Sashe 11
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Haka ta wuni jiki babu k'wari ko girki bata yi ba tunda Salman ba zai dawo ba, haka yamma tayi ta fara shirya mashi abin bud'a baki ba tare da ita taci komai ba, ta kammala da wuri yana zuwa ta shirya komai haka ta kula da duk wani abunda zai ci har ya fita bayan sallah isha'i sannan tayi wanka ta zauna tsakiyar gado ta nata runguzar kuka kamar yarinya saboda takaicin abinda ya isheta.
28/02/2019
17:02 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
```Luv you my fans```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Ko da ya shigo d'aki ya sameta tana ta faman kuka sa
sharbar majina take alama taci kukan ta koshi, zaune yayi yana fuskantar ta yace" wai har yanzu kuka kike? to miye la mamma ta fad'a maki ne haka?" dama tana neman wanda zata fad'ama damuwarta ko zata d'an rage zafi sai ko ta fara magana cikin kuka" yaya Salman wai miyasa Alhaji yake mana haka ne, miyasa baya k'aunar mu, miyasa har yanzu shine mai alhakin ruwa da tsak'i a al'amuran mu, miyasa baya fahimtar soyayyar dake tsakanin Iyaye da yayansu shi kawai kansa ya sani.?"
"Ka duba kaga abinda ya min, ya min aure bada sani na ba ba tare da na shirya ba na hak'ura, amma sa
da ya kawo ni gidan miji kawowar da bana jin akwai wata ya mace a tarihin duniya da aka tab'a mata ita sai ni shi ma na hak'ura, amma bai ishe shi ba shine yanzu zai zareni daga cikin yan uwana ya hana ni zuwa inda suke, kuma suma ya hana su zuwa inda nake, wannan wace irin uk'uba ce dan Allah, wallahi ni ba zan iya zama a gidan nan ba yaya Salman, ni dole na tafi gidan mu dan in na zauna nan to kasheni za kayi da duka" rigar baccin da ta saka ta tub'e da k'arfi tana nunawa Salman jikinta da fuskarta tana fad'in" ka duba ka gani yaya Salman jikina duk shatin bulala ne, dukan da Alhaji yasa aka min a gaban mahaifana da kuma wanda kai kamin, wallahi ba zan iya zama a gidanka ba yaya Salman saboda b
kada imani ko kad'an k'eta kawai ka iya" fad'awa tayi jikinshi tana kuka da k'yar Salman yasa hannu ya fara shafar bayanta amma da ya ji laushi sai ya fara mata wani salon shafa har yana 'ko'karin kaiwa a k'irjinta dan haka ta d'agashi ta kwanta akan gado taci gaba da kukanta, a kasalance Salman ya koma d'akinshi ya kwanta gaba d'aya ta rikita mashi lissafi ko kad'an bai iya tuna abinda ta fad'a ba, shauk'in da ya ji lokacin da ta rumgume shi kawai ya keji, da k'yar bacci ya d'aukeshi cikin wannan mawuyacin halin da bai taba jin irin sa ba a rayuwar shi.
23:00 Ummi ta shigo d'akin cikin sallama da muryarta data dakushe wajen kuka, har ta aje faranti ta zuba mashi duk yana bacci bai san ta shigo ba, saida ta daddab'a pilow da yake kwance sannan ya tashi aje masa tayi ta ta koma d'akinta.
Tun 07:30 Ummi ta kammala had'a abun karyawa amma bata ji d'uriyar Salman ba haka ta zauna tana jiran taga fitowar shi, 09:20 ya fito da dogon wando sai singlet fara k'al kallonshi Ummi tayi ganin ba wani shiri bane yayi amma ya yi masifar had'uwa a cikin zuciyarta tace(na tabbata yaya Salman b
yada burin auren mace irina, shi ma zaiso ace ya auri kyakyawa kamar shi amma Alhaji ya masa yankan k'auna).
Zaunawa yayi ya karya dan Ummi har tayi nata break d'in, yana idawa yace mata" ki fito min da kujera waje" yana wucewa ta mik'e ta d'auki d'aya daga cikin na dinning ta kai masa zata juya ta tafi yace" zauna nan" jujjuyawa tayi ganin babu wata kujerar yasa tace" bara na d'auko kujera" kallon daya mata yasa ta cire takalminta ta zauna in da ya nuna mata, k'afa ya d'ora mata a cinyarta tare da mik'a mata abin yankar akaifu kallonshi tayi baki bud'e tace" wannan kuma fa, miye haka?" bai tanka taba hakan yasa ganin babu wasa a al'amarin yasa ta fara masa gyaran akaifun, kuma abin takaicin ma babu wani abinda za'a cire haka kawai tayi iya yinta ta cire na cirewa tana idawa dana k'afa ya mik'o hannu, nan ma Kallon shi tayi tace" yaya Salman wai miya samu hannayen naka?" Hararan ta yayi yace" wallahi zan zubar maki da hak'ori" turo baki tayi ta rik'e hannun, Kallonta yayi ya kalli hannunta saboda wani sanyi da ya ji tattausan hannun Ummi ma'abocin zufa a kowane yanayi zafi da sanyi, haka hannunta yake cikin zufa kowane lokaci, sab'anin nashi mai cikakkar tsoka da dogayan yatsu da santsi haka Ummi ta gama masa gyaran tsaf tana idawa yace" to maza kije d'akina ki d'auki d'aya daga cikin jakunkuna da ke da kwai ki shiryamin k'ananan kayana a ciki da duk wani abu da mutum zai buk'ata idan yayi tafiya." kai ta dafe cike da nuna damuwa kafin tayi magana yace" ba zaki yi ba ko?" kai ta girgiza sannan ta wuce jiki a sanyaye, Sa
da ta b'ace ma ganinshi sannan ya kau da kanshi.
