← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 43

Sashe 42

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke! Hurera shiru-shiru fa ba hauka ba ne, kada kiga na baki dama kina jefomin tambayoyi ki d'auka na zama mijin ta ce ne to ina nan a tsayena tamkar Nonon maza ban rankwafa ba ko na kafan allura dan haka wallahi ki shiga hankalinki da ni ko allura ta tono garma, sirrin b'oye ya fito fili a yi walk'iya kowa ya ga zahiri, idan kuma kin musanta to ki cigaba da tsayawa a gaba kina furtamin duk kalaman da suka zo bakinki ni kuma zan shayar da ke zumar mamaki ba Madara ba domin terere zanyi ma'ishi ban da abin kaico."

"Allah ya shirya ka."

"Amin, yin la'asar yafi miki ko inyi bankad'a, kuma dole ki bani wani kaso a dukiyarki domin dogaro da kaina ko in hau munbari na fed'e biri har wutsiya, in na ce har wutsiya to tundaga salsalan zan soma tareda bada damar duk wanda bai fahimta ba yazo na yi masa bayani gamsas-shiya."

"Malam me ka sha ne yau?"

"Abin da tunaninki ya baki."

Shiru Mama ta yi jikinta asake hakan da Baba ya hango ya sake bud'e mata wuta da barazana ta wani sigan mai tab'a zuciya wanda ya sanyani fitowa idanuna cike da hawaye na russuna gabansa na ce "Dan Allah Baba kayi shiru kaga makwafta na iya jiyo harshenka sannan ni ta kace tayimin duk hukunci da kaso ba mai hanaka dama kyawun mijin d'iya na farko ya zamo zab'in mahaifinta ne, na amince Baba ka yi sadaka da ni ga kowa zaka sameni mai biyayya ga zab'in ka ni dai fatana rashin jituwar da ke samuwa tsakaninka da Mama ya zo k'arshe, hankalin mahaifana ya dawo wuri d'aya yarda zasu kashe su rufe ba mai ji."

"Uwata ta shi ki koma d'akin ki bana son shirme."

"Mama kiyi hak'uri yau komi yazo k'arshe walallahi bana son wannan rayuwar da mukeyi na sababin Baba."

"Na ce ki koma d'akin ki ko ki tafi wurin Fanta."

"Da dai kin barta taji komi saboda lamarin ya shafeta kinga daga nan za...

"Malam na rantse da wanda ya haliccemu zan wulak'an...

"Mama ki bari, miji darajarsa daban ya ke nasan kin sani to dan darajar mai daraja Manzon farko da k'arshe ki daina d'aga harshenki sama da nasa domin hukuncin Allah zai sauka kanki kai tsaye batare da duban 'yancinki kike karewa ba."

"Allah ya yi miki albarka Uwata, nagode ainun da tunasarwa, maza tashi ki tafi wurin Fanta ina son samun masalaha da Malam."

Kallon Baba na yi ya zunkud'a kafad'a sai na maida kollon kan Mama ta murmusa tare da bani umurni da hannu wato na tashi. Mik'ewa na yi na koma d'akina na fito da hijab na yi waje amma ba gidan Uncle na nufa ba, titi na mik'e ina zantukan zucci ganin ina ta tafiya mutane na rakani da ido sai na tsaida mai Napep na sanar masa da inda na nufa wato gidan Baba Umaru domin kalaman Baba sun tsayamin a rai ina burin sanin fashin bak'insu a bakin Hajiya Inna domin na tabbata ta san komi.

'Fed'e biri har wutsiya, tereren bankad'a, abin b'oye ya fito fili, allura ta tono garma.'

Sune kalaman da na ke ta maimaitawa a cikin zuciyana, ina mai burin jin fashin bak'in su.

