Sashe 27
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read
D'akinshi ya koma yana tunani akan abinda ta fad'a har bacci ya d'aukeshi, ita ma bacci ne yayi gaba da ita.
05/03/2019
17:33 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Tunda safe Ummi ta tashi ta had'a abin karyawa iya bakinta ta ci, tana kammalawa tayi wanka ta komo falo ta zauna tana kallo, Salman ne ya fito daga d'akinshi singlet da dogon wando da alama sport zai je.
Ko kallonshi Ummi ba tayi ba haka ta zauna har ya dawo saidai baiyi gumi ba saboda ansha ruwa jiya, d'aki ya shiga kai tsaye ya shiga toilet dan yin wanka, yana fitowa ya shirya cikin k'ananan kaya sannan ya fito falon.
Ba tare daya kalleta ba yace "tunda har yanzu ba kiyi wayon gaida mutane ba, to ki kawo min abinci na."
Bata kalleshi itama tace "iya bakina kawai na dafa kuma na cinye."
Wani kallo ya watso mata kafin yace "Ummi karki saka ni abinda banyi niyya ba, ki kawo min abinci na kafin ranki ya b'ace."
Saida ta watsa masa harara ta murgud'a baki sannan tace "kaji min mutum dan Allah, to wallahi ba zai yiwu ba haka kawai ni da ciyar da kai kuma wata da morarka, kaje mana amaryarka ta baka abincin."
Dariya ce ta sub'uce masa bai shirya ba, sosai yake dariya har da rik'e ciki yake, Ummi kam ta gama cika dan haushi kawai sai taja dogon tsaki, shiru Salman yayi yana kallonta kafin ya mik'e tsaye yasa hannuwa aljihu yace,
"Ok zan tafi naci a waje, amma fa karki manta Salman d'an dangi ne, iya gidansu Khamis ma kad'ai zan iya cika ciki na har saina ture."
Yana shirin ficewa Ummi tayi karaf ta rik'e hannunshi tana fad'in "a'a dan Allah kayi hak'uri to zan dafa maka abinda kake so."
Kallonta yayi ya kalli hannun data rik'e yace "sake min hannu malama"
"Dan Allah kayi hak'uri wallahi zan yi." ta fad'a kamar mai shirin fashewa da kuka, dawowa yayi ya zauna bisa kujera har yanzu tana rik'e da hannunshi, kallonta yayi sosai kamar yana so ya fahimci wani abu a tare da ita kafin yace,
"Mi amarya ta ta miki ne haka? tun jiya kike masifa a kanta."
Dama kamar jira take sai kawai ta fara kuka kamar an k'wak'wale mata ido, Salman kam shiru yayi yana sauraranta har ta gama, kusan minti shabiyar tayi tana kuka kafin ta bawa kanta hak'uri ta share hawaye ta kalleshi tace,
"Yaya Salman wai da gaske aure zaka k'ara?"
Cike da gamsarwa yace "e aure zanyi, miya faru?"
Shan majina ta fara tare da saukowa daga kan kujera ta zube akan gwiwoyinta biyu ta had'e hannayenta biyu alamar rok'o tace "yaya Salman dan Allah kayi hak'uri karka k'ara aure, wallahi ni kuma nayi maka alk'warin zan canja zan zama yanda kake so kuma zanyi duk abinda kake so."
Hannayenshi ya d'ora akan gwiwoyinshi yana kallonta cikin mamaki yace "Ummi me yasa ba kya so, miye matsalarki idan na k'ara aure?"
Kuka take sosai tace "ban sani ba nima yaya Salman, kawai dai bana jin dad'i idan kace zaka k'ara aure zafi nake ji a cikin nan da k'unci." ta fad'a tare da d'ora hannu a k'irjinta b'angaren zuciyarta.
Wani irin murmushi Salman yayi najin dad'i yayin da yake fad'a a zuciyarsa "lallai wannan so ne kuma Ummi tayi nisa, kawai dai ta kasa fad'a kamar yanda nima na kasa fad'an komai."
Da hannu ya mata alama ta zauna kusa dashi, tana zaunawa ya kalleta yace "Ummi da gaske kike fad'an maganar nan?"
Cikin kuka tace "wallahi da gaske nake yaya Salman, ba zan sake maka rashin kunya ba."
Shi kam kamar yayi dariya amma ya rik'e, cewa yayi "ok tunda kince haka na yarda, amma a bisa wani sharad'i."
"Na yarda koma wane iri ne in dai zai hana ka k'ara aure."
"Ok ba zan k'ara aure ba in dai zaki dinga jin magana ta, amma ki sani duk sanda kika min ba daidai ba to tabbas a satin nan k'anwarki zata shigo gidan nan a matsayin amaryarki."
Saida ta harareshi ta gefen ido tace "na yarda, kuma wallahi idan nayi abinda kake so kuma kace zaka k'ara aure to wallahi...." mik'ewa tayi danta had'a mashi abin karin, da sauri ya rik'e hannunta yace,
"Wallahi me?"
Saida ta nuna shi da yatsa tace "saina kashe ka, dan ba zan had'u ni da wata a kanka ba." Fak'at
Wucewa tayi Salman ya bita da ido "anya yarinyar nan ba zata kashe ni ba kuwa in ina maganar auren nan?"
