Sashe 35
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Cike da rad'ad'i ta rik'e hannunshi sosai tare da matse fuska take wasu k'walla suka zubo mata, hannayenshi ya kai da nufin ya gyara mata zama zafi yaji a jikinta mai matuk'ar zafi sosai, gyara mata zaman yayi ya koma ya zauna yana kallon fuskarta, k'asa tayi da kanta yayin da take addu'a ya tashi ya fita dan ta koma ta kwanta dan zaman ba dad'i, hannayenta ya kamo duka biyu yace,
" *ZEINAB* kiyi hak'uri ki yafe..."da sauri Ummi ta rufe masa baki da hannunta, kai kawai ta girgiza dan ba zata iya magana ba ko tayi ma ba zai ji ba, kallon idonta yayi ya d'oke hannunta yace,
"A'a Ummi, ki barni na saka maki albarka tare da nuna maki tsantsan farin cikina idan ba zaki bari na nemi yafiyarki ba."
Ci gaba yayi da fad'in "ZEINAB, INA SONKI SO MAI TSANANI, SON DA BA ZAN IYA RAYUWA BABU KE BA."
"Ummi kin zama silar sauyawar rayuwata, kin sabinta min ita ta hanyar da banyi tunani ba, ko kad'an ban tab'a tunanin kece wacce zata kawo wannan sauyin a rayuwata ba, Ummi na san ni mugu ne a idonki kuma azzalumi, amma duk da haka baki hanani kanki ba a gaskiya na gode maki sosai."
Ganin hawaye na zarya a fuskarta yasa Salman rud'ewa ya fara goge mata da hannunshi yana fad'in "kiyi hak'uri idan na fad'i wani abu da bai maki dad'i ba, Ummi bana san ganin hawayenki ko kad'an saboda suna tab'amin zuciya sosai."
Tashi yayi tare da fad'in "bari na kawo maki tea kisha kafin na samo maki abinda zaki ci kisha magani, dan naji jikinki da zafi."
Yana fad'a ya fita ya barta, yana fita Ummi ta fara k'ok'arin saukowa daga gadon dan tayi fitsari ta dawo ta kwanta, ansha daga kafin ta iya sauko da k'afafunta tana sauke numfashin wahala, Salman ne ya sake shigowa d'akin dan ya tambayeta ko zata iya cin indomie ya dafa mata.
Tsaye yayi yana kallonta ganin ta kasa tashi yasa ya k'araso yana fad'in "bari na taimaka maki tunda naga kin kasa."
Hannu ta d'aga masa alamar ya barshi, kallonta yayi yace "bari na taimaka maki mana, ko zaki iya ne?"
Kai ta d'aga masa alamar Eh, d'aga kafad'a yayi yace "ok, zaki ci indomie na d'ora maki."
Dariya ce ta sub'uce mata har tana nunashi da hannu, cikin dakusashiyar muryarta tace "wai kaine zaka dafa indomie naci?"
Kallon mamaki ya bita dashi kafin yace "me kike nufi to, ban iya ba? to ni tun kafin a haifeki nake dafa abinci."
Kai kawai ta girgiza masa dan ita kad'ai ta san me take ji, juyawa yayi zai fita tace "yaya dan Allah ka kawo min madara."
Tsaye yayi yana kallonta kafin yace "kenan ba zaki daina shan madarar nan ba ko?"
Bud'a baki tayi tace "rayuwata ce fa, me yasa zan daina lokaci d'aya haka?"
"Saboda kin zama babbar mace."yana fad'a ya bar d'akin, binshi tayi da kallo kafin ta tab'e baki dan bata gane komai ba.
Cije leb'en k'asa tayi ta rufe ido haka ta dogara ta tashi da k'arfi har takai kanta toilet d'in, saida ta k'ara saka wasu ruwan zafin sannan ta kama ruwa dasu tare da yin wanka tayo alwala sannan ta fito, sallaya ta shinfid'a ta d'auko doguwar rigar Salman ruwan k'asa ta saka.
Zaune tayi bakin gado tana sauke numfashi dan kwance kawai take so tayi, Salman ne ya shigo da plate d'in indomie da robar madara da ruwa a hannunshi, ajewa yayi gefe ya kalleta yace " da alama kin fara cin gadona tun yanzu, ina fatan dai kinyi sallah?"
Cike da shagwab'a ta turo baki tace "kai nake jira ka d'auko min hijab, tunda kai ma ka ci gadon k'afafuna."
Dariya ya tin tsire da ita har ya fita daga d'akin yana dariya, yana kawo mata ta saka ta kabbara sallah a daddafe, tana sallamewa tabi lafiyar sallaya ta kwanta dan ko kad'an zaman babu dad'i, Salman daya fito daga wanka ne ya kalleta yace "malama tashi kici abincin mana, idan kin ida kya fad'amin me kika ji."
Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi tana fad'in "na fad'a maka me?"
Juyowa yayi ya kalleta yace "karki damu, ina nufin ki fad'amin ya kika ji abincin."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake komawa ta kwanta, har saida ya shirya cikin wata dalleliyar shadda (couleur pr
) d'inshi bleue sai walk'iya take kai dagani ka san ansha kud'i wajen, ga hula da takalma da agogo ta fata duka kalar d'inkin rigar bak'ak'e, wani irin shek'i ne fuskarshi keyi kamar sabon wata dan sha hud'u, bayan k'yali da fuskarshi keyi ga tsantsar kyanshi daya k'ara fitowa fili, k'amshi kawai yake zubawa na had'add'en turarenshi DOLBY, sak ya fito angonshi.
Da kanshi ya zo ya bata abincin sannan taci tasha madara ya bata magani tasha, saida yasha rarrashi kafin ta yarda tasha maganin.
