

"Fine mai kallo k'urillah."

Murmushi na yi dan nafahimci yana da son raha kuma shima ya tsani kallo kamar yarda na tsana amma sai gashi yau ina yi har ana sanarmin da ba'aso lamarin da ya zamo karan farko cikin rayuwata.

"Kaga Brother zan sanya Abba ya yi maka aure da yar daji mai tallan Nono in har baka daina takurawa iyalina ba."

"Wallahi na bari Yaya domin ban shirya kashe 'yar mutane ba, good night, iyalin big brother Allah tashemu lafiya.."

Ya fice da sauri, kallon Uncle na yi ya girgiza kai tare da janyo kujera ya nunamin da yatsa na zauna ya dawo bayana ya dafa kujerar na kalleshi ya jinjinamin kai tare da cewa.

"Kinga na kori mai takura miki cikin ruwan sanyi."

Shiru na yi tare da kallon hawa da saukan numfashin Mama.

"Alamun ta samu lafiya kenan insha Allah wani abin cutarwa ya bar k'ara shigowa gidanku balle ya nemi tab'a ku."

"Allah ya amince hakan Uncle."

"Amin iyalina."

Murmushi mai sauti na yi saboda tun d'azun sunar ke bani dariya.

"Insha Allah ke iyalina ne Khadijatu."

"Uncle ka tafi gida kaga dare ya soma yi."

Na sauya akalar maganar saboda yarda ke bani kunya.

"Tare zamu kwana."

Idanu waje na ke kallonsa.

"Ko tun yanzu kina son nunamin Maman ke kad'ai ke da ita?"

"A'a fa kawai hakan bai kamata ba ne dubi da kana da iyali kuma na tabbata suna can suna dakon dawowar ka musanman ganin baka saba kaiwa dare a waje ba."

"Sun san inda na ke to ba damuwa."

"Uncle dan Allah ka tafi kada fa ka zamo mara adalci tun ba'ayi nisan zango ba."

"Oh da haka Kuma fa, nagode da tunatarwa, na tafi ki kula da kanki tare da Mama dan Allah."

Kai na motsa ina kallon fuskansa ya yi da ya ke tafiya da baya da baya saida ya kai bakin k'ofa ya d'agamin hannu  cikin cewa "Good night Iyalina."

Da kallo na raka bayarsa ina hasko wal-walar da ke kwance saman fuskansa abinda ya sanyani murmusawa tare da jin sanyi na shiga cikin ma'adanar halittar zuciyana.

"Uhm Uncle manya, sam baya duba girmansa sai ya yi tayimin abinda matasan samari ke yiwa 'yan mata."

'Shi ne So wanda ake kira mai maida tsoho yaro.'

"Aikam in haka ne to So babban kalubale ne a cikin rayuwar bil'adam, tunda yana maida mai natsuwa zuwa kishiyarta."

'Ke dai Deejah ki taka a sannu ka da reshe ya juye da mujiya.'

Idanu na zaro ina jinjina amsan da zuciyata ta bani. Gyara zama na yi cikin k'ok'arin kauda tunanin tun ban soma zamowa mahaukaciya ba. Sai dai abin mamaki fuskan Uncle da na d'an fitina su ne ke tamin gizo a idanu duka na kaiwa goshina ta ke na saki yar k'ara ina liliya wurin saboda zafin da na ji.

Cool music na jiyo nesa da ni mai taken soyayya, inda wayar ke haske na tsirawa ido saboda tun daren jiya rabona da ita.

"Uncle yazomin da ita kenan ko wa?"

Ringing wayar ta kuma na tafi da sauri na d'auka duk kuwa da bak'uwar number ce. Sallama na yi maimakon a amsa sai saukar ajiyar zuciya akayi tare da datse kiran baki d'aya.

"Wa ye?"

Ganin zan sanyawa kaina ciwo akan son gano ko waye sai na watsar da lamarin na koma gaban Mama na zauna na tsirawa hawa da saukan numfashinta idanu tamkar mai irgawa. Addu'a na yi ta karantowa Ina tofa mata zuwa wani lokaci barci ya soma kamani na tashi na kulle k'ofar tare da tofe ko wani sak'o na d'akin da  Ayatul kursiyu na haye gado na kwantar da fuskata a kirjin Mama ba jimawa barci ya d'auke ni.

***
Uncle Muhseen ko da ya isa gida bai shiga gidansa ba a k'ofar gidan su Deejah ya tsaya ya kira wayar Beebah bata daga ba ya nemi na Bintu a kashe , sai da ya kira duka wayoyinsu duk ba wanda ya yi dacen an d'aga, fitowa ya yi ya tura k'ofar gidan ta bud'e ya yi jim saboda tunaninsa a kulle zai sami k'ofar. Hasko shi akayi da filita mai mugun haske ya kare fuskansa hucin duka ya jiyo ya sunkuya da sauri hakan ya yabawa mutumin damar ficewa gidan a guje bayansa Uncle ya biyo amma ya nemesa k'asa ko sama ya rasa, kirjinsa na dukan uku-uku ya nufi cikin gidan, d'akin Deejah ya shiga ya samesu suna ta barci ajiyar zuciya ya sauke ganin babu alamun an tab'a su, ya fito waje yana haskawa da fitilar wayarsa buhunan waken suya ya ciki karo da buhunan waken suya an fito da su an jera.

"Ikon Allah wato barawo ne ya shigo sata, to wa ya bud'e masa gidan? Domin na tabbatar su Bintu sun kulle gidan tunda suka kwanta barci."

Komawa d'akin ya yi dai-dai lokacin Fanta ta tashi zatayi fitsari ganinsa saida ta tsorata dan batayi zaton ganin mutum ba, kiranta ya yi da hannu suka fito waje saida suka kai zaure ya ce "Kulle gidan ki tofa addu'a na shigo duba ku ne."

"To Uncle amma ta ya ka shigo alhalin mun kulle k'ofa?"

"Nima abude na gansa shi yasa na shigo duba ku."

"A bud'e kuma?"

"Kinga kulle ki tafi ki kwanta securities zasu zo gadinku insha Allah bakomi sai khairan."

"To Uncle saida safe."

"Ok mu kwana lafiya."

Yana tsaye ta kulle gidan shi kuma ya kira waya kimanin mintoci goma shabiyar 'yan sanda uku suka zo a mashin sun jima suna magana kafin ya barsu ya shiga motarsa zuwa gidansa.

Sallama ya yi a falon duk da yaga da duhu alamun babu kowa amma bai sanya ya shigo kai tsaye ba. Makunnin wutar ya latsa haske ya gauraye falon zama ya yi cike da gajiya ga yunwar da ta addabesa, mik'ewa ya yi dan samawa kansa abinda zai kori yunwar. Ja baya ya yi cikin razana da ganinta domin sam bai jiyo takunta ba sai gaminta ya yi tsaye gabansa.
Chapter 24 · 0% Book details