← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Awa biyu ta d'auka kafin ta tashi ta fito daga d'akin, cuisine ta nufa dan tunawa da tayi tana cikin d'ori ne ya kirata, tayi mamakin ganin gas a kashe tasan shi ya kashe dan haka ta koma d'akinta ba tare da ta bud'a tukunyar taga abinda ke ciki ba, ko wanka ba tayi ba ta kwanta saman gado taci gaba da kuka da k'unar zuci.
12:20 taga zaman ba zai gyarata ba ta fito ta shiga cuisine ta fara girkin rana, tsananin yunwa da zafin jiki ga ciwon kai duk ya taru ya mata yawa, haka ta kammala girkin da k'yar kamar zata mutu.

Tana idawa ta koma d'aki tayi sallah ko wanka ba tayi ba saboda raunikan dake jikinta, tana kwance Salman ya shigo d'akin yace" wa kika aje da zai zuba maki abincin" fita yayi bai jira amsarta ba tashi tayi tabi bayanshi, tsaf ta zuba masa shinkafa da miyar kayan cikin ragon da tayi, bud'a ciki yayi ya ci abincin sosai, yana kammalawa yayi wanka ya fita b
tare da ya bi ta kan Ummi ba.

Abun ya k'ara tsananta ma Ummi kamar za tayi hauka ta keji, ga zafin ciwo da rad'ad'i ga ciwon kai saboda kukan da take sha ga bakin ciki da kad'aici, tuna dukan da Salman ya mata yasa ta shiga cuisine dan sarrafa abincin dare, macaronie da miyar naman rago ta dafa d'an kad'an wanda zai ishe su.

Da k'yar ta watsa ruwa dan ciwon da ke jikinta ba zai bari ta cud'a ba, d'aure take da towel tana ta kai da kawowa saboda wani sabon rad'ad'i da take ji, mai ta shafa tasa turare gajeran wando tasa iya cinyoyinta sai bras da ta saka wanda taji kamar ma karta saka, maganin da Salman ya siyo mata tasha sannan ta kwanta ba jimawa bacci ya d'auketa.

Kusan awa biyu kenan da Salman ya shigo gidan amma babu ko motsin Ummi, abinci kawai ya ke so yaci amma ya k'i zubawa yana jiran Ummi, a hankali ya bud'a k'ofar d'akinta ya shigo, k'ura mata ido yayi yana k'are mata kallo tas, duk da shatin bulalar da ya gani ya fito sosai a jikinta duk jini ya kwanta ga manyan birridda duk a bayanta ya kwanta, tausayinta ya ji ya kama shi sai yaji baiji dad'i ba lokaci d'aya kuma ya ji wani abu yana tsargar masa tun daga kwanyar kanshi har babban dan yatsan k'afarshi, yana jin abun yana k'ara girmama yana fizgar shi kamar zai aikata wani abu yasa ya daddab'a k'afarta, a hankali ta juyo da kanta sannan ta tashi zaune tana murza fuskarta cikin tattausan murya yace,
"Wa kika aje da zai zuba min abincin?ko ni kike so in zuba da kaina?juyawa yayi har ya kai k'ofar d'akin ya tsaya ya juyo yana kallanta, ganin bata taso ba yasa yace" wai ba kiji ne ina maki magana?" a hankali tace" ina zuwa riga zan saka" kenan sai na zaune ina jiranki harki gama, kinsan awata nawa a gidan nan ina jiranki,ko so kike yinwa ta kashe ni?" yin k'urawa tayi ta tashi ta nufi drower, tsawa ya mata da k'arfi" ke wai ba da ke nake ba da za kice sai kin gama abinda kike, ko wata tsiya ce a jikin naki da zan kalla?dallah wuce mu tafi" ya mata alama da hannu wucewa tayi sub'ur sub'ur k'ugunta na kad'awa harda kakkaryawa bayanta keyi, kamar baturiya haka ta dinga kai da kawowa tana zuba masa, duk da hankalin sa na a waya amma saida zuciyar shi ta fizgi idonshi izuwa shagalta da kallonta musamman ma kunkuminta da k'irjinta sun matuk'ar tafiya da shi, tana zuba mashi ta kama hanya zata koma d'aki ji yayi zata rage masa jin dad'i dan haka yace" zo ki zauna nan" cikin shagwab'a ta kalleshi tace" yaya Salman kayi hak'uri na sako riga" zo nan nac
e" dole ta zo taja kujera nesa da shi ta zauna tana ta b'oye k'irjinta, shiru babu mai magana hakan yasa Ummi ta d'auki robar madara akan dinning ta fara sha cikin d'ari d'ari, ana cikin haka hadari ya taso iska aka fara da k'arfi, Ummi duk ta k'agu ta tashi Salman ko ko a jikinshi abincin shi yake ci hankali kwance, wutar da aka d'auke tare da sako ruwa mai k'arfi yasa Ummi matso da kujerarta kusan Salman, tunda ya lura a tsorace take kawai sai ya k'i kunna hasken wayar shi, tsawar da akayi irin mai sa hanjin mutum kad'awa yasa Ummi mak'alewa a jikin Salman ta lakayo da hannunta ta wuyanshi rik'e da robarta a hunnu tana fad'in" yaya Salman tsoro nake ji, dan Allah muje d'aki" bai tankata ba saidai duk tasa jikinsa yayi sanyi saboda yanda k'irjinsu ke had'e.

