← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 49

Sashe 38

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Haka ma Salman farar shadda yasa dogon d'inki ne aka mashi kalar zaren da aka mashi kwalliyar dashi, kalar takalma da hular da agogon da yasa bak'ak'e, saida suka d'auki kansu photuna kafin suka fita suka bar gidan.

Ummi bakinta yak'i rufuwa saboda farin ciki, haka har suka kai gidan Alhaji gaba d'aya Ummi gani tayi unguwar ta sauya mata kamar ba in da ta tashi ba, Ummi na fitowa daga mota yara dake wasa k'ofar gidan kowa da fararen kayanshi suka tarbeta da murnarsu tsalle kawai suke wasu na fad'in "aunty Ummi, wasu na fad'in aunty, wasu na fad'in Ummi sak, wasu na fad'in tanti."
Masha Allah gidan ya cika tamk'am da 'yan uwa 'ya'ya jikoki da 'yayan jikokin, nan Ummi ta dinga kwasar gaisuwa ga manyanta dama na k'asa da ita, kowa dake wajen yayi mamaki da kuma farin cikin ganin Ummi da Salman a tare, ko ba'a tambaya ba kasan suna farin ciki dan dukansu jikinsu ya nuna hakan, fatarsu tayi fresh kamar k'wai ga k'iba da Ummi ta k'ara, hakan ba k'aramin dad'i yama mutanen dake wajen ba.

Mamar Nuseiba da Mama Hawa basu ji dad'in hakan ba, dan kuwa a tunaninsu shirin Ummi da Salman kamar barazana ne ga 'ya'yansu wajen hanasu shiga gidan Salman a matsayin mata, Ummi ma haka ta gaishe dasu sama sama ba kamar yanda tama kowa ba, dan a ganinta suna so su rabata da farin cikinta ne, su Jawahir murna har tayi masu yawa saboda ganin Ummi, saida ta gama gaisawa da kowa ta shiga babban falo nan ma ta jima sosai suna gaisawa da kakanin nasu suna tsakonarta ita da Salman wai sai yau ya barta ta fita har yasa ta kod'e fatarta ta fice tayi haske.

Alhaji kamar ya d'aukesu ya goya ganin yanda suka zama abin sha'awa, gashi alamu ya nuna suna zaune lafiya da junansu, Mamar Salman kam tunda ta zauna kusa da Ummi ta d'ora kanta a saman cinyarta tana ta shafar kanta fira kawai suke gashi ta hanata ta tashi suyi hira dasu Jawahir da suke fama da 'yan cikunnansu da basu wuce wata hud'u ba, duk da basu girma ba amma kallo d'aya zaka masu ka gane dan ya d'an turo rigunansu gaba.

Mama duk tunaninta shine Ummi ma ciki gareta shi yasa take ta nan-nan da ita kamar jaririya, haka Ummi ta kwanta saman k'afafun sarakuwar tata hira kawai ake sha cike da farin ciki wanda kuma dama wannan ne musababbin yin taron a kowane k'arshen wata.

Salman kam kallon mahaifiyar tashi kawai yake tare da matar tashi da suke hira abinsu kamar ba surukai ba, farin ciki da soyayyar Ummi na k'ara nunkuwa a cikin zuciyarshi tare da girmanta, ya kuma yarda Mama zata iya yi masa komai akan Ummi d'in.

La Mama ma kallonsu kawai take ita har kunya ma take ji, yayin da Mamar Nuseiba ranta ke k'ara b'acewa tana ganin Mama ma zata iya basu matsala akan burin nasu, haka aka dinga hira ana raha har sallah azahar sannan maza suka nufi masallaci mata kuma suka fara aika tasu sallah a cikin gida.

Ummi na kammala sallah a d'akin Hajia Zeinabou ta mik'e ta cire hijabinta zata fito falo, Hajiar ce ta kalleta cike da mamaki tace "takwara halan wasa kike da cin abinci?"
Cikin rashin fahimta Ummi tace "me kika gani Hajia?"
Ci gaba tayi da d'aura d'an kwalinta tace "naga 'yan uwanki kowace cikinta ya fito, amma banda ke, na sanki fa da tsinannen tamne tamne, kinga damar ki maida kayan mak'ulashe abincinki."
Gyara tsayuwarta tayi tace "to Hajia su ba ciki garesu dole cikinsu zai taso mana, ni kuma me na aje a cikin?"
Hajia tasan Ummi da barkwanci, dan haka tace "shikenan to."
Tab'e baki tayi ta bud'a labulen d'akin dan ta fito, tsaye tayi ganin Nuseiba da Rumana zaune cikin 'yan uwa ana hira, kallonsu take sosai dan kamar ta shak'e wuyan ko wacce a cikinsu take ji.

Salman ma idonshi na kan Ummi data fito babu hijab, ranshi ya b'ace duk da dai kusan kowa dake nan haka suke, amma ai ya kamata ace ita ta rufe jikinta ko dan yanda kayan suka ma jikinta d'araf, cikin sanyin jiki ta k'arasa fitowa ta zauna wajen da La Mama ke zaune tare da Mama suna hira yayin da Mama ke gyaran zogale saboda Ummi.

