Sashe 10
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 6 min read
Jikinshi ne duk yayi sanyi da yaji tace akwai Allah, Allah kuma ba azzalumin bayinsa ba ne dole zai mata sakayya, aje ball d'in yayi ya koma ciki saida yayi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya wanda suka karb'e shi matuk'a sun masa kyau ga k'amshin turarenshi mai sanyaya zuciya, haka ya shigo d'akin Ummi ya sameta tana ta kuka a tsakiyar gado, sai ya ji baiji dad'in hakan ba tausayi ta bashi sosai ( k'aro na farko kenan a rayuwar Salman da ya ji tausayin Ummi har cikin zuciyar shi) zaune yayi cikin muryar rarrashi yace" Ummi dan Allah kiyi ha'kuri ki yafemin, wallahi banyi nufin ta sameki ba" d'ago da fuskar tayi yanzu kam gaba d'aya fuskar ta d'an kumbura ido sun ida yin ja saboda kuka, kau da kanshi yayi kai lokaci d'aya kuma ya kalleta yace" kin yafemin Ummi?" bata tanka saba haka yaci gaba da rarrashinta har saida yace" dan Allah Ummi ki yafemin, wallahi ba zan iya kwana d
alhakinki a kaina ba Ummi kin had'ani da Allah kinsan kuma dole zai maki sakayya, kiwa Allah ki yafemin kinji, in kuma ba zaki iya ba to ki fad'i abinda kike so nayi sannan ki yafemin?" sai lokacin kad'ai tayi magana tace
"In dai kana so na yafemaka to saidai in ka yarda zaka mayar da ni gidan mu" kallonta yayi yace" kema kinsan hakan ba zai yiwuba, idan na kaiki gida ko da da wuni d'aya ne to nima zan shiga cikin bak'in jadawalin Alhaji, ni kuma yanzu ban shirya rabuwa da kowa nawa ba." kuka ta k'ara fashewa da shi tana fad'in" wallahi ni sai na tafi gidan mu ba zan iya zama da kai a gidan nan ba ka kashe ni, ka duba kaga yanda na koma kamar wata jaka kun same ni sai duka kuke, ta yaya zan iya zama da Kai a gidan nan ni dama ba kyau ba jar fatar ce kawai gashi kuma yanzu kun mayar da fatar ta koma kala biyu ja da bak'i, dan mugunta kuma yanzu fuskar tawa kake hari ka nakasata" mik'ewa yayi yace" kiyi ha'kuri idan za kiyi, idan kuma ba zaki yafe ba to ruwanki ne kuma." fita yayi ya zuba abinci yaci ya fita ya bar gidan.
Ganin fuskar tayi sauki yasa tayi girkin rana, bayan ya dawo yaga babu kumburi sai dai har yanzu akwai ja a idon, dan haka yayi tunanin siyo mata magani idan ya fita, abinci yaci yayi wanka zai fita Ummi tayi saurin tare gabanshi ta durkusa tace" dan Allah yaya Salman ka taimaka min ka bani waya ta ina so in kira la mamma da Abba" cikin dakewa yace" ki fidda rai da wannan wayar, dan b
zan baki ba ki dinga taramin maza cikin gida ba" kallonshi tayi tace" Salman me kake nufi?zargi na kake?" kunnanta ya kama ya murd'e har saida ta saki k'ara yace" kar na sak
jin bakinki ya kira sunana daga yau, ko dai kice yallab'ai ko kuma ranka shi d'ad'e" sabo yasa Ummi murgud'a baki tace" to sannu, kaji mun mutum wai ranka shi d'ad'e kamar wani sarki" kwaf ya buge bakinta yace" to naji bakinki ya kira ni da sunana kiga yanda zanyi da ke a gidan nan" wucewa yayi ya barta nan.
Da wuri Salman ya shigo saboda hadarin da ya taso, Sa
da yayi wanka ya fito ya zauna Ummi ta zuba mashi abinci, cewa yayi ta zauna tare suka ci abinci sannan ya bata magani sa
da yayi kamar ya bibbigeta sannan tasha.
