Sashe 24
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read
Babu wanda ya k'ara magana a cikin su har su Mama da aunty Hawa suka shigo gidan cikin sallama, tarbansu su kayi saida suka zauna sannan samarin da suka zo da su suka fara shigowa da akwatinan lefen Ummi.
lefe kenen bayan tariyar amarya_
Akwati guda takwas haka aka shigo dasu kowace taf take da kaya na alfarma, Sa'adat ce tace "amma Mama ku kad'ai kuka zo? gashi nan ma babu kowa"
Dariya Mama tayi tace "a'a karki damu, Alhaji dama yace mu dake manya muzo kawai ba sai an tara jama'a."
Sai lokacin Ummi ta fahimci irin kallon da Mama Hawa take mata tare ma da kayan, sosai ta k'ara shiga hankalinta tare da cin burin kyautatawa yaya Salman sannan ya zama nata ita kad'ai.
Haka su Mama suka koma bayan tafiyar su Sa'adat ta duba kayan, matuk'a kayan sun birge sosai sunyi kyau, haka suka wuni gidan Ummi da Islam nata shirmen su sai yamma Sa'adat ta kammala girki da sauran gyaran gidan bayan takai akwatinan d'aki sannan ta shirya dan tafiya gida.
Tana saka hijab d'inta tace "to Ummi ni zan wuce sai kuma na sake dawo wa, dan Allah k'anwata kiyi tunani akan abinda na fad'a maki."
"Karki damu zanyi insha Allah" Ummi ta fad'a tana kallonta.
"Yawwa ko kefa, ni na wuce saida safe"
Kallon Islam tayi dake ta cakular kan Ummi wai tana mata kitso duk kitson dake kanta , cewa tayi "to autar La Mama sai anjima ko"
Saida ta turo baki gaba tace "ni dai ki gaishe min da d'iyana"
Dariya Ummi tayi tace "k'awar yau kenan kin yarda d'iyanki ne?"
Dariya su kayi gaba d'ayansu ita dai ta wuce abinta, su kuma suka ci gaba da harkokin su cikin nishad'i.
D'aki Ummi taje ta d'an gyara jikinta ta canja kaya hannu takai ta d'auki turarenta sai taga wayam, tayi mamaki amma saita bud'a jakarta ta d'auko wani irinshi ta shafa sannan ta fito falo ta zauna, Islam kam kallonta kawai take tana so tayi magana kuma ta kasa.
Wayar Ummi Islam ta d'auka ta sambad'a masu wak'a, nan fa suka fara casu ba kama hannun yaro, tun Ummi na rausaya daga zaune harta mik'e duk da k'afafunta amma haka ta dage suna rawa.
Salman kam daya shigo gidan tsaye yayi yana kallon ikon Allah, wai Ummi mai ciwo a k'afa amma gashi tana ta tik'ar rawa da k'afafun, ya shagala sosai wajen kallonta ganin yanda take biyar kid'in da kyau.
Yana lab'e yana kallonsu har aka kai k'arshen wak'ar *DACE* wajen wani baiti da ake fad'an,
_"Lokaci muke jira sai ka zo_"
_"In da rai rabon mu dole sai yazo_"
_"Babu kai kad'ai nake kira gwarzo_"
_"In da kake ba kira kawai nazo_"
_"Zuciya na saki, ba batun cire ki_"
_"Sa hannunka doki, banyi maka tsaki_"
_"Babu shi babu duka a tsarin soyayya_"
_"Na sani babu duka a tsarin soyayya_"
Take Salman yaji kamar dashi Ummi take, hannayenshi ya kalla duka biyu murmushi yayi tare da fad'in "wannan shine dalilin da yasa yanzu bana san dukanki"
Maida kallonshi yayi garesu har sun shiga wata wakar ita ma ta Umar m sharif mai taken *BABBAR RANA*
Kallonsu yake duk yanda tayi haka Islam keyi sai dariya suke suna farin ciki, kamar ba ita ke rawar ba saboda gwanancewa har aka kai wani baiti daya saka shi darawa,
_"Mu tuk'a mota mata tukunya_"
_"Mota ba taje ba in babu taya_"
_Gida babu gida in babu mata_"
_"Mutum babu mutum in baida mata_"
Dariya yayi tare da kutsa kai cikin d'akin, da sauri Ummi ta zube k'asa tana fad'in "wayo Mamana k'afata zata cire, wayo Allah na"
Murmushi kawai Salman keyi harya sunkuya wajenta ya rik'e k'afar yana kallon k'wayar idonta yace "to yaya da sauk'i yanzu?"
Kunya ce ta rufe Ummi dan haka tace "da sauk'i, sannu da zuwa"
Cike da mamaki yace "Ummi yau ni ake wa sannu da zuwa?"
Kallonshi tayi cike da jin kunya tace "kayi hak'uri, muje kaci abinci"
Tana fad'a ta mik'e ta nufi dinning ta fara zuba abinci, kamar wawa haka ya bita ya zauna yana kallonta cike da birgewa, Islam kam ba zata iya hak'ura ba dan haka ta kalli yaya Salman cikin rad'a tace,
"Yaya Salman wai aunty Ummi bata jin kunya ne?"
Kanshi ya sunkuyo wajenta tare da rufe baki yace "me yasa kika ce haka?"
