Sashe 42
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Salman kanshi yanzu duk wani abu da zaiyi mai mahimmanci to saiya shawarci Ummi akai, akwai lokacin da wani mutum ya bashi fili a maimakon kud'in da yake biyarsa, suna zaune da Ummi ya kira Khamis yana fad'a mashi cewa bai san yanda zaiyi da filin ba, dan haka kawai ya samo masa mai siya ya sayar dashi, Ummi na jin haka tayi shiru saida suka kammala hira ya kashe waya sannan ta gyara zama tana kallonshi cikin nutsuwa tace,
"Mon sweet, saina ji kamar kuna magana akan zaku siyar da filin ko?"
"Eh, ina so in siyar dashi, dama na karb'a ne saboda in ban karb'a ba to bai zama lallai kud'in su fito ba."
"Amma da ba zaku damu ba da nace wani abu?"
Murmushi yayi yace "damuwa kuma, tame kenan? fad'i kawai ina jinki."
"Sai nake ganin fili kadarace bai kamata ku siyar ba, wanda ya baku shi ya baku ne saboda rashin sanin mahimmancinshi da kuma rasa yanda zaiyi, shi yasa nake ganin me zai hana ku tayar da gini a wajen tunda kunce filin yana cikin mutane ne akan titi, kunga kenan zai iya yin amfani."
"To ke yanzu me kike ganin ya kamata ayi a wajen idan an gineshi?"
"Zaku iya tayar da shago a wajen, ko dai ku dinga zuba kayan da kuke kawowa, ko kuma ku mayar dashi wata babbar super market in har kuna ganin aljihunku yana da nauyi zaku iya yi, amma fa wannan tunanina ne."
Wani kallo ya bita dashi ya jima yana kallonta, hakan yasa ta tsargu dan bata san me kallon yake nufi ba, fad'awa tayi jikinshi tana fad'in "kuyi hak'uri dan Allah idan na fad'i wani abu ba daidai ba, shawara ce kawai."
Rumgumeta yayi sosai a jikinshi yace "Ummi na kin had'u sosai gashi kin bani shawara akan abinda banyi tunaninshi ba, nagode sosai kuma insha Allah zanyi yanda kika ce."
Daga wannan lokaci Salman ya zama komai zaiyi ya kan shawarceta, idan shawarar ta masa ya d'auka, idan akasin hakane kuma zaiyi tunani akai, wasu lokuta ma idan ta baya shawara akan wani abu ya kan fad'awa Abbanshi ko Abban Ummi, amma sai ayi katari sun bashi shawarar data bashi, wannan ne ya k'ara karfafa masa gwiwa akan shawartar ta, gashi kuma duk abinda suka tattauna babu mai ji koda mahaifiyarta ce.
Bayan wani d'an lokaci ya gine filin kamar yanda tace, yayin da ya mayar dashi had'add'iya kuma matsakaiciyar mall, ya bawa Ummi zab'in sunan daza a saka a wajen, bud'ar bakinta cewa tayi "asa US super market."
Dariya yayi yace "US kuma kamar wata turai?"
Cikin salon yarinta tayi maganar "Eh mana, U yana nufin Ummi, S yana nufin Salman."
Sai lokacin ya fahimceta dan haka aka lak'abawa wajen US super market, _to dai zanje na siyowa fans d'ina chocolat acan
Salman bai gushe ba saida ya sake tambayarta yaran da za'a saka a wajen dan tsaro, shawarar da Ummi ta bashi baiyi tsammaninta ba, bai kuma tsinke da al'amarin ba har saida ya bincika ya samo matasa daga cikin 'yan uwa wanda ba suda abinyi ya d'orasu a wajen, irin farin ciki da godiya tare da sa albarkar da iyayensu suka dinga saka masa yaji dad'i sosai, hakan yasa ya k'ara girmama duk wani tunani na Ummi, yanzu haka duk wani lissafi da zaiyi a gida to tare sukeyi, wani lokaci da gangan yake yin kuskure a take Ummi zata fad'a masa ba haka bane.
