← Book details Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 43

Sashe 31

Damuwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In wannan ne ai ba wanda ya kaika murna."

"Me kike nufi da zantukanki Asabe!?"

Ya furta cikin fad'a tare da fitowa waje.

Ja baya sukayi ya watsa musu mugun kallo ya koma d'akin yana ta sababi wanda basa fahimtar me ke cewa.

Jan hannun Asabe, Hinde ta yi suka shige k'uryan d'akinta gudun kada ya jiyo abinda zasu tattauna.

"Yaya wallahi ki daina kaini bango kada wata rana na tona asirin dake birne."

"Hinde wai har sai yaushe zaki daina yimin barazana kina doramin alhalin mutuwar Jaririn da tuncan a matacce ya iso duniya?"

"Yaya wallahi ke kika kashewa Hurera d'a dan najiyo kukansa amma kafin in shigo kin aikata mugun nufinki."

"Ikon Allah, a she har yanzu sharrinki bai ragu ba Hinde saima k'aruwa?"

"Sharrinmu dai zaki ce."

"To naji nina kashe Jaririn Hurera amma aikema kinyi mata asirin da bazata sake haihuwa ba tare da sanyawa Uwani bak'in jinin rashin mijin aure."

"Au haka bokanki ya sanar miki da ni ce na aikata wad'an nan aiyukan?"

"Ko me zaki ce na tabbata ke ce kikayi su."

"Bilahil azim ban shiga lamarin Uwani ba na sandai na kashewa Hurere kwayoyin halittar haihuwa."

"Oh a she kema kin aikata kisan kan kenan?"

"Ni kam Yaya ba wannan zancen ya sa na janyoki muyi ba dan Allah mu rufe babinsa tunda duk munsan gaskiyan muna yiwa Hurera zagon k'asa tsawon shekaru kuma har yau bamuyi nasarar ganin bayanta ba."

"Naji, ina sauraren dalilin janyoni k'uryan d'akinki ya ke jikan iblis."

Dariya Hinde ta yi sai kace wacce aka ambatawa sunar arziki ta ce "Yaya matso ki ji abinda na shirya a game da zancen zuwar Malam gadin dukiyan Hurera."

Da sauri Asabe ta kai kunninta daf da bakin Hinde, zuwa can suka shek'e da dariya tare da tafawa.

"Hinde a gaskiya ke d'in shu'uma ce ta k'arshe."

"Kiyi shiru kawai mu jira baiyanar sakamako wanda zamu kwashi rawar d'aga buje, muci kaji mu more a cikin dukiyar bulus, bamu tara ba amma munfi mai ita cin moriyarta."

Wani shewan suka kuma sakawa har da daka tsalla tamkar yara.

***
Iya gigicewa Aliyu ya yi ganin halin da Masoyiyarsa ke ciki tsakanin rayuwa da mutuwa. Sai kallon na'urar da ke nuna tana da rai ya keyi tamkar ya tafi ya latsashi ta dawo hayyacinta.

Mama sai kallonsa ta keyi tana tantance natsuwarsa.

'Shi da Alhaji ko wa ye mijin uwata cikinsu oho?'

Ta ambata cikin ranta.

Kasa jurewa ya yi ya fice daga d'akin, ya zauna gefe ya dafe kansa, Salma tazo ta tsaya gefensa saboda itama lamarin ya tab'a ranta.

Beebah ce ta matsa daf da shi wacce ta biyo bayansa ta ce "Duk halin da muke ciki kenan Aliyu, kayi hak'uri insha Allah zata dawo hayyacinta."

"Allah ya amince hakan."

"Amin."

"Na yi ta kiran wayarta bai shiga naki kuma baki d'auka."

"Wayarta ba asan inda ta ke ba nawa kuma na dakinta an kulle."

"Ayya nima na sami k'aramin hatsari ne jiya da Rana."

"Sannu Allah ya baka lafiya."

"Amin."

"Zan wuce."

"Ok Agaida Hajiya"

"Zataji."

"Sister sai anjima."

"To Allah ya kara musu lafiya."

"Amin, mungode."

Beebah ta dawo d'akin jikinta a sake saboda hango k'aunar Deejah mai tsanani a idanun Aliyu da ta yi.

