← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 49

Sashe 31

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read

Bai bar latsa kumatunta ba yace "Ummi na barki ki koma makaranta ne saboda tabbacin da nake da akan ki, na san zaki kula da kanki sannan zaki karemin mutunci na dama mutuncinki."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon cikin idonshi tace "insha Allah yayana, ba zan tab'a baka kunya ba, sannan ba zanyi abinda zai shafi mutuncin ku ba, zanyi iya bakin k'ok'arina wajen ganin na kare maku hakk'inku da yake kaina musamman ma kai."
Murmushin jin dad'i yayi yace "me yasa musamman ma ni?"
K'asa tayi da idonta cikin jin kunya tace "saboda kai mijina ne." tana fad'a ta k'arasa shigewa d'aki tana dariya, Salman ma haka d'aki ya shiga yana jin wani sanyi na ratsashi yana ji ina ma ace Ummi ta fad'a mashi kalmar so a matsayin godiyar abinda ya mata.

Tun asuba Ummi da tayi sallah bata kwanta ba, tana gama had'a abinda kari ta d'an gyara abinda zata gyara a d'akinta da falo dama cuisine, tana kammalawa ta shiga wanka tana fitowa tsaf ta shirya cikin tenue d'inta.

Jakarta ta d'auko da hijab da nik'ab ta fito falo ta ajesu saman kujera sannan ta nufi d'akin Salman dan ta tashe shi, da sallama ta shiga amma shiru bai amsa ba alamar bacci yake, saida ta k'arasa har gabanshi ta k'ura mashi ido tana kallo yana baccinshi cikin kwanciyar hankali.

Rumgume hannayenta tayi a bayanta a hankali tace "ina sonka yaya Salman, sai dai ba zan iya fad'a maka ba, dan na san kai baka sona kuma ba zaka soni ba, amma zan ci gaba da jiran lokaci na san zai zo."
Lek'a fuskarshi tayi taga sosai yake baccinshi dan haka ta sunkuya daf da k'eyarshi ta sumbata, mik'ewa tayi tare da zura hannunta ta rufe hancinshi, da sauri ya juyo da kanshi yana bud'a idonshi yana ganin Ummi ya tashi zaune yana ci gaba da kallonta, murmushi kawai take masa kafin yace,
"Wannnan kuma wane irin tayar da mutum daga bacci ne?"
D'aga kafad'u tayi tare da d'aga gira sama alamar ba magana, saukowa yayi daga kan gadon yana fad'in "saina ji kamar an sumbace ni a kaina ko?"
Bud'e baki tayi cike da mamaki, lokaci d'aya kuma tayi k'asa da kanta tana wuru wuru da ido, gaf da ita ya matso yace "kece ko, ko dai akwai abinda kike b'oyewa ne ban sani ba?"
D'ago ido tayi suka kalli juna, ja tayi da baya tana fad'in "haba dai sumbata fa? sai kace wani jariri."
Toilet ya nufa yana fad'in "banyi mamaki ba dan kince haka, amma ki sani wani lokacin ma miji yafi jariri buk'atar kulawa."
Kallonshi tayi tace "to, ni dai na san ana cewa namiji kamar k'aramin yaro ne, duk in da kayi dashi can zaiyi."
Tsaye yayi yana kallonta kafin yace "kuma ke kin yarda da abinda aka fad'a d'in?"
Murmushi tayi tace "me zai hana ko, tunda mune ke jan ragamar."
Ganin ya tun karota yasa tayi saurin ja da baya tana fad'in "dan Allah ni dai kaje ka shirya kar nayi late a zuwan farko."
Sai lokacin ya lura da kayan dake jikinta dan haka yace "oh, hakane fa, ok ki bani 5 minute ina zuwa."
Kallon agogon dake gefe gadon tayi tace "ah bon, 5 minute?

