← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 6 min read

Wani hamshak'in murmushi yayi mata tare da fad'in "wannan kyau haka, kinga yanda kika had'u, ai da farko ban ganeki ba na d'auka wata sabuwar amaryarce Alhaji ya auramin ban sani ba."
Wata yar k"aramar dariya tayi hakan yasa ya lotsa hannunshi a dinple d'inta, cewa tayi "ai ko a mafarki idan kaga wata mace ta shigo d'akin nan, to ka tabbata ZEINAB ce, wato Umminka."
Janyota yayi jikinshi ya rumgumeta suna kallon juna yace "tabbas wannan haka yake, ke kad'ai ce keda ni kuma zan ci gaba da zama naki da yardar Allah, kamar yanda zan ci gaba da yiwa Alhaji addu'a da wannan *AUREN HA'DIN* da yayi mana."
Murmushi tayi tace "gaskiya kam, nima zan ci gaba dayi masa addu'a har k'arshen rayuwata."
Remonte d'in hannunshi ya juya ya kashe tv sannan yaja musu blanket suka shige ciki yana tambayarta " kin yiwa yarana addu'ar bacci?"
Gira ta d'aga masa tare da cewa "na masu mana."
Sumbatarta yayi yace "kin kyauta my zuma."
Dariya tayi tace "gishirina kenan ba kada dama."
D'ago da kansa yayi daya tutsashi tsakiyar mamanta yana lasa yace "gishiri kuma, yau haka na samu? nan gaba kuma bansan me zaki cemin ba."
Dariya tayi tace "to ai kune kuka cemin zuma."
Saida ya had'a goshinshi da nata hancinshi da nata hancin sannan yace "to ai zumar ce ko? nifa dama ina so in fad'a maki wani abu."
"Ina jinku."
"Tunda nake tare dake kullum gamsuwa da farin ciki ne kike cika zuciyata dashi, da wannan nake cewa dan Allah ki rage amfani da abinda kike amfani dashi wanda kullum kike rikita min lissafi dashi, wallahi ina tsoron wata rana dad'i yamin yawa na mutu, wallahi sai dai kiji ni shiru babu numfashi."
Wata shu'umar dariya tayi tace "wasa kuke dani, kuna nufin kenan na daina gamsar daku ta yanda zaku samu damar d'auko min wata a matsayin k'anwa ko?"
Cikin dakusashiyar murya yace "wallahi da gaske nake fad'a maki, dad'in ya fara min yawa dan har yanzu banji wani d'and'anon abu a duniyar nan ba daya kai min ke d'and'ano mai dad'i."
Tana shafar bayanshi tace "to ku rok"i Allah yasa ya rage, amma bani ba."
_Ni kam dake tsaye ina kallon ikon Allah, tab'e baki nayi nace "kaji wani kicihi kuma wai wani zak'i da galmi, to ko me hakan yake nufi?"
Da sauri Salman ya yaye blanket d'in yana kallona da mamaki, Ummi ce tayi dariya tace "aunty Sam bafa gishiri da zak'i muka ce ba, zuma ne da gishiri."
Cewa nayi "ayyah, yanzu na gane, to kenan me sunan yake nufi?"
Cikin tsawa Salman yace "keh, waike wace irin 'yar sa ido ce?dallah malama b'ace min da gani."
Ummi ce tace "haba sweet cocomber, wannan fa aunty Sam ce, ko baka ganeta ba?"
Kallonta yayi yace "ke dallah wace aunty Sam, ke ba kiga hark'allar da nake bane?"
Kallona Ummi tayi tace "auntyna kiyi hak'uri dan Allah ki jiramu a waje ina zuwa yanzu."
Hararan Salman nayi nace "su hark'alla manya, sai kace wanda yake filin daga yana fama da arna irinsu ABU JAHAL, ABU SUFYAN, DA MUSAILAMATUL KAZZAB."
Ban an kara ba naji Salman ya jefomin pillow yana k'ok'arin tasowa daga kan Ummi yana fad'in "ke, zan ci gidanku wallahi, kinsan irin arnan da nake kashewa anan d'in?sunfi FIR'AUNA kafirci."
Da gudu na bar d'akin, har na fita kuma na tuna da sak'on MY HEENAT hakan yasa dole na kuma bud'e k'ofar d'akin a hankali na lek'o kaina ina fad'in "dan Allah yaya Salman minti biyu?"
Cike da k'osawa Salman ya kalleni yace "oh my gosh, na rasa yanda zanyi da yarinyar nan, to miye kuma yanzun?"
Saida na tattare siket d'ina sannan na fara masa bayani cikin sauri "dama my heenat ce tace wai na fad'a maka akwai k'annenta, idan kana son d'aya daga ciki zaka iya yin magana saita had'aka da d'aya daga cikinsu."
Remonte d'in dake aje gefe naga ya d'auka tun kafin ya jefo min na bar d'akin @360, gudu nayi sosai har saida na bar unguwar na tsaya ina sauke numfashi cikin zuciyata kuma ina fad'in "my heenat da nasan haka sak'onki zai zama, da ban fad'i ba."
Sai lokacin na lura ban d'auko takalmana ba, amma dai nace ma ch
rie da Maman dady suzo su d"auko min, danni da gidan Salman sai kuma haihuwa ta biyu idan Ummi tayi.