***
Deejah na fita Mama ta nuna Baba da yatsa cikin b'acin rai ta ce "Duk abin da ka shirya Malam tafi kayi amma ka sani hukuncin mai karya alk'awari zai hau kanka kuma zan kai k'ararka wurin wanda baya barci balle gyan-gyad'i wato Allah sannan ka tuna Allah na amsar addu'ar wanda aka zalunta nan ta ke, a k'arshe ina yima albishi da cewa Aurenmu guntilalle sunarsa dan na fahimci ka manta yarjejeniyarmu sanan kamar yarda ka tonamin asiri nima zan tona naka, muzuba shege ka fasa d'an halas sai yanka, zamuga wanda zaifi kunyata a idon duniya."

Baki bud'e Baba ke kallonta har ta dasa aya.

"Sharri zakiyi min ko me Hurera?"

"Au sharri ko? Tam ga fili ga mai doki ai wanda ya fasa aikata nufinsa ba d'an hakas ba ne."

"Hurera kinfi kowa sanin banda tambon abin ash-sha dan haka ki gama borin kunyarki ki dawo kan hanya domin ba mai hanani samun rabo a cikin dukiyarki."

"Sai Allah da ya haliccemu, shi ne zai hakana samun rabon nan."

Mama ta bashi amsa idanu soye cikin rashin tsoro na ban mamaki.

"Shi kenan muzuba mugani."

Ya ambata cikin buga babban rigansa.

Har ya juya zai tafi Mama ta bi bayarsa da sauri ta rik'o babban rigarsa ya juyo a fusace sai ta fad'a k'irjinsa ya ko rungumeta tsan-tsan yana sauke numfashi saboda duk tsiyarsa yana son Mama matuk'a, sun jima a haka sannan ya d'agota ta k'ara lafewa tare da yin d'age ta kai bakinta cikin kunninsa ta yi masa rad'a lamarin da ya sanya shi tureta yana gwama numfashi cikin nunota da yatsa sai dai ya kasa furta kalma saboda nauyin da harshensa ya yi.

Barin masa wurin ta yi jikinta a mugun sanyaye.

'Innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, Malam, a she dai shi d'in ne ba wani bare ba, wayyo ni Hureratu naga takaina, wannan wacce irin rayuwa ce na ke kan fuskanta? Ba laifi na ba ne, tun daga tushe bansan ta inda aka hau balle saukan amma k'addarar bata sanja zani ba, Allah Astagafirullah.'

Sune zantukan zuccin da Mama ke ambata har ta isa d'akinta ta yi masauki a bakin dago tallabe da kumatunta duka biyun, hawaye na bin samansu.

Baba kam zama ya yi a k'asa dab'as kamar kayan wanki dafe da k'irjinsa wanda ke bugawa da k'arfi, addu'a ma ya kasa ambata haka kunnuwarsa sun kasa yarda da abinda Mama ta furta masa, ya jima zaune sannan ya tashi tsaye ya k'urawa hanyar zaure idanu zuwa can harshensa ya motsa. 'Ta ya hakan zai faru? Kai dole na san inda kaina ke ciwo, wallahi ko zan rasa rayuwata ba zan bari Hurera ta fidda bak'in labarin nan ba, Anya Hurera bata da shafan shed'anu kuwa?.'

Amsar da baibawa zuciyarsa kenan ba ya zabura ya fad'a d'akin Mama a fusace.

Tana ganinsa ta mik'e ta bi gefensa ta fice zuwa d'akin Deejah ta murza key saboda in har ta tsaya za'a iya haifar d'a mara ido dan ta tabbata yarda ta kekijin zugi a zuciyarta abin da bai tab'a faruwa da su ba shi ne zai afkuwa wato fad'a da duka.

***
Ina isa k'ofar gidan Baba Umaru kiran Mama ya shigo wayana na d'auka tare da sanar da ita inda na tafi.

"Uwata kada inji zancen komi ya fito abakinki idan har kina son zaman aurena da Malam ya yi k'arko."

Shiru na yi zuciyata na kuma d'aukan zafi.