'Allah ya baki lafiya Deejah.'

Ta furta cikin ranta.

Aunty Nafisa kam jikinta ne ya yi mugun sanyi dan ita sam bata kawo haka jikin ya yi tsanani ba, mugun nufinta kauda shi gefe ta yi ta ja kujera gefe da zauna tana nazarin rayuwa.

Su Bintu ba su bar Asibitin ba sai bayan sallar magriba lokacin da Hajiya Inna ta zo. A hanya ba wanda ya yi magana hatta Aunty Nafisa ta kame bakinta. Sai da suka shigo layin gida sannan Beebah ta ce "Ita dai rayuwa wata aba ce mai ban mamaki yanzu ka ke mutum anjima ka zamo gawa dan haka mu aikata khairan domin bamusan aya mutuwa zata riskemu ba."

"Zantukanki abar yin nazari ne sister, Allah ka sanya-ya mana zuciya."

"Amin Fanta."

Suka amsa Banda Aunty Nafisa da ta yi nisa cikin tunanin yarda zata raba mijinta da Deejah cikin ruwan sanyi.

Uncle suka samu zaune a falo tare da yara wanda sukayi barci a saman jikinsa. Duk a falon suka zauna tare da gaisar da shi ya amsa cikin tambayarsu jikin Deejah.

"Da sauk'i amma na musulinci."

Fanta ta ambata cikin rawar murya.

"Insha Allah zata tashi cikin lafiya."

"Allah ya so hakan."

Suka amsa masa.

Siririn tsaki Nafisa ta ja suka kalleta sai kuma suka mik'e a tare suka bar falon.

"D'auki yaran nan ki kaisu d'akinsu."

Banza ta yi da shi ta mike ta haye sama. Girgiza kai ya yi yana jan Mata shiriya cikin ransa, yaran ya d'auka ya kai d'akinsu.

Har ya kwanta ganin Aunty Nafisa ta shigo sai ya sauka ya fice d'akin da sauri ta biyosa amma kafin ta cinmasa ya fice falon baki daya.

"Me hakan ke nufi? Abban Hafiz na nufin na zamemasa dodo kenan?"

'Ga alamu nan kin gani.'

"Wallahi bai isa ba."

Ta bawa zuciyarta amsa cikin fushi.

Da takaicin ya isheta sai ta zube saman kujerar falo ta fashe da kuka mai sauti wanda har su Fanta na jiyota amma ba wanda ya yi yunk'urin fitowa.

Uncle  kuwa ficewa daga gidan ya yi baki d'aya saboda baya muradin sauraren zantukan Nafisa wanda ke saka masa ciwon kai. Daga inda ya ke tsaye yana hango duk abin da ke faruwa a k'ofar gidan su Deejah.

"Wallahi ina tausayin halin da kike ciki Khadijatu, Allah ya tashi kafadarki lafiya alfarman Manzon Allah S A.W."

Ya furta a hankali. Wayar Dr. Jalal ya kira sun jima suna tattauna yarda jikin nata ya ke. Ya kashe wayar ya juya zai shiga gida yajiyo tsayawar mota waigowa ya yi samari biyu ya hango sun fito a cikin motar na d'aukan kaya wato mai budadden baya wacce ake kira da akori kura. Gidan su Deejah suka shiga ya ware ido yana mamakin daga inda suka zo. Kimanin mintoci biyar da shigarsu suka fito kowa d'auke da buhun waken suya a bayansa da alamu a kwai wanda ya d'ora musu aciki. Gyara tsayuwarsa ya yi cikin sake shiga mamaki, yana nan har suka gama zuba buhunan waken wanda suka cika motar taf. Ganin zasu tafi ya isa wurij da hanzari duk suka sakko suna kallonsa cikin alamun rashin gaskiya.

Sallama ya yi musu suka amsa cikin muryan mashaya.

"Wa ya turoko d'aukan kayan?"

"Mamallakinsu."

Suka amsa a tare cikin cijewa na 'yan daba.

"Wa kenan?"

"Mai gidan."

"Baba ko Mama?"

Nan fa sukayi shiru zuwa can dayansu ya amsa "Mama."

"Ok kud'an bani mintoci biyu."

"Muna sauri ne Malam bazamu iya jiranka ba."