Tsaf Ummi ta had'a mashi kayanshi tare da duk abinda zai buk'ata, kama daga turare maclean brush mai zanin rufa kayan bacci ect...., tana idawa ta shiga cuisine dan had'a abincin rana dan 12:50 tayi, tana cikin aiki ya lek'o yana fad'in" ina aikin dana saki?" cikin sauri tace" na kammala suna d'aki" hararanta yayi yace" amma ba kisan ki ce kin gama aiki ba idan an saki?" turo baki tayi tace" kayi ha'kuri"wucewa yayi ya barta, d'akinshi ya shiga ya bud'a kayan sosai ya ji dad'in ganin yanda ta had'a masa kayan ba tare da ya nuna mata ba harda ma abinda shi kanshi bai taba tunanin d'aukaba duk lokacin da zaiyi tafiya wato maclean da brush, duk lokacin da yayi tafiya saidai ya siyi sabbi idan zai taho kuma ya baro su dan sun gama mashi aiki, wanka yayi ya shirya cikin dogayen kaya da hula yayi kyau sosai yana fitowa ya k'walla kiran Ummi har tuntub'e take wajen sauri tana zuwa ta zube k'asa tana fad'in
"Gani"d'auko min sallaya" mik'ewa tayi ta d'auko mik'a masa tayi, hararanta yayi yace" bara na sunkuya saina karb'a ko?" turo baki tayi sannan ta sunkuya ta mik'a masa, yana karb'a yace" wuce muje " binshi tayi tana guna-guni har sa
da ya shiga mota sannan yace" oya, kimin Addu'a zan fita" dalala ta kalleshi tace" yau dai da alama bokan naka ce maka yayi saina maka addu'a sannan harkokin zasu tafi yanda ya kamata ko?" cikin zafin rai ya bud'e k'ofar mota yana shirin fitowa, da sauri ta maida k'ofar ta rufe tana fad'in" sai ka dawo to" juyawa tayi zata wuce yace" ke wannan ce addu'a, haka ake a garin ku?" murgud'a baki tayi tace" in dai sai na maka addu'a zaka tafi, to ka kwana anan" da gudu ta shige d'aki, shi kuma k'wafa yayi yaja mota yana fad'in" lallai da sauranki har yanzu, amma zanyi maganinki nan ba da d'ad'ewa ba."
Tana gama aikinta tayi sallah tana idawa ta shiga gyaran d'akinshi tana kammalawa ya dawo gidan, sa
da yaci abinci sannan ya shiga d'aki ya tattaro mata kayanshi k'anana yace ta wanke, saida tasha mari sakamakon cewa da tayi" haba dan Allah wannan wane irin rashin imani ne? wannan kayan ina zan iya wanke su, nifa ko a gidan mu bana wanki bare kuma nan" bakinta ya murd'e yace" nan ai ba gidan ku bane gidan mijinki ne, kuma daga yau karna sak
jin kince min mara Imani, in kuma ba haka ba wallahi saina sauke maki Kafad'a" tsaki tayi tace" wai miji, ina mijin yake anan? saidai muna maza" ji kake Tasssss, ya kasheta da mari tare da fad'in" ke har kin isa ki fad'amin haka, wallahi ko Sa'ada dake gaba dake bata isa ta fad'amin haka ba, bare kuma ke da aka ha
fa a gabanta" haka ta fara wanki tana kuka tana fad'a, bata gama ba sai misalin 17:40,saboda ko a gida ita ma kayan da suka zama wajibi ne a gareta ta wanke da kanta take wankewa, amma manyan kaya mai wanki ake bawa ya wanke mata, amma yau gashi tana ma k'aton gardi wanki( inji Ummi fa).
Tana idawa ko wanka bata yiba ta d'ora girkin dare, a gajiye ta kammala aiki bayan sallah isha'i, tana gamawa ta aje Kwanukan a dinning tayi alwala tayi sallah tana sallamewa daga nan bacci ya d'auketa ko shafa'i da witri bata yiba, Salman na lek'awa yaga tana bacci ya fito yana cewa" raguwar banza, ai dama da gangan nake saka ki aikin dan babu tsiyar da kuke a gida ke da su Khairat da jawahir sai iskanci da zuwa gidajen juna ana d'aukar photo" da kanshi ya zuba abincin yaci ya koma d'akinshi yana latse latse a ordinateur d'in shi, jin an fara kad'a iska ga walk'iya da ake ana cikin haka aka fara yayyafi har ruwa suka fara k'arfi, ganin an d'auke wuta yasa ya kunna wutar wayar shi ya tashi ya nufi d'akin Ummi dan yasan yanzu zata fara neman taimako, k'aro yayi da Ummi k'ofar d'akin tana shirin fitowa daga ita sai towel d'in dake d'aure a k'ugunta tana shafa turare aka d'auke wutar, kallon juna su kayi sum sum Ummi ta haye saman gadon ta kwanta, Salman ma zaune yayi gefenta tsawon lokaci ya d'auka a zaune, ganin ba ada niyyar maido wutar ya gyara kwancinshi shi ma bacci ya d'aukeshi.
Salman ne ya fara farkawa da k'yar ya bud'a idonshi saboda haske an maido wuta suna bacci, addu'ar tashi daga bacci yayi( Alhamdu lillahi lazhi ahayana ba'ada ma amatana wa ilaihin nushur).