"Idan kinsan ba wanda ya ganki to ki juyo domin kina shiga Hajiya Inna zata gano da matsala ta sanarwa da Baba shi kuma ya yi alk'awarin raba aurenmu duk in wata matsala ya kuma fillowa a tsakaninmu, na san kinfi kowa son zamammu da Malam ya d'ore."

A jiyar zuciya na sauke tare da cewa mai Napep "Juya dani inda ka d'auko ni."

"Allah ya yi miki albarka."

"Amin."

Na amsa cikin rawar murya.

A kwanar fita layin motar Kawu Habibu ya sha gabanmu, k'iris ya rage  bamu fad'a masa ba salati muka ambata da k'arfi, ni da mai Napep

"Kalli wani banza dai."

"Yi hak'uri Malam Kawuna ne."

"Amma dai bai da lafiya ne ko?"

Ban amsa masa ba na hango fitowar Kawu, yana isowa ya mik'awa mai Napep dubu d'aya tare da cewa "Sauketa, Allah bada sa'a."

Godiya ya yi masa amaimakon zagi dana zata zai auna masa tamkar yarda ya soma

' Kud'i kenan, masu gidan rana.'

Na ambata cikin raina sannan na fito na shiga motar, maimakon mu nufi hayar gida sai ya juyo dani gidan Baba Umaru.

"Ka kaini gida ne Kawu."

"Hajiya Inna ta umurceni da in kawo mata ke domin Annur yaron Yaya Shafi'i ya sanar mata da zuwarki tare da komawarki batare da kin taka k'ofar gidan ba."

Lumshe ido na yi ina tunano abin da zansanar mata domin kare martaban auren Mama wanda na ke burin ganin ya inganta har zuwa mutuwa.

"Ina son Mata mai halayyaki Khadija."

Ban bud'e ido ba amma na tabbata kallona Kawu keyi.

"A yau kuma a yanzu na k'ara nutso da son k'ara aure da mai kamanninki sak ko da ta hayayyane ba sai lalai mai siffarki ba."

Zillo zuciyana ta yi na bud'e ido da sauri na kafeshi da su.

Dariya ya kyalkyale da shi tare da dukan steering, na yi kwal-kwal da ido zan fashe da kukan dama na ke cikinsa, ya yi saurin kunna wayarsa karatun Qur'ani ya bayya cikin sural Ankabut. Lum na yi ina bin karatun cikin raina ina maijin natsuwa na rab'ata.

Sautin fitar murmushinsa yasa na kalleshi ya motsamin kai "Duk kan damuwa maganinsa na cikin sauraren zancen Allah ko tilawarsa dan haka kada ki sake damuwa ya yi sanadin rayuwarki abanza batare da kin cikawa Mamanki burinta ba na yiwa 'ya'yanki tawai."

"Nagode Kawu da kayi sanadin natsuwa ya nashe ruhina."

Jinjina kai ya yi tare da yin parking a k'ofar gidan sannan ya maido hankalinshi kaina ya ce "Ba Hajiya Inna ta ce in daukoki ba ni da kaina naga zuwarki tare da komawarki shi yasa na dawo da ke domin inji dalilin zuwarki sannan kika koma batare da kin shiga cikin gida ba."

"Kawu yawan bincike haramun ne to ka barshi a sirri ne."

"Shi kenan Dije na bar kaza cikin hashinta domin kada in figeta na gano kwarangwal ce."

Murmushi na yi jin yarda ya yi zancen cike da tsokanar da ya saba.

"Yanzu taho muje ki gaida su sai in maidaki gida."

"Hajiya Inna zata tambayi inda muka had'u kuma kasan ban iya k'arya ba."

"Haka ne shi yasa na ke k'aunarki tamakar rai da ajali."

"Kawu dan Allah ka bari wallahi zanyi maka kuka."

"Oya maza kiyimin kukan tsun-tsu Kanari ni kuma na shagala da saurarenki na yi ta dilalan yamu tamkar dolo."
Chapter 42 · 0% Book details