"Ok to zaku iya tafiya amma ba da kayan ba."

"Yallab'ai me kake nufi?"

Cigaba da danna wayarsa ya ke ta yi wanda tun soma yi musu magana ya fara.

Kallon juna sukeyi sai suka koma saman motar tare da bawa driver umurnin tafiya. Yana kunna motar wata mota ta gyara parking a gabansa, kafin samarin su san abinyi 'yan sanda sun kamasu sun tura cikin motarsu har da drivern.

Hannu Uncle Muhseen ya d'agawa 'yan sanda dan su tafi saboda ya sami wayar Dr. Jalal.

"Kaiwa Mama please."

"Ok ganima tare da ita nazo bata magani."

"Had'ani da ita."

"To gata."

Gaisheta ya yi cikin girmamawa ta amsa itama cikin girma.

"Mama kinyi magana ne azo a kwashe waken suyar da kika ajiye?"

"A'a."

"Ok to ya jikin naki?"

"Alhamdulillah."

"Na Khadijatu fa?"

"To angode Allah dai."

"Insha Allah muna tare da nasara."

"To Alhaji, nagode sosai da kulawa."

"Bakomi Mama masu iya magana sunce yiwa wani yiwa kai."

"Haka ne, Allah ya rubuce."

"Ami, sai da safe."

"Allah ya tashemu lafiya."

"Amin."

Wayar Mama ta tsirawa ido.

"Tabbas da abinda ke faruwa amma tunda ya nuna bai son fad'amin na barwa Allah lamarin, Allah yasa khairan ne."

"Amin."

Dr. Jalal ya amsa.

"Likita wai me ye ma'anar wannan k'aran da wancan na'urar keyi wanda kika sanyawa Uwata?"

"Shi ke nuna tana da rai."

"Ikon Allah sai kallo."

"Kuma idan kin lura da kyau zakiga tana sauke numfashi sai dai in ta yi d'aya tana d'aukan sekonni kafin ta k'ara amma duk ba matsala ba ne insha Allah zata tashi cikin k'oshin lafiya."

"Allah ya nunamin wannan lokaci."

"Amin."

Shigowar Hajiya Inna ya bawa Dr. Jalal daman barin d'akin. K'aramin Qur'ani Hajiya Inna ta mik'awa Mama ta amsa tare da yi mata godiya.

"Ya zamo shi ne abin yin bitarki Safe, Rana Dare domin duk kan waraka yana cikinsa, duk in kin idar da karatun kiyi tawassali da sunayen Allah d'ari ba d'aya ki rok'a mata sauki, insha Allah zakiga rahma na samuwa gareta tare da ke kanki."

"Nagode Inna, wallahi kunyimin duk kan komi, bazan tab'a mantawa da ku ba cikin farihin rayuwata, Allah ya saka muku da gidan Aljanna."

"Amin, kada ki samu ke d'iyarmu ce tamkar Habibu haka muka daukeki."

Kuka Mama ta fashe da shi Hajiya Inna ta matsa ta dafa kanta ta soma tofa mata addu'a, rungumeta Mama ta yi ta cigaba da kukan wanda damuwar halin da Deejah ke cike ne jigon yinsa.

Uncle Muhseen kam suna gama wayar ya kira wasu matasa suka maida waken ciki ya sallamesu ya koma gidansa ya d'auka kwad'o ya kulle gidan inda anan yaga wanda suka yanke da zarto. Tuno yarda sukayi da Baba yasa shi kiran number da ya amsa wurin Mama sai dai ya kira wayar nasa har sau biyar ba'a d'aga ba kallon agogon wayarsa ya yi yaga k'arfe Sha d'aya saura.

"Dare ya yi dana tafi gidanka na sanarma da abin da ke faruwa amma insha Allah gobe da subahi zan isa masallacin da kake limanci muyi maganar dan bana son muna samun sab'ani a matsayinka na mahaifin wacce na ke burin ta zama uwar 'ya'yana nan gaba."

Ya ambata cike da damuwa ganin dare na k'arayi sai ya koma gida cike da takaicin rashin aikinyin da ke jefe matasa cikin halin sace-sace gami da shaye-shaye.

*TALLA.*
Chapter 31 · 0% Book details