Ashe ina fitowa Ummi ta kalli Salman tace "haba babban mutum, aunty Sam d'in kama haka, kasan itama fa tana da masoya wallahi zamu ji ba dad'i fa idan ta fad'a masu."
Cikin wani yanayi yace "gobe zanje na bata hak'uri, shikenan hakan ya maki?"
"Idan ma baku jeba ni zanje na bata hak'uri."
Hancinta ya kama yace "amma bada izini na zaki jeba."
Hararanshi tayi sama da k'asa cikin dariya tace "to waya fad'a maku dama ina neman izininku idan ina san fita."
Dariya yayi dan ya fahimci ta tuna dah ne, a lokacin da ta nemi izinin fita ya hanata har tayi hatsari, cewa yayi "in ko ki kaje to zaki rasa ido ko k'afa."
Cikin dariya tace "idan ma na rasa ai kune za kuyi jinyata."
Kafad'a ya d'aga yace "um um, ba zanyi ba wannan karin, za kiji da kanki ne"
Dariya tayi tace "dole zakuyi kodan gudun kar na maku fitsari akan kago."
Fashewa yayi da dariya yace "ai a gadonki zakiyi jinyar ba a nawa ba."
Cikin kunne ta rad'a masa "amma ai kunfi jin dad'in bacci akan gadona."
Kallonta yayi yace "kuma fa hakane yarinyata."
Hararan wasa ta masa tace "wacece yarinyar?"
Hannu ya d'aga mata yace "afuwan, to 'yan matana."
Duka ta kai mashi a k'irji lokaci d'aya kuma ta rumgumeshi tare da fad'in "shashasha na kenan, ina sonku sosai."
Shima rumgumeta yayi yace "nima ina sonki sosai rabin raina."
Haka suka lula duniyarsu mai wuyar fassarawa da kuma dad'i da annashuwa a wajensu.
*ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH, ALHAMDULILLAH KASIRAN.*
_ALLAH NA GODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA WANNAN NOVEL LAFIYA KAMAR YANDA NA FARASHI LAFIYA, 'YAN UWA KUMA MASOYANA INA SONKU INA ALFAHARI DAKU._
*BANDA NOVEL D'IN DAYA FI _KAUSSAR_ AMMA KUMA _AUREN HA'DI_ MA YA ZAMA ZAKARAN GWAJIN DAFI, DAN DAGA IRIN MASOYAN DAYA SAMU NASAN CEWA SAK'ON DA NAKE SAN ISARWA YAJE IN DA NAKE SO YAJE.*
```AUREN HA'DI BAWAI NAYI SHI BANE KAWAI DAN NISHAD'I KO SAK'ON SOYAYYA, DUK IN DA AKACE AUREN HA'DI, TO CIKIN BIYU DOLE D'AYA ZAI FARU,```
_1-IN MA ZUMUNCI YA D'ORE KO KUMA YA WARGAJE,_
_2-TSAYAWA TSAYIN DAKA AKAN KOWACE UWA AKAN 'YA"YANTA, MUSAMMAN MATA DOMIN GIDAN AURE ZASU JE, KAMAR DAI YANDA LA MAMA TAYI._
_3-SANIN GIRMAN MIJI DOLE AKAN KOWACE MACE MAI NEMAN ALJANNA._
_4-SOYAYYA KAN IYA SA MACE TA MANCE DA KOMAI, KAMAR DAI YANDA UMMI TAYI DUK DA BATA SAMU HAIHUWA DA WURI BA, DAMA MU MATA 'YAN SOYAYYA NE HAKA ALLAH YA HALLINCE MU._
_5-GIRMAMA MIJI TA HANYAR YI MASA BIYAYYA DA LADABI DA KUMA JIN MAGANARSA._
_WANNAN SUNE GINSHIK'IN DA YASA NA SAKE RUBUTA WANNAN NOVEL, SANNAN 'YAN UWA BANCE MAKU HAR ABADA BA, AMMA DAI BANA TUNANIN SAKE RUBUTU MUSAMMAM MA NAN KUSA, AMMA WATAK'ILA KU JIMU A CI GABAN *AURENMU A YAU* WANDA MUKE NI DA 'YAN HANUNA._
*ALLAH KA YAFE MIN KURA KURAINA DAKE CIKIN WANNAN RUBUTU, A IN DA NAYI DAIDAI KUMA KA BANI LADAR TARE DA LADAR FAD'AKARWA, DUK WANDA YA KARANTA KUMA YA K'ARU ALLAH KAYI MASA ALBARKA, ALLAH KA SHIRYA MIN YARANA KA K'ARA MAMU DANK'ON SOYAYYA DA MIJINA D'AYA TAMKAR DA DUBU, INA ALFAHARI DAKU, DOMIN KUNA BANI 'YANCINA A MATSAYINA NA MACE, KUNATAUSAYA MIN A MATSAYINA NA MAI RAUNI, KUNA WASA DANI DA HIRA DANI A MATSAYINA NA ABOKIYAR ZAMANKU.

LUV YOU MON ANGE
*SEE YOU GUY'S*
_SAMEERA CE_
> @ B
@ B
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
9edfc26388d845889eaf93002737b6aa
Chapter 49 · 0% Book details