Ba tada niyar sakinshi dan haka ya kama hannunta ya kaita d'akinta, amma ina tace ai ba zata zauna ita kad'ai ba, harya aje mata wayar shi kuma yaga shi ma baya gani dan haka ya zauna gefen gadonta yana satar kallonta har bacci ya d'auketa, lullub'eta yayi da zanin rufa yana kallonta yana girgiza kai fitowa yayi ya koma d'akinshi yana fad'in" jaraba bacci da madara a hannu, kamar wata yar shekara biyu a duniya, ai ko mai shan nono ba za tayi wannan jaraba ba."tsaki yayi ya kwanta kafin bacci shima ya d'auke shi.
28/02/2019
17:02 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah_ )
*Page*
Ummi tayi nisa a cikin baccin taji ana tsawa, zunbur ta tashi zaune tare da rik'e robar madarar da tasha bacci ya d'auketa daga nan, ganin babu wuta a d'akin sai duhu yasa ta fara k'ara tana fad'in" yaya Salman, dan Allah ka zo, wallahi tsoro nake ji, dan Allah kayi hak'uri ka zo, Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un shikenan mutuwa zanyi" shiru tayi dan tasan ba zai zo taimaka mata ba zanin rufa taja ta k'ank'ame a ciki tana rawar jiki.

Cike da k'asaita ya shigo d'akin da wayar shi a hannunshi, gefen gado ya ajeta ya zauna ya mik'e k'afafunshi saman gadon ya jingina bayanshi tare da rumgume hannayenshi a k'irjinshi sannan ya kalleta yace" haka ya maki?nasan za kice tsoro kike ji ba zaki iya bacci ke kad'ai b
ana ruwa, to gani sai ki kwanta yanzu." ya k'arashe maganar da hararenta turo baki tayi a hankali ta sulale ta kwanta tare da gyara rufarta dan-danan bacci ya sake gaba da ita.

Makara yayi wajen tashi ko da Salman ya farka gari har yayi haske sai lokacin yaga yanda ya kwana daga zaune, juyawa yayi ya kalli Ummi sai yaga ba tanan mamaki yayi ta tashi amma ni ta k'yaleni, tashi yayi ya nufi d'akinshi ya nata matsar wuya saboda ciwon da yaji yana yi masa, sallah yayi ya sako kayan sport ya fito dan ya yaje bayan gidan a wani hankad'ed'en d'aki in da yasa aka gyara shi ya zuba kayan motsa jiki, Ummi ya gani tana Aje kwanuka a dinning ba tare da ya tsaya ba yace" ki biyo ni da jus mai sanyi" jiki na rawa Ummi ta bud'a fridge ta d'auko dan yanzu kam harga Allah tsoron Salman ya kamata, saida ta kai farfajiyar gidan saboda sanyin da taji na ruwan da aka sha jiya ta tuna doguwar riga ce a jikinta wacce ta d'ora a kayan da ta kwana da su, juyawa tayi da nufi ta d'auko hijab Salman ya juyo yace" zaki wuce ko sai rai ya b'ace" wucewa tayi da saurinta harya bud'a d'akin suka shiga, kallo Ummi take sosai yanda aka k'awata wajen mik'a mashi jus d'in tayi dan ta koma in da ta fito, hararan daya mata yasa ta sunkuya ta aje ta tashi zata fita yace" zo nan, kinga waccen k'arfen shi nake so ki d'auko min" kallan k'arfen tayi taga ko zai kasheta ba zata iya d'aukarshi ba,dan haka ta juya ta kalleshi tace" yaya Salman ba zan iya d'aukar shi ba wallahi" wata kyakyawar waya ya d'auka yana shirin zuk'a mata ta nufi wajen k'arfen a guje ta fara 'ko'karin d'aga shi, ganin ta kasa yace ta d'auko na kusa da shi shima bata d'auko ba saida kanshi yazo ya d'auka ya fara d'agawa k'wanji na fitowa da jijiyoyi haka ta saki baki tana kallonshi, yana gamawa ya d'auki ball ya fito tsakar gidan ya fara bugawa, haka kawai Ummi taji tana san ta yita kallonshi yanda yake ball d'in da kuzari da salo, Salman na ganin ta saki baki ya jefo mata ball d'in da nufin koda ta sameta ta sameta a in da b
za taji ciwo ba, sai ko a fuskar Ummi ji kake Timm ball ta mare ta, duk'ewa tayi tare da rufe fuskarta, jin ba tayi k'ara ba yasa Salman tunanin ba taji zafi ba, d'aukar ball d'in yayi ya ci gaba da bugawa saida yaga Ummi ta jima bata d'ago ba ya zo kusa da ita, sunkuyawa yayi ya d'ago da kanta take gabanshi yayi wata mummunar fad'uwa saboda ganin idonta na dama ya kumbura ga jini ya kwanta abin tausayi" oh mon Dieu, pardon Ummi kinji bansan haka zata faru ba dan Allah kiyi ha'kuri" hawayenta ta goge ta mike tsaye tace" ba komai akwai Allah" wucewa tayi d'akinta nan ta fara sabon kuka kamar da bakin k'warya.
Chapter 9 · 0% Book details