← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 49

Sashe 3

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read

Minti talatin kenan Jamal ya kira Ummi yace gashi nan K'ofar gida ta fito ko ya shigo tunda shi da aure yake santa, cewa tayi ya jira ta a bayan gidan su tana zuwa, duk da tace mashi tana zuwa amma ta d'auki Kusan minti sha biyar kafin ta fito ba tare da kowa yaga fitar taba, tana so ta fad'a mashi Komai akanta da auren da aka d'aura mata dan taba shi hakuri suyi sallama.
*To Allah ya kauda b'acin rana*
27/02/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*page*
zaune ta same shi cikin mota k'afafun shi a waje, yana ganin ta ya fito ya rufe k'ofar bakin shi har kunne, gaissawa sukayi a gurguje Ummi tace" am Jamal na fito ne dan na fad'a maka ko wacece ni, muna cikin halaka Jamal" cike da mamaki yace" halaka kuma wace irin halaka Ummi?" kanta k'asa tace" Jamal ni fa ba yanda ka d'auka b'ace, a yanzu haka ina da aure a kai na kuma na fito dan na fad'a maka haka, Dan Allah muyi hakuri da juna kaje ka nemi wata wacce ta fini,watakila ita ce mafi alkairi a gare ka" cikin wani irin yanayi yace" a'a Ummi dan Allah karki min haka, wallahi ina sonki, kuma na fad'a maki Komai a game da ni kinsan koni waye kinsan labaran soyayyata har guda hud'u, Dan Allah Ummi ki amince ki aure ni ko zaki canza wannan labaran nawa marasa dad'in ji, idan kuma baki so na ne basai kin b'ullo min ta wannan hanyar ba"
"A'a Jamal ba haka bane, wallahi an d'aura min aure yanzu haka gobe zan tare idan Allah ya kai mu" haba Ummi kar ki raina min Wayo mana, ki fito ki fad'amin gaskiya kawai" cikin kossawa tace" kaga Jamal na fad'ama gaskiya ina da aure dan Allah kar ka sak
kira na kuma ka manta da ni a rayuwarka, ka gafarce ni ban d'auka haka zata faru ba" zata wuce ya rike hijabinta yayi dai-dai da karasowar Alhaji Manu wanda ya tsinkaye su tun daga nesa amma yana tinanin ko su waye, yana ganin haka ya kunna tocilar shi dake hannunshi, da sauri Ummi ta juya sai ko yaga fuskarta, Ummi ma ba ganin Alhaji ta tsora ta sosai kubce hijabin''ta tayi ta ari na kare da gudu ta shiga gida, yayi dai-dai da fitowar La mamma da Abba tare da Salman suna tambayar k'annanta dake wasa a tsakar gidan.
yana ganin ta daka da gudu ya ciro wayar shi ya kira AUWAL Babban d'a ne ga baba Yahaya, yana d'auka yace" kai kana ina?" cike da ladabi yace" yanzu na shigo gida zan gaida su Mamma" to mu had'u da kai gidan baban ka Hamidu" bai ko amsa ba ya kashe wayar, tunda Ummi ta shiga d'aki ta kasa zaune ta kasa tsaye dan tasan yaou kam sai ta Allah babu abinda zai hana a dake ta a gidan nan, Addu'a ta ke koda za'a dake ta to kowama ya dake ta amma banda yaya Auwal.
kai tsaye falo ya shiga ya zauna yana 'kare ma su La mamma kallo babu wanda ya iya tambayar shi lafiya sa
da Auwal ya shigo sannan ya kalli La mamma yace" Hawatan kin bani kunya banyi tsammanin haka daga gare ki ba,na d'auka amanar da na baki zaki kula da ita ashe ba haka bane" cikin rashin fahimta jiki na rawa La mamma tace" mi kuma ya faru wallahi bansan Komai ba Alhaji" maida kallan shi yayi ga Salman yace" kira min ita"wucewa yayi yana tinanin komi ta aikata hatsabibiyar oho.
yanda yaga tana ta safa da marwa yasa yace" wace tsiyar ki kayi?" hararan shi kawai tayi taci gaba da kai da kawo warta," to wuce muje Alhaji na kiran ki kuma Allah yasa ya bani bulalar da kai na na zane ki" yan cikinta ne suka kad'a da sauri tace" bulala kuma?" gira ya daga yace" ai ke da kinga Auwal kinsan yana tare da bulalar shi sabida ire irenku" Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un na shiga uku, Dan Allah yaya Salman ka taimaka min wallahi babu abinda nayi, kace karya dake ni" ke wuce mu tafi ni babu ruwa na nasan mi kika aikata, ina mijinki amma bansan fitar kiba saidai naga kin dawo" wucewa yayi ya bar tanan kamar zatayi fitsari daga tsaye, jin muryar Alhaji ne yana fad'in" kaga kace in ba zata fito ba ni sai naga shiga na fiddo ta" a hankali ta bud'e K'ofar d'akin tana raba idanu ganin Auwal ya k'ara kad'a mata yan hanjinta, kusa da La mamma ta durk'usa kamar zata shige jikinta, cikin b'acin rai Alhaji yace" Ummi ni zaki zubarwa da mutunci, ni zaki tozarta a unguwar nan da aurenki ki fita kije wajen wani dan Iska har yana rik'e hannunki" to bari kiji wallahi baki isa ba ko ubanki bai isa in shinfid'a doka ba ya 'ketare bare ke yar da ya Ha
fa" carbin dake hannunshi ya tilla ma Auwal yace" zanemin ita ta yanda bazata sak
tinanin saba Umarni na ba nan gaba" tsabar rashin imani da tausayi yasa Auwal jayo Hijabin Ummi ya fara tsula mata carbi kamar Allah ya aikoshi, Ihu take tana ba Alhaji hakuri amma ina ga Abba zaune amma babu yanda zaiyi koda Ummi taji duka yana ratsa har cikin ruhinta sai ta fara kiran sunan" wayoo La mamma kice yayi hakuri wallahi bazan sake ba, Abba ka bashi hakuri wallahi babu abinda nayi, wayoo yaya Salman dan Allah kace yayi hakuri" har saida hijabinta ya fita ta zama daga ita sai doguwar riga, ganin yanda take ta k'o'karin shigewa jikin Auwal tana so ta rike carbi yasa Salman jin ba dad'i, mikewa yayi ya rik'e carbin ya kamo Oummi da hannu daya ya kalli Alhaji yace" Dan Allah ayi hakuri ba zata sak
ba Insha Allahu" mikewa Alhaji yayi tsaye yace" k'warai ba zata sak
ba kamar yanda ba zata k'ara koda Awa daya ba a gidan nan ba" kallan ta yayi ya daka mata tsawa" wuce mu tafi" raba ido tayi dan bata san inda zata wuce ba duk ta rud'e" zaki wuce ko sai'' na sa ya d'auko min ke?" da sauri ta d'auki hijabinta jiki na rawa duk zugi ta keji a jikinta sa
da ta kai bakin k'ofar d'akin ta juya ta kalli su Abba cikin kuka tace" Abba ku yafemin dan Allah, La mamma kiyi hakuri" da sauri ta bar wajen suna fita K'ofar gida Alhaji yace ma Salman " d'auko motar ka na kai ta gidan ta" mamaki yasa Salman yin tsaye amma daya mashi tsawa saiya wuce babu shiri ya d'auko mota, basu tsaya ko ina ba sai sabon gidan Salman da duka jiya ne aka kammala gyaran shi.

