Sashe 19
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Idonshi na kan k'afarta yace "mina fad'a maki a lokacin da mukayi waya?"
Gabanta taji ya fad'i, amma ganin ko kallonta baya yi yasa cikin tattausan murya tace "kace karna fita"
"Sai kuma nace mi a gaba?"
Murya na rawa tace "kace idan na fita zan rasa k'afa ko ido" har yanzu yak'i d'agowa ya kalleta yaci gaba da cewa,
"Sai ke kuma ki kayi mi?"
"Saina fita"
"Bayan kin fita kuma miya faru?"
"Nayi accident a hanya"
"Sai mi ya faru bayan had'arin ya faru?"
"Ciwo naji"
"A me kenan?"
Kamar zatayi kuka tace "a k'afafuna da kuma hannu"
"Me kika fahimta daga abinda ya faru?"
Cikin muryar kuka tace "na dinga jin maganarka, idan kace nayi to nayi, idan kace na bari na bari."
Jinjina kai yayi yace "da kuma mi?"
"Tasirin bakin miji akan matarsa"
"To yanzu idan na hanaki zaki hanu?"
Kai ta girgiza ta k'ara fashewa da kuka tana fad'in" kayi hak'uri yaya Salman wallahi ba zan sak
ba daga yau, duk abinda kace nayi zanyi"
Sai lokacin ya d'ago kai ya kalleta yace "kin tabbata?"
Saida ta sharb'i majina tace "wallahi zanyi na maka alk'awari, amma dan Allah karka fad'ama La mama"
Kafeta yayi da ido yace "kenan yanzu zaki dinga jin maganata idan na maki?"
"Wallahi zan ji yaya Salman"
Ajiyar zuciya ya sauk
yace "shi kenan na yafe maki tunda kince ba zaki sak
ba, nima kuma ki yafemin dan bai kamata na fad'a maki haka ba, kamata yayi na tsoratar dake ta wata hanyar daban ba wannan ba."
Kallon shi kawai take baki bud'e, karo na farko kenan a tarihin rayuwarsu da taji makamancin wad'annan kalaman daga bakin shi.
Yana gamawa ya bata magani tasha, amma ta dinga tsala kukan shagwab'a wai ita ba zata shaba, saboda tausayi yasa Salman rarrashin Ummi , amma fafur tak'i tasha sai baud'ewa take tana botsarewa, dole dai tasa ya koma Salman d'insa na ainihi, tsawa d'aya ya mata ta karb'a tasha jiki na rawa, dan Salman ba daga nan ba wajen tsare gida.
Tashi yayi ya maida robar cuisine ya aje ya dawo ya d'auketa ya kaita d'aki ya kwantar da ita yaja zanin rufa ya rufeta sannan yace "kiyi bacci" yana fad'a ya bar d'akin.
Ummi na bacci cikin farin ciki saiko tayi mafarkin mai adaidaitar nan da taga ganshi a fashe, girgigit ta tashi tare da fad'in "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, innalillahi wa'ina ilaihir raju'un, Hasbunallahu wani'imal wakil."
Dafe kanta tayi ta fara rera kuka, saboda abunne kawai ke dawo mata a kai yana mata yawo a k'wak'walwa, a hankali take rera kukan hannayenta biyu a kanta.
Salman dake tsaye yana nafilfili yaji tashinta dan haka ya shigo cikin azama dan yaga mike faruwa.
Zaune yayi kusanta yana fad'in "Ummi lafiya miya faru?"
Tana d'aga kai ta kalleshi kawai saita fad'a jikinshi ta k'ara fashewa da kuka, rigar shi kawai take ta cukuikuyewa tana k'ara tusa kanta cikin k'irjinshi tana fad'in "yaya Salman shi nake gani wallahi tsoro nake ji, zamu k'ara fad'uwa, dan Allah karka tafi duk jini ne a jikinshi ga kanshi ma ya fashe"
Shiru yayi yana tunani (dole ne abun ya tsaya mata a rai, dan yanda aka fad'a masa gawar mutumin dole ko namiji yaji abu bare kuma mace mai rauni), hannayenshi ya dora a bayanta yana cewa "shikenan to ya isa haka kinji, insha Allah bazai sak
dawowa ba, calme toi"
Haka yaci gaba da shafa bayanta har bacci ya d'auketa, a hankali ya maida kanta saman pillow yayi mata addu'a ya shafa mata, idonshi akan fuskarta, mik'ewa yayi ya shinfid'a sallayarta yaci gaba da sallarshi.
Har aka kira sallah asuba Ummi na bacci, Salman ne ya taso ya tayar da ita dan tayi sallah, saida ta tashi zaune tayi addu'ar tashi daga bacci sannan ta kalleshi.
"Malama ki tashi kiyi sallah" yana fad'a ya juya zai fita, yunk'urawa tayi ta tashi amma ina k'afafu sunyi tsami.
_Wayyo Ummi wallahi irin ciwon da naji nima kenan lokacin da na fad'i da moto, saida na zama gurguwa ta kwana uku_
Da sauri tace "yaya Salman dan Allah kaini toilet"
Dawowa yayi ya tsaya yana kallonta kafin yace "haka ake neman taimako cike da bada umarni?"
Turo baki tayi tare da zabga uwar harara ta kau da kai gefe tana wani jijjiga, k'ura mata ido yayi yana jiran yaji ko zata rarrasheshi amma shiru kake ji.
Ummi tunaninta shine ya zatayi ta rarrashi mutum, batasan yanda zatayi ba dan tunda take bata tab'a rarrashi ba idan tana son abu, ita dai idan taga abu tana so koba nata bane to kawai za tace ne abata, idan ba'a bata ba ta fashe da kuka su Hajia Alhaji maman Salman mahaifinta suna kewaye da ita su zasu goyi bayan abata ko sun san ita ce marar gskiyar wannan shine.
