← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 49

Sashe 6

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read

K'ofar gidan ta tsayar da shi tace" to dan ciki bakin nazo gida lafiya babu abinda ya sameni sai ka mutu tsabar takaici" tana fad'i ta wuce gidan su Alhaji a tinanin su kuma Salman ne ya dawo da ita, tana shiga su Khairat suka karb'i kayan suka fara dubawa, ba bata lokaci saiko aka keto da ruwa mai k'arfin gaske.
_To bari muji wai wannan Yar tsama yaoushe ta fara tsakanin Ummi da Salman ne?
27/02/2019
17:32 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
```Mommyn Khadija``` ( ma Belle)
```Mommyn Sultan```
```Mommyn Labyb``` (Mamien mu)
```My Heenat``` (Raheenat)
```Choukoura``` (Chouk Beby)
```Halima```
```Maman samha```
( *Cette page ce pour vous)*
~Luv u
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana insha Allah)
*Page*
__A fahimtar Salman shine k'arshen rainin da mace zata ma namiji to ta harareshi ko tsaki had'e da murgud'a baki, dan ko a film yaga haka to ya tsani wannan matar kenan dan ko miji da matar shine ta_ _ma shi haka to ta gama raina shi dan haka ya tsani abin sosai._
__Tunda Ummi ta tashi tana k'arama ya zama in dai Salman zai mata magana to sai tayi abinda ya tsana harta girma, bayan ta mallaki_ _hankalin kanta sai ta gane Salman baya so ita kuma sai ya zama d'abi'arta hakan, duk lokacin da yake mata fad'a ko ya dake ta akan ta raina shi sai Mahaifiyar shi tace, kawai dai dan ya sama ransa ne shiyasa ko d'umi tayi sai yaga kamar tayi abinda baya so, Mahaifiyar Ummi kuma tana cewa, da gangan ta keyi dan tasan baya so, to haka_ _dai ya zama kowa da bayan wanda ya ke bi, kasancewar su mak'otan juna dan Ummi bata wanka ta bushe sai a gidan wajen k'awarta Khairat, haka ma Salman ya fi wuni gidan akan gidan su sabida k'annan Ummi da Mahaifiyar su yana jin dad'in zama da su._
_Rayuwar Iyalin tana da ban sha'awa dan Ummi da su Jawahir duk lokacin da babu
cole ko makaranta to suka_ _zab'i gidan da zasu je su kwana biyu a can, haka zasu dinga farin ciki suna d'aukar photunan junan su sabida_ _tarihi shiyasa suka shak'u sosai ba su tab'a samun sab'ani ba._
_In dai Ummi zata ma Salman_ _abinda baya so to ya kan dage ya tumurmushe ta san ransa kuma hakan ya samu asali ne sabida la mamma tace duk sanda ta mashi to ya daketa har sai ranar da ta daina dan kanta, burin Iyayen nasu bai wuce suga an had'a auren su ba to amma yaran ma sunki jituwa tsakanin su duk da dama ana had'a_ __auren ne ba sai wanda ka ke so ba ko ku ke fahimtar juna._
```Wannan kenan```
Washe gari amare suka shirya zuwa wajen kitso,Salman da Khamis ne su ka kai su a mota ma saida aka samu matsala tsakanin Ummi da Salman sakamakon..., sorry dear wayar ta gaji
27/02/2019
17:33 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*(Yan uwa ku gafarceni a bisa kuskuren da nayi wajen saka num page, kamata yayi wannan ta zama 27-28)*
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*Page*
Salman da Khamis ne a gaba, yayin da su Jawahir ke su biyar ke baya Ummi kuma tana bisa k'afafun Jawahir a bayan kujerar da Salman ke tuk'i, saboda rububin da yayi yawa da ramuka dake wurin yasa Salman shiga wani rame da baisan da shi ba hakan yasa kowa saida ya girgiza Ummi da ke k'afafun Jawahir saida tayi kamar zata fad'i da sauri ta rik'e kafad'un Salman duka biyun tare da fad'in" Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raju'un, malam kashe mu kake so kayi ne?"da k'arfi Salman ya fizge hannayenshi yana fad'in" ke wannan wani irin abu ne? muguwa kawai" mugu dai, kaji mutum kamar makaho da ba zaka kalli inda zaka saka mu ba" ke rufa min wannan banzan bakin naki kinji ko" idan kuma naki fa saime ya faru?" sai kisha dan banzan duka kuwa mahaukaciya kawai" turo baki tayi ta harare shi kallanta yayi ta madubi dan haka ya zuro hannu ya mazge kanta, haka suka kai suna fad'a.

Amare kitso aka masu Ummi kuma kunshi, bayan sun koma gida duk da dare yayi amma la mamma ta mata nata kitson kanana mai kyawun gaske irin na buzaye.