Nuseiba sarkin tsoro tuni cikinta ya d'uri ruwa dan tasan Ummi farin sani, tsaf zata cinyeta ko ruwa ba zata sha ba, tunda tayi k'asa da kanta bata sake d'agowa ba sai gabanta dake fad'uwa, har yanzu kuma tana nan akan bakanta akan son auren yaya Salman duk da dai tana ganin canji yanzu daga wajenshi, kusan wata biyu kenan baya kiranta babu text, idan ita ta masa baya maido mata to amma kuma duk da haka bata sare ba, gashi yanzu ma da suka zo gaisuwarsu kawai ya amsa bai sake ko kallonta ba bare kuma Rumana da dama ba ra'ayinta yake ba.

Ummi kam har yanzu bata daina kallonsu ba, juyawa tayi in da Salman d'in yake, karaf idonsu suka had'e dana juna dan dama kallonta yake, kunya ce ta rufeta dan ta d'auka za taga yana kallon d'aya daga cikinsu ne, k'asan da tayi da kanta tare da d'an murmushi yasa Mama ta kalleta tace,
"Ya dai Ummi na?"
Cike da shagwab'a ta girgiza kai tana fad'in "ba komai Mama."
D'ora kanta tayi a kafad'ar Mama, La Mama kam take ta jefeta da wata harara wanda tasa Ummi d'aga kanta daga kafad'ar Mama, duk a idon Mama hakan ta faru shi yasa Mama ta sake maida kan Ummi a cinyarta tace "kwanta ke rabu da ita kinji."
Kallon La Mama tayi tace "dan Allah Hawatan ki rabu da yarinyar nan, haba kamar ta tsare maki wani abu."
Hararan Ummi ta sake yi tana fad'in "kenan baki fahimci abinda nake nufi ba ko,ke marar kunyar ina ce, wannan ba sarakuwarki bace da zaki maida ita kamar abokiyar ki?"
Ummi na shirin d'aga kanta Mama ta sake kwantar da ita tace "bana san haka fa Hawatan, akan me zaki takura mata, ke ko tausayinta ma ba kya yi? kuma mu babu ruwanmu da wata surukanta ka ni a matsayin 'ya na d'auketa kuma ita ma uwa ta d'auke ni, dan haka ki shafa mana lafiya muyi harkar mu."
Duk abinda suke Salman na kallonsu dan haka ya taso ya zauna k'asa ya lank'washe k'afafunshi, Ummi ya kalla yace "ina kika baro hijabinki?"
Kafin tayi magana Mama ta bishi da harara tace "bata sani ba, dama dan ka mata wannan tambayar ne ka zo nan?"
Sosa k'eya yayi yace "a'a, naga dai baya jikinta ne shi yasa."
"Mu da babu a jikinmu me yasa baka tambayemu ba?"
Baiyi magana ba La Mama ta kalli Ummi tace "wai ba dake ake magana kina ji kinyi shiru, ki tashi ki d'auko hijabinki."
Tashi tayi tana shirin yunk'urawa, take siket d'inta tayi hakan yasa ta koma ta fad'i zaune, da sauri ta rik'e k'ugunta ba dan taji wani abu dan gane da hakan ba, da sauri Mama ta janyota ta rumgumata a jikinta tana kallon Salman tace "kai tashi ka bani waje dan Allah, daga zuwanka kana nema kaja mana matsala."
La Mama cewa tayi "dan Allah ki barshi, ina kike so ya tafi daya wuce wajen iyalenshi, ko yana da wanda suka fi mashi mune a duniya."
Da hannu Mama ta nuna shi tace "to ki fad'a masa kar ya sake shiga harkar 'yata."
Haka suka dinga sama da k'asa yaran na jinsu dan dama wannan ba sabon abu bane a wajensu, Mama na gama gyaran zogalen ta tashi Ummi tare dasu Hafsat da Nadia da Khairat suka ci Jawahir kuma tace bata ci.

Suna cikin cin zogalen su Sa'ada da sukayi girki suka fara rarrabawa kamar dai a gidan biki, Ummi kam bata ci ba saboda zogalen data ci ta isheta, Mama kam saida ta kalli Salman tace "yarinyar nan nasan bata damu da cin abinci ba, kuma kai da yake sakarai ne baka damu da lallab'ata ba har ta samu ta ci, kanka kawai ka sani shi yasa kake mulluk'a uwar k'iba kana barinta."
Kusan kowa dake d'akin saida ya dara, Hajia Abu ce tace "to ai zaifi idan kika mata fad'a da kanki watak'ila taji maganarki, dan nima na lura da hakan kamar bata san cin abinci."
Shagwab'e fuska Ummi tayi dan har yanzu bata fahimci in da zancen yayi ba, haka kam kowa dinga sa baki yana fad'in ta dinga cin abinci kar tayi wasa da lafiyarta, Salman ta kalla dake nesa da ita suna cin abinci tare dasu Khamis, ido ta masa alama akan ita fa bata fahimta ba, shi ma da hannu ya mata alama ta hanyar d'ora hannunshi a cikinshi sannan ya nunata da yatsa alamar ita, da sauri ta bud'a baki ta dafe k'irji tana fad'in "ni d'in?"
Kallonta kowa yayi dan maganarta ta fito fili, haka aka kammala cin abincin daga nan kuma Alhaji ya nemi da kowa ya bashi hankalinshi akwai muhimmiyar magana, kusan yan mata biyar dake wajen babu wacce gabanta bai fad'i ba, dan sun san sun isa aure kuma in dai har maganar aure ce Alhaji zaiyi to zaiyi wuya su tsallake, daga ciki har da Nuseiba da Rumana.
Chapter 38 · 0% Book details