_Ah to koma dai miye ni dai ina daga nan_
Haka ta wuni ita d'aya a gidan jikinta yayi sauk'i sosai shi yasa ma babu wanda yazo gidan dubata saidai kiranta a waya kawai, har dare haka ta kammala 'yan aikace aikacenta kafin Salman ya shigo gidan, kai tsaye d'akinshi ya shiga yayi wanka yana fitowa ya shafa mai, tsaye yayi yana kallon kayan da zaisa kafin daga bisani ya yanke wata shawara.
"Abule, Abule, wai Abu bata jine?" Salman ne fa ke kiran Ummi haka, Ummi dake zaune falo tun kiran farko taji tasowa tayi tana fad'in "haba wallahi saina maka rashin mutunci in kana kirana da wannan sunan."
"Gani" ta fad'a a tsaye, kallonta yayi dan bai san da shigowarta ba hankalinshi na kan sak'on daya shigo wayarshi yanzu, ba tare daya kalleta ba yace "fiddo min kayan da zansa."
Kallon ba kada hankali ta bishi dashi har ta bud'a wadrob d'in ta d'auko wasu bleue noir rigar kamar singlet saidai hannuwan suna da fad'i sai dogon wando.
Aje masa tayi tana kallon wayar dake hannunshi, tashi yayi ya aje wayar dan yasa kaya, sai kawai idonta ya sauka kan chart d'in da suke da mai wannan sunan *Reine*, da sauri ta d'auki wayar tana kar'ema photon Nuseiba kallo wanda ga dukan alama yanzu ta aiko shi, a k'asa kuma ta rubuta,
__kana da girma a wajena yaya Salman, ba zan iya had'a ido da kai ba koda a photona ne._"
Jin hawaye sun taho mata ne yasa ta aje wayar tana kallonshi, kallonta yake shima kafin yace "ya dai lafiya?"
"Allah zai saka min in har kaci amana ta, kuma wallahi zanje na samu Nuseiba har gida sai naji dalilin da yasa take kula ka, azzalumai macuta kawai."
Zata fita ya rik'o hannunta tare da fad'in "ke kina hauka ne, wai mi yake damunki ne?"
Cikin b'acin rai ta fizge hannunta tace "l
che moi (sake ni)"
Tana fita d'akinta ta shiga ta fad'a saman gado ta fashe da wani kuka mai cin rai da ban tausayi.
*Kishi kenan, zama da kishiya sai dole amma idan a kayi hak'uri to komai ya kan zo ya wuce kamar bai faru ba, mu dinga saka hak'uri tare da tausar zuciyar mu da kuma addu'a, dan ba kowace mace bace zata iya hak'urin ganin ta had'a miji da wata.* _Allah kasa muyi kishi mai tsabta irin na matan Annabi (S A W)_
Yana saka kaya ya d'auki wayar yana kallon Nuseiba kafin yace "kiyi hak'uri ba zan iya juran ganin hawayenta ba, in dai har a kanki ne take shiga k'unci to daga yau ba zata sake b'ata ranta ba, ina son aurenki ne saboda kashe wata matsalata, amma idan maganar so ake to Ummi ce a cikin zuciyata dama birnin raina, bana jin wata ko wani abu kamar yanda nake jinta a cikin zuciyata dan haka daga yau komai ya k'are, ba wai zumuncin mu ba saidai daga yanzu ba zan sake maki kallon wacce nake so na aura ba, daga yanzu kin koma k'anwata kamar yanda kike a da, Ummi kuma zan ci gaba da k'ok'arin sakata farin ciki da yardar Allah."
"Dole na guji b'acin ranta in dai har a kaina take kishi haka, ban san me take ji ba amma da zan iya kwatantashi da abinda naji jiya lokacin da tace min wannan likitan ya rik'eta, to tabbas ba k'aramin b'acin rai da tashin hankali take ciki ba."
Yana fad'a ya canja sunan Nuseiba daga Reine zuwa Cousine Nuseiba kamar yanda yake a sauran numbobin 'yan uwa, d'akin Ummi ya shiga sosai ta bashi tausayi ganin ta dage tana kuka dan taji sauk'in abinda ke damunta.
Zaune yayi tare da d'agota ya d'ora kanta a k'irjinshi yana fad'in "haba Ummi duk wannan kuka dan kinga photon Nuseiba ne? amma ai ni na maki alk'awarin na fasa ko?"
D'agawa tayi daga jikinshi cikin kuka tace "yaya Salman me yasa, me yasa nake jin haka? wallahi ji nake na tsani 'yar uwata?
"
Kai ya girgiza mata ya k'ara janyota ya rumgume yana cewa "shhhh, kiyi shiru kinji ya wuce ba zan sake ba"
Cewa tayi "yaya Salman ba wai na hana ka k'ara aure bane, ni kawai bana so ne ka auri kowace mace, ina ji da ina da iko a kanka to dana hana ka auren kowace mace a duniya, yafi muyi zaman mu haka koda ma za kayi ta duka na wallahi ba zan gaji ba."
Ji yayi duk ya k'ara jin haushin kanshi in dai har tana jin haka a kanshi, to miye zaisa ba zai zauna da ita ba ya kuma k'ara sonta fiye da yanda ita take sonshi.