Ok je t'atend."
Ciki ya shige ita kuma ta dawo falo ta zauna jiranshi, kallon agogo take lokaci na tafiya amma Salman shiru bai fito ba, ido Ummi ta fiddo tare da mik'ewa tsaye tana dafe da k'irjinta ganin 07:45, kukan shagwab'a ta saka tana fad'in,
"Shikenan zuwan farko zan fara da late."
Hijabinta ta saka ta goya jakarta ta d'aura nik'ab, d'akin Salman ta nufa sai kuma suka ci karo da juna, ido ya fiddo waje yana k'are mata kallo sama da k'asa kafin ya nunata da hannu yace "ke kuma wannan shiga haka bak'a k'irin kamar wata 'yar wuta."
Turo baki tayi duk da baya gani sannan tace "yaya Salman ka dubi lokaci fa ya wuce, wallahi nayi retard."
Lokaci ya duba ya k'ara zaro ido yana fad'in "kai kai kai, lallai kam, to wuce muje ina fatan dai kin karya?"
"Ni ban karya ba, kawai idan naje naci wani abu."
Wucewa sukayi bayan ta rufe d'akin, tunda suka kama hanya tayi shiru tana kallon gari, Salman ne ya kalleta yace "ina fatan dai ba zaki cire nik'ab d'innan ba idan kinje can?"
"Haba yaya Salman dole zan cire mana dan nasha iska, lokacin zafi ne gashi yanzu ba'a ruwa sosai."
Hararanta yayi yace "bana so, karki bud'e fuskarki kowa ya gani."
"Amma yaya Salman akwai takura fa, kai baka san nik'ab ba wallahi tana hana mutum kyakyawan shed'a."
Kallonta yayi irin ba wasanan yace "wallahi idan naji labarin kin cireta, to daga ranar bake ba k'ara komawa makaranta."
Cikin shagwab'a tace "to yayana idan zan ci abinci kuma fa?"
"To na yarda ki d'aga idan zaki ci abinci, amma da kin ida ki mayar."
Hararan gefen ido ta watsa masa a ranta tace "sai kace wani sona yake da yake takura min haka"
Kallonshi tayi tace "wai yaya Salman ta yaya ka sama min gurbin karatu anan ne cikin sauri haka?"
Ba tare daya kalleta ba yace "to miye na wahala a ciki, dama anan kike karatu kuma sun baki gurbi in da zaki ci gaba, kawai baki zo da wuri bane har anyi karatun wata biyu babu ke."
Cikin tsoro Ummi tace "to yanzu idan suka tambayeni ya zance masu?"
"Na gama da wannan ma, dan na fad'a masu kinyi aure kuma yanzu ba kida lafiya."
Wani kallo ta masa tace "to me kace masu yake damuna?"
Wani kallon raini ya mata yace "na fad'a masu kina fama da laulayi ne."
A firgice ta kalleshi tace "laulayi, na ciki ko na me?"
"Ke wanne kika sani?"
Kallon gabanta tayi tace "na san na ciki."
Shima ba tare daya kalleta ba yace "to shi nake nufi."
Wani lallausan murmushi tayi tare da dafe cikin tace "wai ciki, Ummi da ciki, babbar magana."
Kallonta yayi yace "kina sonshi kenan?"
"Ina so sosai, Allah ya nuna min na samu nima."
Kallon ba kida hankali ya mata yace "keda ko hanyar daya bi baki bi ba, kuma a hakan kike neman shi."
Bata kalleshi ba tace "to miye a ciki? ai abun rabone kura ta haifi akuya."
Kallonta yayi yace "lallai kam, amma ki sani wanna kura za tasha dukan tsiya idan ta haifi akuya."
"Lallai kam, watak'ila kuma ba zata sha ba." fad'ar haka yayi daidai da zuwansu ecole d'in, bud'a k'ofar tayi zata fita tace "sai anjima."
"Idan kun tashi ki kira ni." ya fad'a yana kallonta, har zata fita ta tsaya tare da tara masa hannu tace "kud'in abinci na."
Hannu yasa aljihu ya fito da kud'i yana tambayar ta "nawa zan baki?kin san ni ba d'a gareni ba bare na san nawa ake bayarwa, kuma ma ke har wani kud'i za'a baki da girmanki."
"To ina girman yake? har yanzu fa ban wuce jaririya ba."
Kallonta yayi sosai yace "a hakan, uwar wasu kakar wasu?"
Cikin shagwab'a tace "nifa yarinya ce, har yanzu a wanke nake babu datti."
"Allah ya shirya min ke 'yan matana, ni fad'a min nawa zan baki."
Dariya tayi tace "ameen yaya Salman, kawai ka kimanta sai ka bani."
Kafin su ankara suka ji k'arar k'araurawa (sonner) lokacin shiga aji yayi.

Cikin hanzari tace "kawai ka lissafa nawa ake baka da kana kamar ni."
"Ni ai ina kamar ki kud'in makaranta ma ni na biyawa kaina."
Cike da k'aguwa Ummi tace "to kawai ka ban 1000f ta isheni."
Dubawa yayi sai dai babu wacce ta buk'ata, dan haka ya bata 5000f tana karb'a ta fita tana fad'in "zan aje maka canjinka, sai kazo."
Kallonta yayi sai gudu take har ta shige ciki, kai ya girgiza yaja motar yana fad'in "kaji gudun da take kamar yarinya, ba zata yi hankali ba wannan har saina saita ta."
Yaji dad'i sosai ganin yanda kayan suka mata d'as da ita, gashi duk sun rufe jikinta sai idanunta kawai da hannayenta ne a waje, dan takalman data saka ma k'afa ciki ne maras tudu(valerine) bak'ak'e.
```SAM```
11/03/2019
17:51 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*HASBUNALLAH WANI'IMAL WAKIL*
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Su Jawahir sunyi farin ciki sosai ganin Ummi a makaranta ba zato ba tsammani, haka suka kasance tare har lokacin tashi yayi Ummi ta kira Salman yazo ya d'auketa.

Sosai su Jawahir suka birge Ummi ganinsu da tayi kowace da d'an k'aramin cikinta tana turawa, babban abinda yafi shiga ranta shine, ganin yanda suka canja lokaci d'aya duk sun canja abincin cinsu, abinda waccen take ci yanzu bata ko san k'amshinsa, haka abinda wata bata ci a da yanzu kuma tana cinshi sosai, wannan canjin ya birge Ummi sosai.
```ALLAH YA KAWO MAI ALBARKA```
Suna shiga gida ta cire nik'ab da hijab da jakarta ta yab'a akan kujerar falo ita kuma tayi ciki, Salman kam ruwa ya d'auko a fridge ya zauna yana sha, ya jima zauna yana jiran ta fito ta fad'a mashi abinda zata ci dan ya siyo mata amma shiru, mik'ewa yayi ya nufi d'akin, k'ofar kawai ya bud'a ba tare daya shiga ba.
Chapter 31 · 0% Book details