Yana iza k'eyar ta yace Salman ya maida shi gida suna tafiya Ummi ta fad'i a tsakar falon ta fashe da kuka tare da k'ara kamar ta kashe kanta take ji.
27/02/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*page*
Koda Salman ya shigo ya sameta nan bai tankata ba ya wuce d'akin shi, Oummi kam bata farka ba sai da aka gama sallah asuba tana tashi zaune tayi akan kujera tana tinanin inda zatayi alwala tayi sallah, zazzab'i ne ruf ya rufe ta da k'yar ta fito farfajiyar gidan ta samu panpo tayi alwala ta dawo falo tayi sallah ta koma ta zauna.

Har saida gari ya waye sannan Salman ya shigo gidan daga massalaci lokacin har bacci ya sak
d'aukar ta saman kujera, kallanta yayi ya kalli agogon dake mak'ale a bango dab da ita yazo ya kama kafar ta ya fizgo har saida ta fad'o k'asa, a tsora ta bud'e ido ta sauke a kanshi, gyara zamanta tayi cikin muryar da tasha kuka tace" miye haka dan Allah?" cikin fad'a yace" Dallah malama tashi kiyi sallah kin wani saki baki kina bacci har safiya tayi" hararan shi ta murgud'a baki tace" amma ai nayi sallah" tsayuwar sa ya gyara yace" to naji abin karyawa fa, ko shima harkin gama?" tashi tayi tsaye tace" haba dan Allah wane irin abin karyawa kuma, ni ban dafa ba kuma gaskiya ba zan'iya ba" tana rufe baki ya kama kunnenta ya murd'e yace" karki sak
bari saina maki magana akan abin karyawa, ki tashi kiyi abinda nasa ki idan kin gama zan fada komai a kaina dan bana san shirme" ganin batada niyar tashi yasa ya d'aga carbin shi zai tsula mata da gudu ta shiga cuisine kin ta fara had'a abin kari.
Chapter 3 · 0% Book details