← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 49

Sashe 7

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read

Sallama tayi suka amsa Mubarak ne ya bata izinin shiga, saida ta shiga tayi da na sanin shiga saboda yawan su su da abokansu ne sunfi su goma sai shiri ake, Mubarak kawai ta kalla tace" yaya Mubarak chargeur kina nazo karb'a" cikin sakin fuska yace" OK na kine dama? bari in d'auko maki" tsaye tayi tana jira Khamis ne yace" k'anwata gaskiya kinyi kyau sosai, ina ma hada ke zamu angwance, gashi sai k'yalli kike kema kamar amarya" murmuchi tayi in da Salman ya bita da wani kallo dan yasan dama saita murmusa shi kuma yana so yaga dinple kinta, wani daga cikin abokanne yace" abokina da in dai baku mata miji ba to ni kam ina so" kai na rabaka, kai b
kasan auren dangin mu ba?" to miye a ciki in haka ne ai sai na komo cikin dangin naku" dariya suka saka, Salman kam cewa yayi" lalle kam da kayi asara ka dawo danginmu saboda wannan abar" kallon mamaki suka mashi d'aya yace" to saboda me, wannan zuk'ek'iyar budurwar, ko ni in har za'a bani ita ai da gudu zan dawo" hararanshi Salman yayi yace" ka koji haushi wallahi ba kayi zab'en k'warai ba" Khamis ne yace" ku fa baku fahimce shi ba yana so ya nuna maku ita d'in matar da zai aura ce, amma kunk'i ganewa" da dariya ya k'arashe maganar, Salman kam kamar ya kai mashi duka, kafin yayi magana Ummi ta murgud'a baki tace" haba yaya Khamis kamar dai maza sun k'are a garin da zan auri wannan halintar" wani bakin ciki ne ya taso ma Salman da yaji an kwashe da dariya, kallanta yayi yace" ke bar nan wajen" tana karb'ar chargeur kin ta wuce saida ta kai k'ofar d'aki ta juyo tace" to kama bakin ni ka daina kallona" wannan maganar ba k'aramin b'ata masa ray tayi ba,( *to fa shine yan uwa ku kaga Salman ya biyo ta a guje har kuma suka zama miji da mata* ).
```CiGaban Labari```
Su Khamis na tafiya Salman ya shiga d'akin Ummi dan ya san da gangan ta zuba masa abinci a jiki, tsaye ya same ta tana gyaran shinfid'a ko riga babu a jikinta sai bras da ta kamata sosai abunka ga mai yar k'iba hakan yasa duk bayanta ya kakkarya gata jawur sai shatin bulaliyar da ta sha sai dogon wando a jikinta shi ma bak'i kamar bras kin, shiru yayi ya ma rasa abinda ya zo fad'a Ummi kam ba tayi wani k'ok'arin rufe jikinta ba duk da ta ganshi.

Hannunta rik'e da pillow ta kalleshi tace" malam ya dai lafiya ka shigo min wannan lokacin haka?" da sauri ya d'auke kanshi daga kallanta bai ce k'ala ba dan haka tace" ka shigo d'aki babu sallama, ba tap
ba excuse kawai ka shigo, yanzu idan nayi ihu nace za kamin fyade kana ganin zaka fita?" ci gaba tayi da abinda take, ganin ba yada abin fad'a yasa ya juya ya fita, d'akinshi ya shiga ya kwanta saman gado yana kallon sama a hankali yake rufe idonshi yana bud'ewa wani sabon abu yake ji a tare da shi, surarta ce take dawo mashi a k'wak'walwar shi a haka bacci yayi gaba da shi duk da yaso ya fita.
27/02/2019
17:34 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*Page*
Misalin 23:30 ya farka, wanka ya farayi ya fito ya kalli agogo tsaki yayi yana fad'in" mi yarinyar nan take nufi da ni ne da har yanzu bata kawo min Tea na ba?"wani tsakin ya k'ara saki ya fito ya nufo k'ofarta, zai bud'e wata zuciyar ta gargad'eshi karya sak
ganinta a yanda ya ganta d'azun, ya dan jima a tsaye kafin ya zira kai cikin d'akin, ga dukkan alama tayi nisa a cikin baccin ta har yanzu babu riga a jikinta tayi rub da ciki, sai lokacin ya kalli shatikan carbin da ke bayanta duk ya farfashe, ga kananan kitsonta daya kwanta a bayanta kamar ya taba wata zuciyar ta gargad'e shi, k'afarta ya kama ya fizgo a tsorace ta mik'e zaune tana murza ido tare da kallonshi kafin tace" wai dan Allah miye haka, haka ake tada mutum daga bacci kamar a gidan mahaukata, kai idan aka maka haka sa kaji dad'i?" ke rufe min baki ina abinda na saki?" kallaonshi tayi ido bud'e tace" wane abu kuma?" dan 'kuwa ya mata yace" ban sani ba, Tea k'in fa, ko ni kike so naje na dafa?" kau da kai tayi tace" nifa ba zan'iya ba, ace Tea ba za'a shashi da safe ko da rana ba sai dare yayi kuma sai na kai har cikin d'aki haba gaskiya da sak