_MATA SUNA DA ABIN MAMAKI, WALLAHI WATA SHAWARAR IDAN MACE TA BAKA ITA ZA KAYI MAMAKI, AMMA MAZANMU BASU SON SHAWARTARMU AKAN KOMAI SABODA SUNA MANA D'AUKAR MASU K'ARAMAR K'WAK'WALWA._
Hum.
Duk shekarun nan da aka d'auka ko sau d'aya Ummi bata tab'a koda b'atan wata ba, saboda yanda Salman ke kula da ita da kuma farin cikin da suke ciki yasa ko kad'an Ummi bata damu da rashin samun cikinta ba, da farko ta fara damuwa a duk lokacin da suka had'u wajen wata sabga ko r
union d'in gidan Alhaji idan suka had'u da sauran 'yan uwanta kuma abokan aurenta su Jawahir, to tabbas ta kanji babu dad'i tana ji ina ma itama ta samu nata, hakan yasa duk ranar da akayi wata sagba Salman yana fahimtar damuwa a tare da ita, daga wannan lokaci ya k'ara zage damtse wajen ganin ya sakata farin ciki, yanzu kam koda tana damuwa to ba kullum ba, dan harkokinta ma sun isheta suna kau da hankalinta daga duk wani abu da zai sata tunani marar kyau.
Duk da abin na cikin ranta amma bata yarda ta nuna damuwarta a fili ba, musamman a gaban Salman dan kowane lokaci suna tare, dan tunda ta kammala karatunta to ya daina tafiya shi kad'ai sai dai su tafi tare, dan ko lokacin tana makaranta ko hutu akayi to tare suke tafiya baya yarda ya barta saboda sabo da sukayi da junansu.
A wannan lokacin kuma Jawahir da Khairat suna da 'ya'ya bibbiyu da kuma tsohon ciki wato na uku, Hafsat tana da d'iya uku sai Nadiya dake da biyu, cikin hakane kuma mijin Khairat yaya Noura da mijin Jawahir yaya Khamis suka k'ara aure na biyu, mijin Hafsat ma haka wato yaya Shamsu yana nan yana shirin k'ara aure.
A lokacin auren ansha badak'ala sosai, amma dama duk abinda Allah ya hukunta babu wani mahaluki daya isa ya dakatar face Ubangiji, duk da dai Khamis ba zab'inshi bace domin kuwa Mamarshi ce ta zab'a mashi yarinyar d'iyar k'anwarta ce, hak'uri kawai Jawahir tayi tare da kau da kanta daga duk wani abu da zai sata bak'in ciki, lokacin kuma Khairat ta kasa hak'uri da b'oye kishinta har saida ta baro gidan mijinta tayi yaji, amma tana zuwa ta samu Salman a gidan hakan yasa ya fafarota da kanshi ya mayar da ita gidan mijinta tare da mata kashedi akan kar ta sake maimaita wannan kuskuren.
Lokacin hankalin Ummi ya tashi sosai saboda a tunaninta ai Salman da Khamis kullum suna tare, dan haka in dai har Khamis zai k'ara aure to Salman ma dole zai k'ara wataran, musamman ma ita da bata haihuwa, hakan da Salman ya fahimta ne yasa ya fara kwantar mata da hankali ta hanyar sake kusanci da ita, kuma hakan yayi amfani saboda ta shiga farin ciki sosai.
Daf da bikin Khamis Ummi da La Mama da Sa'ada da Islam suka tafi AGADEZ wajen bikin d'iyar aunty Fateema k'anwar La Mama, sun tafi da niyyar yin sati biyu dan suga 'yan uwa saboda jimawa da sukayi basu je ba, a ranar da suka je Inna ta kalli Ummi tace,
"Ummi kenan, gashi yanzu an girma hankali kuma yazo maki?"
