← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 49

Sashe 5

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 6 min read

Zaman da matan shi suke sai san barka zama ne da kowace take girmama abokiyar zamanta, sabida tsari da tarbiyar gidan yasa kowane yaro bai san ainahin wacece ta haife shi ba, kowa mama ce kuma kowace tana d'aukar d'an yar uwar ta amatsayin d'anta, da haka ne Alhaji Hamidu ya saka ma yar shi sunan Zeinab duk da b
ita ta haife shi ba.

Ba iya nan abin ya tsaya ba har jikoki haka yake tsitar su da dai daya yana had'a su aure, sannan auren kaka manu kamar auren zobe ne babu saki saidai ya yarda duk wanda aka ma ba daidai ba ya kawo kara, amma ko yaji kayi to take za'a d'ora maka kayan ka aka ka koma inda ka fito.

Sabida rik'o da addini yasa babu d'
ko jika da ya kai shekara goma sha takwas ba tare da ya aura da shi ba, sai Oummi tayi wannan sa'ar sabida k'wak'walwa da Allah ya mata harta sauke Alkur'ani ta nada shekara goma sha hud'u sannan ta samu( BEPC) ta nada shekara goma sha shida, hakan yasa ya barta ta ci gaba da karatun Alkur'ani harta samu harda lokacin ta nada shekara goma sha takwas, Oummi dai ba wata kyakyawar yarinya bace face abu biyu da Allah ya bata, jar fata da manyan ido masu kyan gani sai dinple wanda ko d'umi take yake k'ara mata Kyaou
Salman shi ne na farko a duka iyalen da kaka manu ya fi so, dan haka yake daga mashi k'afa harya haura shekarun da ya ke ma mazan aure, amma ba dan yana so ba, dama yana cewa idan lokaci yayi zai bashi mamaki to gashi ya mashi aure babu shiri.
_Kwana hud'u kafin d'aurin_
_auren___ *Salman da Oummi*
~Ku ja muje
27/02/2019
17:31 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
_Cette page ce pour toi mon macho *Meelat AHK,* tu auras la b
diction da Dieu insha, que Dieu te b
nisse.

Bizou_
```dedecated to```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*Page*
Kamar yanda ya zama al'adar gidan yake idan ya rage saura sati d'aya a d'aura aure to amare su kan dawo da zama gidan Alhaji har a d'aura auren.

Ummi ma ta dawo tare da amaren dan b
zata iya zama babu su ba sune k'awayenta ita ce k'awarsu kuma yan uwan juna, yaou tunda safe suke takura Ummi akan taje ta karb'o sauran dinkin su daya rage amma sabida san jiki irin nata taki tafiya har saida marece yayi ta fara shirin tafiya amma kuma hajia Babba tace ba zata ba tunda babu wanda zai kaita kuma Alhaji ya hana su shiga adaidaita dan haka ta zauna jiran Allah ya kawo wanda zai kaita.

Zaune take tana jiran taga wanda zai shigo, kwatsam Khamis da Salman suka shigo cikin farin ciki suna hira,saida suka gaishe da su hajia suka fito zasu tafi hajia Babba tace" yaran albarka ina zaku haka?" Khamis ne yace" hajia yadai ko ba kisan mu fita ne?" tsaki tayi tace" kai tafi can ina ruwana da ku dan kun fita, wace uwar zaku bani idan kuna gidan ma, ina so inji inda zaku ne dan ku biyamin da wannan yarinyar" to ina zataje ita?" wajen tailleur kin su karb'o sauran dinkin su" to ai ba damuwa dama wajen aski zamuje yanzu, taso muje Ummi" Salman ne yace" kaga karfa ka d'auko mana yarinyar nan kasan yanzu raina zai b'ace" kafad'ar shi ya dafa yace" haba karka damu wannan fa k'anwarka ce" maida kallanshi yayi ga Ummi yace" taso muje".

Haka suka d'auki hanya Khamis da Ummi nata hirar su, Salman kuma ko tanke bai kula su ba har suka isa wajen, ta samu ana cikin dinke na k'arshe dan haka ta zauna ta jira Khamis kuma yace Salman ya kaishi wajen askin saiya dawo ya d'auketa, haka kuwa akayi ya dawo d'aukar Ummi amma na second d'aya bai jira ba haka ya fara zuk'a mata oder dole ta fito a hargitse tana saka kayan a leda ta shiga mota suka wuce, suna bisa hanya hadari ya taso aka fara iska gari yayi jawur harda baki ga k'ura da k'yar kake ganin gaban ka.

Salman ne yayi tsaki yana fad'in" wannan jaraba har yaoushe da irinta, gashi kinja min na rasa aski sabida bakin halinki kod'an saurayi ma ba kida shi wanda zai maki anfani idan irin haka ta taso, murgud'a baki tayi tace" e d'in banada ai kai naga kanada budurwar, kuma duk bakin halin mutum ai baya rasa massoyi saidai in hali baizo d'aya ba" da k'arfi yasa hannu ya bige bakin Yayana fad'in" yimun shiru kona taka ki yanzun nan marar kunyar banza" rufe baki tayi tace" wallahi saidai mu taka juna, haka kawai zaka takuramin" cikin d'aga murya yace" ke ni kike fad'awa haka, Allah saina sauke ki a nan naga abinda zai faru" cike da tsiwa Ummi tace" yo ka sauke ni mana saime inada wanda zai maida ni idan ma ka sauke ni" OK haka kika ce, to sauka ya fad'a lokacin da yayi parking kamar wasa ya sauke Ummi a nan ba tare da wani tinani ba, ganin yanda gari yake yasa har saida tayi kuka sannan ta matse kayanta ta d'auki hanya a k'afa.

Tafe take tana share hawaye tana tinanin abinda zata ma Salman idan taje gida, oder taji Daga bayanta wata tsaleliyar mota ce ke biyar ta amma bata tsaya ba har saida ya tare gabanta sannan ta tsaya, wani santalelen saurayi ne ya fito daga ciki yana fad'in" haba hajia inata oder amma kinki tsayawa" hararanshi tayi tace" to lafiya?" kinga yanzu dai ba wannan ba ki shigo dan Allah na rage maki hanya inba damuwa" sabida bacin rai yasa tace" da damuwa malam, dan Allah ka wuce ka barni" zata wuce taji anyi tsawa mai k'arfi alamar ana ruwa a wani wajen, abar da tafi tsoro kenan dan haka ta bud'e motar da sauri ta shiga tana k'ilu k'ilu da ido, dariya yayi ya shiga saida sukayi nisa yace" yan mata ni suna na JAMAL, ke kuma fa?" bata fad'a mashi ba sai kwatancen gidan su ta mashi dan ya sauke ta.

Dak'yar ya samu ta bashi number wayarta, tana fitowa yayi dai-dai da kawowar Salman dan haka tabi bayanshi dan ta sauke ruwan bala'i, Jamal kam bin bayanta yayi da kallo yana lasar leb'e yace" ina san faran mace amma fa badan na aureta ba, kema zan latsaki kad'an duk da naga akwai tsiwa da jan aji a tare da ita, amma ba komai naga wanda suka ninka ta so dubu dan haka zan fara shawo kanta kafin nan sai in abka mata" kara lashe leb'en yayi yaja motar ya wuce.
Chapter 5 · 0% Book details