Yau ta kama ranar Juma'a washe gari kuma d'aurin aure, Ummi da amare ne zaune a d'aki suna hira hajia Babba ta kira Ummi tana fitowa tace" d'oki abincin nan ki kaima su Khamis a d'akin baki" Kallan hajiar tayi tace" su yaya Khamis kuma,miya kawo su nan da har za suci abinci?" to ina ruwanki?kiyi abinda na saki kawai" gwalo ta mata tace" naji tsohuwa mai ran k'arfe"duka ta kai mata bata sameta ba tace" ke tafi can in banda shegantaka babu abinda kika aje" d'auka tayi ta wuce tana dariya.

Saida tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga, tana ganin Salman ta murtuke fuska irin babu wasa dinnan, gaishe da Khamis tayi ta duk'a ta aje ta tashi zata tafi Khamis yace" k'anwata ina kika baro min amarya ta?" murmuchi tayi tace" yaya Khamis ko dai zance kazo? in kira maka ita" dariya yayi yace" a'a rufan asiri karki sa tsohon nan ya balbaleni da masifa" dariya tayi ta juya zata tafi idonta suka sauka akan Salman dake kallan kumatunta, harga Allah suna birgeshi idan sunan lotsawar nan amma ba yarinyar ba, kamar daga sama Ummi tace" malam lafiyar kallo na?" cikin d'aure fuska yace" ke ni sa'anki ne? wallahi ki kiyaye ni" juyawa tayi ta fita saida ta kai kofar d'akin tasa takalminta sannan tace" kana kallan mutum kamar maye" da gudu ta ida fita shi kuma ya bita da kallo ya, girgiza kai yayi yace" Allah ya shirya ki" Khamis ne yace" da wannan Addu'ar ka ke mata ma tun tini da yanzu ta shiryu" tsaki yayi yace"wannan din?ai ka barta inda ka ganta kawai" abincin suka ci bayan sun kammala suka fito Khamis ya shiga wajen su hajia, Salman kuma ya nufi b'angaren Alhaji.

Bayan sun gaisa Alhaji yace" Salman kaga dai yanzu gobe za'a d'aura auren yan uwanka, na so ace da kai a ciki amma Allah bai nufa ba, nayi nayi da kai ka fiddo da mata a cikin yan uwa, amma kayi wasa da damar da na baka wacce ban taba bawa kowa ita ba, amma ba komai akwai lokacin da zan baka mamaki" kanshi k'asa yace" kayi hakuri Alhaji, insha Allah zan samo nima nan ba dadewa ba" kafadu Alhaji ya daga yace" kai ka sani, ni nasan da ka duba da ka samu, tunda ga sunan birjik muna da su iri iri, in kuma wannan ka kake so abokiyar fad'anka sai ka fad'a babu yar da zaka nema ka rasa a cikin dangin nan" wani kallo Salman ya masa kafin yace" ba komai Alhaji zan nemo, amma ba wannan ba" haka su kayi sallama Alhaji yana mamakin irin wannan rashin jituwa.
27/02/2019
17:33 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Washe gari da safe, Ummi ce keta bilinbituwar neman chargeur ta saboda wayar ta ta kusan d'aukewa, cikin masifa tace"Khairat ke wai ina kika d'ora min chargeur ta ne?" Khairat da ke dunkule cikin hijabi tace" to ni ina zan sani tunda ban d'auka ba" ke wallahi ba zan yarda ba, duk in da kuka kaita sai kun fiddo ta" Nadia ce ta lek'o da kanta daga cikin hijabi tace" ke jiya fa yaya Mubarak ya aiko yaro aka karb'ar masa shi ma wai bai ga ta shi ba" hararanta tayi tace" oho kenan ke kika bada dan yana mijinki? kuma kina ji ina tambaya kika min shiru, ta tashi ki karb'o min kaya ta" ido Nadiya ta fiddo tace" wacece zata karb'o makin?ina ga ko da ba kiyi abinda za kiyi da ita ba, kafin wannan ranar ma aka hana mu zuwa b'angarensu bare kuma yau" tsaki tayi tace" to kenan nice zan karb'o da kaina, wai ku dan kunga zaku aure ne shiyasa kuka raina ni?" a'a su Ummi manya ba haka bane, kije dai da Kanki zaifi" amma kinsan yanzu suna tare da wannan dan rainin hankalin,ba zan juri kallon banza ba ma daga gare shi bare bak'ar magana" dariya sukayi dan sun san wa take nufi, juyawa tayi ta fita Jawahir kuma cewa tayi" kai Allah yasa a had'a yaya Salman da Ummi aure muga cakwakiya" Hafsat ce tace" ke ai ko in Ummi bata kashe shi da bakin ciki ba, to shi ya kashe ta da duka, ai had'a su bana jin zai haifar da d'a mai ido".
Chapter 6 · 0% Book details