Jin fitsari na shirin kubce mata yasa ta sak
kallonshi tace "dan Allah haba ka kaini fitsari nake ji fa"
Kallonta kawai yake kamar gunki, kwab'e fuska tayi tace "ni dai inba zaka kaini ba wallahi zanyi shi a nan"
Baisan sanda dariya ta sub'uce masa ba, amma saiya dake yace "to kiyi mana gadonki ne fa ba nawa ba"
Hawaye ne suka fara taho mata tusa hannayenta tayi tsakankanin cinyoyinta tana ta matsewa wai karya fito, saiko taji fitsarin ya fara zubowa, fashewa tayi da kuka tana fad'in "dan Allah ka kaini wallahi zai taho"
Cak ya d'auketa yayi toilet da ita ya aje tsaye, ina yana ajeta fitsarin ya ida tahowa, Salman kam mutuwar tsaye yayi yana kallonta kafin ya fara shek'a dariya har yana rik'e ciki.
Ummi kam ko a jikinta dan inta nuna masa taji kunya to ta shiga uku kenan zai dinga tsokanarta kullum, cikin shagwab'a tace "ni dan Allah ka fita to na gyara jikina"
Da k'yar ya dakata daga dariyar ya nunata da hannu yace "ke yanzu ko kunya bakya ji kamar wata k'aramar yarinya fitsari daga tsaye"
Turo baki tayi tace "to miye a ciki ai laifinka ne, kuma ma da kake cewa bana jin kunya, kunyarka zanji? kaifa yayana ne kuma mijina to miye a ciki dan nayi fitsari gabanka."
Kallon rigarshi yayi yace "dubi kinsa na d'auka ke kin b'atamin riga, yanzu dole saina canja wata." juyawa yayi ya fita yana dariya.
Yana sauyawa ya nufi masallaci zuciyarshi cike da farin ciki, haka kawai yake jin nishad'i, tabbas Ummi ta birgeshi yau data nuna ba wani abu bane dan tayi fitsari daga tsaye kuma a gabanshi, dariya ya sak
b'allewa da ita harya isa masallacin.
Ta kasa tsaye da kyau dole ta zauna k'asa tunda dai dama kayanta sun riga sun b'ace, gashi hannu na ciwo ta kasa cire su dole ta zauna zaman jiran Salman, tare da tunanin cire kunya ta rok'eshi ya cire mata kayan, sannan ya mata wanka.
```Irkwai beri```
Yana dawowa ya shigo d'akin ya sameta zaune a toilet, tambayarta yayi "miye haka ke kuma, kina zaune har naje na dawo ba kiyi komai ba?"
Turo baki tayi tace "to ni dan Allah ka ciremin bazan iya ba" ido ya fiddo waje yace "ke d'an aikinki kika mayar dani ko me?"
Langab'e kai tayi tana shirin kuka tace "dan Allah ka ciremin" hararanta yayi yace "ke in zaki tashi kiyi abinda ya dace ki tashi, in kuma ba zaki yiba to ki zauna nan har sarkin zama ya sameki."
Juyawa yayi zai fita Ummi tace "dan Allah yaya Salman, *AGU TIZEDAT*(kayi hak'uri) *WURTU ZILISA*(ba zan sak
ba)."
Juyowa yayi yace "iyee, d'iyar Mama kenan wato harda buzanci yau, kin tuna yaren mahaifiya kenan, amma karki manta ni ban iya buzanci ba dama fulatanci ne to da sauk'i ina ji kad'an kad'an"
Yanda tayi kalar tausayi yasa ya shigo toilet d'in ya kama hannunta ya mik'ar da ita tsaye, kallon juna sukayi Ummi kam kawar da kai tayi gefe , zuciyar ta na k'ara tsananta bugawa.
Bayanta ya koma a hankali ya fara zuge zif d'in rigarta, da k'yar ya had'iye wasu yawu da suka tarar masa k'irjinsa kamar zai fito, take hannayensa suka fara kakkarwa kamar mazari, Ummi najin ya sab'ile mata rigar ta zube k'asa ya rage daga ita sai bras da pants, da sauri ta juya tana fuskantarshi amma kanta na kallon k'asa rufe jikinta tayi tace.
"Ya isa haka nagode" kamar jira yake dama saiko fit ya fice daga d'akin gaba d'aya, yana shiga d'akin shi ya fad'a saman gado ruf da ciki idonshi rufe yana sauke numfashi a hankali, tashi yayi ya bud'e drower ya d'auki maganinshi guda d'aya yasha sannan ya shiga wanka.
Ummi kam da k'yar ta samu ta wanke jikinta duk inda ya b'ace, sannan ta fito ta d'auki wata doguwar riga tasa ta zauna tayi sallah, tana idawa bata tashi ba saima tunani data shiga yi.
"Na d'auka kamar yanda nayi fitsari gabanshi ba tare da na ji nauyi ba, na zata haka zan iya jarumtar fiskantarshi ya ciremin kayana sannan yamin wanka ya sak
min kaya, ashe ba haka abin yake ba, yana da wuya ka iya jarumtar tsayawa wani ya kalli tsiraicinka ba tare da baka ji wani abu ba."
Ganin safiya tayi yasa ta tashi da k'yar ta dinga d'ogala k'afafu haka ta kai kanta falo amma fa anci wuya.
_ALLAH YA BADA LAFIYA_
05/03/2019
17:31 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Salman ne ya fito cikin k'ananan kaya farar riga mai dogayen hannu sai bak'in wando, yayi kyau sosai tsaf Ummi ta k'are masa kallo cike da birgewa.