Kwance ta sake komawa yana kallonta yace "anya kuwa Ummi zaki kai yamma, ko dai na d'auko wuka na k'arasa ki kafin ki min musai."
Sai dai ba tayi magana sai ko amai ya sub'uce mata, sosai tayi amai dan saida ta maido duk abinda taci, hankalin Salman ya tashi sosai duk ya rud'e ya rasa ya zaiyi, yana gyara mata jikinta d'auke sallaya ya wanke ya shanya ya dawo wajenta ya zauna yana kallonta.
"Ummi bari na d'auko maki kaya ki canja sai muje asibiti a duba min ke, dan watak'ila har na samu k'aruwar yaro ko yarinya."
Kunya ce ta rufeta ta fad'a jikinshi tana dukan k'irjinshi, zameta yayi daga jikinshi yace "ina zuwa."
Riga da zane ya d'auko mata simple d'inki ba kwalliya sosai, saida ya canja mata kaya kawai ta dage ita babu in da zata je kawai taje a mata tonon asiri sai kowa ya san me ya faru.
Dole ya sake bata parac
tamol tasha bayan tasha madara dan cikinta babu komai, komawa tayi ta kwanta ya rufeta da bargo ba jimawa bacci ya sake d'aukarta, ya jima yana kallon fuskarta gaba d'aya sai yaga yau tafi masa kyau akan kullum, wani shek'in amarci take ita kanta, falo ya dawo ya zauna dan dama ita yama kwalliyar kallo ya fara cike da farin ciki murmushi ya kasa barin fuskarshi dan har yanzu yana taro daren jiya, daren daya fi kowane dare a wurinshi daren da ba zai tab'a mantawa dashi ba, ajiyar zuciya ya sauke fuskarshi d'auke da k'asaitaccen murshi yace,
"Ummi ba dai zafi ba."
_Hum wai zafi._
25/03/2019
16:14 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
~ALLAH YA BARMU DA MASU SON MU~
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Har sallah azahar Ummi na bacci saida Salman ya dawo daga masallaci ya tasheta tayi sallah, tana kammalawa ta fito falo da tafiya kamar mai koyo tana zuwa ta zauna k'asa kusan k'afafun Salman, saukowa yayi ya zauna kusa da ita yana fad'in "aljannata ya jikin naki?"
Kallonshi tayi da mamaki tace "aljannarka kuma, yanzu kenan na tashi daga aljana na koma aljannarka?"
Gira ya d'aga mata yace "in dai har Ubangiji yana bamu aljanna a duniyar nan, to ni kece aljannata."
Had'a kanta tayi da gwiwa tana murmushi, yana ganin haka ya fara mata cakulkuli yana fad'in "tunda ba zaki fad'a ba sai mu sake komawa ciki."
Ummi kam dariya take tana bille bille duk ta hayeshi, saida yaga hawaye sun fara fitowa a idonta tsabar dariya sannan ya daina, ba tare data tashi daga jikinshi ba ta gyara kwanciyarta ta yanda suke kallon juna tace "nifa yunwa nake ji."
Wani kallon so ya mata yace "na sani dama dole zaki ji yunwa, amma kiyi hak'uri na kira Mama na fad'a mata kuma yanzu zata aiko maki da abinci."
Cikin yaushi ta kalleshi tace "yanzu fad'awa Mama kayi?"
"A'a, na dai fad'a mata ba kiyi d'ori ba tasa dake a nasu."
Kallonshi tayi tace "yaya Salman na d'auka fita kayi duk kasa hankalina ya kasa kwanciya."
Cike da mamaki yace "me yasa?"
"To ai naga kayi kwalliya ne dayawa, kuma naga ko a aurenmu ba kayi irinta ba."
Dariya yayi yana kallon fuskarta yace "kwalliya fa,to kenan kwalliyarce ta d'aga maki hankali?"
"Yaya Salman ina jin baka duba madubi ba bane shi yasa, kai kyakyawane kuma yau naga kafi kullum kyau, kaga dole hankalina ya tashi dan ban san da suwa zaka had'u ba."
"Wai mata kike nufi?"
Turo baki tayi tace "Eh mana."
Gashinta ya fara shafawa yana fad'in "da a jiya kika fad'i haka kafin dare, to da saina yarda, amma yanzu ni Salman na Ummi ne ita kad'ai babu k'ari."
Murmushi tayi sosai hakan yasa ya saka d'an yatsarshi a kurmin kumatunta yana kallonta cewa tayi "amma fa yaya Salman kai kace zaka k'ara aure."
"Eh, a dah kenan, amma banda yanzu da Ummi ta zama ta Salman suka had'u suka zama manyan yara."
Dariya tayi tace "ni dama babbar yarinya ce."
"Da gaske, to shikenan zamu gani."
Cikin shagwab'a tace "yaya Salman da gaske ba zaka k'ara aure ba?"
Murmushi yayi yace "ba zan k"ara in dai kina tare dani."
Tashi tayi zaune ta tara mashi tafin hannunta tace "ka rantse ba zaka k'ara ba."
Fashewa yayi da dariya ya janyota jikinshi ya had'e kanta da k'irjinshi yace "Allah ya shirya min ke."
Tashi tayi daga jikinshi tace "yaya Salman wallahi da gaske nake, in san samuna ne na zauna da kai ni kad'ai, wallahi ba zan juri ganinka da wata mace ba."
Tsaida dariyar sa yayi ya sauke ajiyar zuciya, tabbas ya fahimci da gaske take kuma ga dukkan alama Ummi zata iya yin komai dan taga ta sameshi ita kad'ai.