23:59 Ummi ta kawo ma Salman Tea, ya ji dad'in ganin tsoronshi a idonta sannan tayi abinda ya sata, tana zuba mashi ta zauna k'asa ta jingina da gado, kallonta yayi yace" miye haka kuma?" kamar za tayi kuka tace" dan Allah kayi hak'uri karka koreni, wallahi tsoro nake ji a can, amma idan aka d'auke ruwa zan koma" Tea d'in shi yaci gaba da sha ya shareta har bacci ya d'auketa.
Bugun da taji a k'afa yasa ta bud'a ido tana kallon Salman da yasa jallabiya da sallaya a hannunshi yana 'ko'karin shinfid'awa, tashi tayi ta koma d'akinta duk jikinta ciwo saboda ta kwana daga zaune, sallah tayi tana idawa ta shigo d'akinshi da sallama, durk'usawa tayi ta gaishe shi ya amsa yau ma kamar jiya Al-Qur'ani ya bata ta d'ora a inda ta tsaya, ta jima sannan ya karb'a ta tashi ta nufi cuisine a kasalance dan aikin ya fara gundurarta tunda ko a gida bata makamancin aikin da ta keyi anan ko kad'an sai hutu.
Da k'yar ta samu ta had'a frite da omelette da Tea da yar matsakaiciyar sauce d'in albasa da petit poids ta aje mashi, wanka ta shiga ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa mai da turare kawai ta shafa ta fito falo ta zauna.
Tana ganin ya fito ta tashi cikin ladabi ta sunkuya tace" ina kwana" sama da k'asa ya kalleta ganin fuskarta tayi sauki yasa ya wuce b
tare da ya amsa, bin bayanshi tayi da harara, ganin ya nufi hanyar fita tace" yaya Salman abin karyawar fa?" juyowa yayi ya kalleta yace" kin manta ko wace rana ce yau? ni ba kamar ki bane mai bawa ciki wahala" shiru ta dan yi ta tuna yau alhamis yana azumi, amma kuma ba taga yayi sahur ba, mik'ewa tayi ta tari gabanshi ta tsaya tace" yaya Salman, dan Allah" katseta yayi da fad'in" me na fad'a maki jiya akan kiran sunana?" rufe baki tayi sannan tace" kayi ha'kuri, dama ina so ne ka kiramin la mamma ina so nayi magana da ita" mtssss, dogon tsaki yayi ya zauna saman kujera ya fiddo waya, dad'i ne ya kama Ummi dan tasan zai kira mata mahaifiyarta ne.
Mik'a mata wayar yayi ta d'ora a kunne, tana jin an d'auka ta mik'e dan ta bar wajen da hannu ya mata alama da ta koma ta zauna, jiki a sanyaye ta zauna tana fad'in" wa'alaiki salam, la mamma ni ce, ina kwana" a dak'ile la mamma ta amsa da" lafiya lau" cikin farin ciki Ummi tace" la mamma ina Abba da su Islam duk Suna lafiya?" lafiya lau suke" jikin Ummi ne ya danyi sanhi jin amsar da Mahaifiyarta take bata hakan yasa tace" la mamma ko dai fushi kike da ni?dan Allah kuyi ha'kuri wallahi la mamma ba nida laifi, kawai Alhaji yayi kuskuren fahimta ne amma ban aikata komai ba" hawaye ne suka fara biyo fuskarta Salman ko sai wani b'ata rai yake yana hararanta, la mamma ce tace" kinga ni yanzu banda lokacin wannan maganar, koma miye ai aikin gama ya riga da ya gama tunda kin ja mamu fad'a, ta kai har gaisuwar mu yanzu Alhaji baya amsawa ni da Mahaifinki, kuma kinga ke ma kinci riba tunda yanzu haka ya kafa ma kowa doka akan kar wanda ya kuskura yaje gidanki ko da cikin yara ne, kuma ke ma yace kar mijinki ya yarda ya kawoki cikin iyalenshi dan baya buk'atar ki yanzu." tana gama fad'a ta kashe wayar saboda kukan daya taho mata, tana kashe wayar Ummi ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Salman karb'ar wayar shi yayi ya fice ya bar mata gidan shi kam ko a jikinshi.