Dariya tayi tace "Inna dama ai ina da hankali, girman daine ya k'ara zuwa yanzu."
Murmushi Inna tayi tace "humm, haka kika ce dai, ya mai gidan naki babu wata matsala dai ko?"
"A'a Inna babu matsalar komai, lafiya k'alau muke."
"Ai koda matsalar ma ba fad'a zakuyi ba daga ke har shi d'in, dan shima abinda yake fad'a kenan duk lokacin da mukayi waya."
Cikin mamaki Ummi tace "Inna dama suna kuranku?"
Hararanta tayi tace "kin d'auka shima mara kula ne kamar ke, ai duk safiya ta Allah saiya kirani ya gaishe ni."
Dariya Ummi tayi tace "to amma ai nima ina kiranki ko?"
"Eh, kina kira sati ko kwana biyar ba."
Dariya sukayi gaba d'ayansu, Inna kuma ta d'ora da "gaskiya yaron nan yana da kirki sosai, wallahi ko 'ya'yan dana haifa basa min abinda yake min, kinga duk wata saiya aiko min da kayan abinci da kuma kud'i, kuma abinda yake min dad'i kullum godiya yake min da nuna jin dad'in zama da jikanyata."
Murmushi Ummi tayi tace "to yanzu kin tabbatar muna zaune lafiya ko?"
"Eh mana, dama tsokanarki nake."
Haka akayi biki aka gama cikin farin ciki, yayin da a gida kuma ake bikin Khamis cikin rikici da tashin hankali, domin kuwa amaryar akwai rawar kai dan ko fad'a da akayi amaryar ce gaba, Ummi data samu labari ta waya ji tayi kamar tayi hira tazo wajen bikin.
Kwana d'aya da gama bikin nan Inna tace su tattara su koma in da suka fito, nan suka fara mata magiya da ban hak'uri akan ta barsu su kara koda kwana uku, amma ina tace sai dai su kuma su kula da mazajensu, jin haka yasa La Mama tace to su sutafi su barta ta k'ara kwanaki, bud'ar bakin Inna cewa tayi,
"Au, kenan ke zaki zauna su sutafi ko?"
"Eh, tunda su yara ne su tafi kawai, ni saina zauna daga baya naje."
"Ke hin ki kiyaye ni wallahi, ki tashi ku tattara kayanku gobe ku koma kinji na fad'a maki, in banda hauka waya fad'a maki ana tsufa da kula da miji da za kice wai su yarane."
Haka suka shirya suka dawo badan ransu ya so ba, a daren ranar kam Salman yayi farin ciki sosai, dan kwana hud'u da Ummi tayi bata nan ya jikkata sosai.
Tunda Salman ya d'aukosu daga gidan bus ya kawosu gida, yana aje Ummi kayanta kad'ai ya shigo mata dasu ya fita, ita kuma tana ganin haka ta shiga 'yan gyare gyare tana idawa ta fad'a toilet tayi wanka tana fitowa ta shirya cikin k'ananan kaya, riga mai sirara hannu sai wando jeans bak'i iya cinyoyinta, sakin kitsonta tayi k'anana ya bazu a bayanta mai kawai ta shafa da turare sannan ta fito falo, mamaki had'e da murmushi ne ya bayyana kan fuskarta har ta k'araso in da Salman ke zaune yana kallo.
Duk da ta jima a d'aki amma tayi mamakin ganinshi cikin wata sabuwar shiga, babban rigace da yar ciki da wandonsu sak dai ango, ga hula da agogo da takalmi komai fari sosai yayi kyau sai k'amshi da yake bugawa, tana zaunawa ya mik'e ya nufi cuisine yana fitowa ya fito hannunshi d'auke da plate mai fad'i, gabanta ya aje tare da kamo hannayenta ya zaunar da ita k'asa sannan ya zauna.