" ganin ya fara waige waige yana neman abun bugu yasa ta tashi da gudu ta bar d'akin ta shiga cuisine ta fara had'awa.

Tana kammalawa ta kawo mashi har d'akinshi, kallo d'aya ya mata yaga bacci pal a idonta dan haka ya mata tsaki yace" ba kida aiki sai bacci kamar kasa" lumshe ido tayi ta sak
mik'ama mashi faranti tace" ni ka karb'a dan Allah in tafiya ta" wata harara ya watsa mata yace" ki aza a kaina mana tunda ba babu wurin ajewa" gefen gadon ta d'ora harta juya zata fita yace" waye zai zuba kenan?" dawowa tayi ta zuba mashi kallonshi tayi cikin muryar bacci tace" sugar nawa zan saka a ciki?" d'aya" ya bata amsa idonshi na kallon hannayenta da suka sha jan lalle da bak'i abin sha'awa,tana gamawa ta mik'a mashi wani kallo ya mata yace" ki aje ko dole sai na karb'a" ajewa tayi ta juya cikin magagin bacci ta fita, har saida ta bace ma ganinshi sannan ya kalli faranti yanda ta k'awatashi ma kad'ai da abin birgewa ne ga kamshin da ke tashi mai dad'i, d'auka yayi ya kurb'a har saida ya lumshe ido dan Khairat bata taba dafa mashi mai dad'in wannan ba kuma gashi duk abinda ake sakawa a waccen nan ma an saka "to miye banbanci?" ya tanbayi kanshi.

Yau ma da zazzab'i ta tashi tana yin sallah asuba ta nufi cuisine dan ta tuna abinda ya fad'a mata akan girkin, gashi kuma ta d'ora mai wuya abincin da Abbanta yafi sone ya karya dashi ta d'ora tuwon shinkafa da miyar agushi, duk da ta d'ora da wuri saida tayi late akan lokacin da ya bata sakamakon zazzab'in daya addabeta ga kuka da tasha abunta ta k'oshi.

Tana fitowa zata aje kwanukan ta ganshi zaune ya hakimce rai a b'ace saida ta gama jera duka kayan ta zuba mashi zata wuce d'aki yace" zonan" dawowa tayi ta tsaya sannan yace" k'arfe nawa yanzu?" da k'yar ta gane lokacin dan jiri kawai take gani, a hankali tace" 08:22" bien" ya fad'a yana kallonta yace" nawa mu kayi da ke na dinga samun abinci a nan" kamar za tayi kuka tace" dan Allah kayi hakuri banji dad'i ne shiyasa, kuma kaga tuwo ne nayi" cikin tsawa yace" to sai me, ina ruwana da abinda kika dafa, kina nufin haka zan dinga zaunawa jiranki kullum kenan?" dafe kanta tayi saboda sarawar da yake mata gashi shi kanshi Salman k'in guda uku uku take ganinshi dan haka tace" kayi hakuri dan Allah ka taimaka ka siyo min madara wallahi mutuwa zanyi" wani kallo ya mata yana magana akan wani abu ita kuma tana magana akan wani abu daban, kafin ya ankara ya jita a k'asa ta dad'i hannunta kam har yanzu a kanta ya ke cikin bacin rai yace" ke dan Allah tashi miye haka kamar wacce tasha k'waya" ya jima yana mata magana amma kamar bada ita yake ba, dan haka ya ka mata ta mike tsaye ya zaunar da ita akan kujera, da k'yar take bud'a baki tana fad'in" madara yaya Salman dan Allah ka Siyo min in sha" hararanta yayi yace" ke tafi can sai naci na k'oshi in yaso na siyo maki jarababba kawai kin d'ora ma kanki shan madara kamar wacce saniya ta haifa" kanta a duk'e tace" kaima miyasa ba zaka siyo min ba in yaso sai kaci tuwon, kenan duk jarabar gare mu, kuma wallahi saina fad'ama la mamma nace ka ce mata saniya tunda ai kasan ita ta haifeni in ba kana san cin zarafinta ba miye na had'a yar da ta haifa da saniya" maida hankalinshi yayi ga cin abincin shi har saida ya koshi sannan ya fita ya barta a wannan halin.

Tunda ya fita bai sak
tuna wata Ummi ba harkokin gabanshi kawai yake hankali kwance har saida lokacin dawowar shi yayi da rana, kai tsaye yazo gidan yana shigowa baiga alamun girki ba dan haka ya d'auko belt a d'akinshi ya nufi d'akin Ummi da ke kwance tun safe ga ciwon kai ga zazzab'i ga amai da take na duk wani abinda ta ci.
Chapter 7 · 0% Book details