Cikin rad'a tace "to ni naga duk ta zama wata 'yar iska, bata jin kunyar saka wannan kayan gabanka."
Bud'a baki yayi yana kallonta kafin yace "to ai ba komai bane, ni mijinta ne ke kuma k'anwar ta."
A tare suka kalli Ummi dake tahowa hannunta d'auke da ruwa da jus, d'an k'aramin siket d'inta sai wutsilniya yake, shi kam Salman yana jin dad'in ganinta a haka kamar su zauna haka har abada.
Salman na kai loma bakinshi yace "ashe haka kika iya rawa?"
Ko kai Ummi bata d'aga ba bare ta kalleshi, dan haka yace "waya dafa abincin nan?"
"Ni" ta bashi amsa tana kallonshi, shi kam cewa yayi "um um ba ke bace, saidai ko Sa'adat."
Jim Ummi tayi kafin tace "kasan ita tayi kuma kake tambaya?"
Ba tare daya kalleta ba yace "um um ba wai nasan ita tayi ba, saidai nasan d'and'anon abincin ki"
Kallonshi Ummi tayi tace "ashe kayi manqu
n (missing) abinci na?"
Kallonta yayi ita kuma tayi k'asa da kanta, suna kammalawa suka koma falo suna kallo, Islam da Salman na hira Ummi kam na jinsu har bacci ya d'auketa.
Islam ma bacci tayi saida Salman ya kallesu yace "dole kuyi bacci tun yanzu, tunda kun gaji."
Islam ya d'auka ya kaita d'akin Ummi ya dawo ya d'auki Ummi ya kaita d'akin shi, dan baya so ya bar wata k'ofa da zata falassa zaman da suke.
Yana direta akan gadon ta tashi a tsora ce tana fad'in "miye haka, ya zaka kawo ni nan bayan ga d'aki na can?"
Mik'ewa yayi ya nufi wadrob ya bud'a ya d'auko kayan bacci zai shiga toilet ya juyo yace "karki fita daga d'akin nan."
``` Salman kenan Ummin ce zaka bawa umarni haka```
05/03/2019
17:32 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*SADAUKARWA GA DUKKAN MASOYAN WANNAN LITTAFI, INA YINKU KUMA INA SONKU SOSAI*
_MY HEENAT TACE WAI MAI TAURIN KAI *SALMAN BA*NA UMMI* NI MA SUNA SANI DARIYA_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Ummi na ganin ya shiga toilet ta bishi da harara tana fad'in "kaji min mutum dan Allah kawai sai na kwana a d'akinka, na san meka shirya min."
Fita tayi daga d'akin ko rufe k'ofar ba tayi ba dan kar yaji fitarta ma, kai tsaye fridge ta nufa ta bud'a ta d'auki madara tasha ta mayar
ta d'auki ruwa ta kora dasu, zata rufe robar ruwan ta fad'i ruwan suka zuba, ajewa tayi ta nufi cuisine dan d'auko abinda zata goge a rashin tsammani ta taka ruwan da suka fallatsa in da ba tayi zato ba, sai ko sulb'i ya kwasheta tsaf ya ajeta k'asa ji kake timm.
K'ara tayi lokaci d'aya kuma ta kama bakinta tayi shiru, dafa fridge d'in tayi ta tashi tana kallon ruwan, Salman ne ya fito d'aure da towel a k'ugunshi gabanta ya fad'i saboda ganin ai niyin surarshi duk a mummurd'e, fizgota yayi da k'arfi bai tsaya da ita ko ina ba sai d'akinshi, wurgata yayi akan gado ya koma ya rufe d'akin da key ya kashe wutar d'akin.
FIRST NIGHT_
_MY HEENAT CE TA KWAB'E NI TACE "HABA MY MEERA ME YASA KIKA FIYA AZARB'AB'I NE WAI?
KI BARI MU GANI MANA"_
Ummi na ganin haka ta tashi da guda ta mak'ale a jikin bango ta manta da raunin dake jikinta, Salman kam kallonta yayi yace "nace karki fita daga d'akin nan amma sai gashi kin fita, na d'auka kwanan baya kince zaki dinga jin magana ta"
"Ni na rasa miye Alhaji ya gani a jikinki da har yayi tunanin kin isa aure, bayan ke kuma har yanzu ba kida hankali."
Jin bata amsa masa ba yasa ya d'auko kayan baccin shi daga toilet, ganin yana shirin zare towel d'in daga jikinshi yasa Ummi juyawa tana kallon bango ta d'aga masa hannu ta baya tana fad'in,
"Miye haka malam? dan Allah ka rufa min asiri kar kasa naga ciji ina zaman lafiya na."
Kallonta Salman yayi cikin takon izza ya k'araso wajenta tare da juyota da k'arfi ya had'ata da bango yana kallon fuskarta yace "miye kuma ciji?"
Sai lokacin ta d'aga idonta ta kalleshi sai dai yayi kusa da ita sosai, dan haka ta fara in ina " a...amm....amm...e...bbb ba komai"
Gaf da ita ya matso ya had'a hancinta da nashi numfashin su na gauraya dana juna tare sark'a hannunshi ta bayanta ya rike kunkuminta ya had'a k'ugunsu waje d'aya, hannayenshi yasa a jikin bango ya dafe gaba d'aya ya rufeta ko ganinta ba ayi.