← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 49

Sashe 32

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Da k'yar ya had'e wasu yawu da suka tarar masa sannan ya kau da kansa gefe yana satar kallonta yana tambayarta "amm, dama na zone naji abinda zaki ci na siyo maki?"
Ummi dake ci gaba da shafa manta d'aure da d'an k'aramin towel d'in da ko cinya bai k'arasa rufe mata ba, sannan duk ta barbaza manyan kitsonta a bayanta ya kwanta, cike da karsashi tace masa,
"A'a yaya Salman ina zuwa yanzu saina dafa mana abinda zamu ci, saurin da nake kenan dama."
Cikin satar kallonta yace "kefa yanzu kika dawo kina buk'atar hutu, kawai ki fad'amin me zaki ci."
Juyowa tayi ta nufi wadrob ta bud'a tana duba kayan da zata d'auka tana fad'in "a'a yaya Salman zan dafa da kaina, a cikin kwana shida na karatu, kwana hud'u duk zan dinga tasowa k'arfe 13:30 , kaga idan nace zaka dinga siyomin abinci ai ban kyauta ba, dan haka ka barshi yanzu zan fito na d'ora mana yafi ace munyi latin cin abinci amma ba siyowa ba, kuma ma naga ai daga ni sai kaine a gidan."
Murmushi yayi tare da kallonta yace "sai kin fito."
Sai lokacin ta kalleshi taga yanata wani sunkuye kai, a hankali ta tako tazo gabanshi ta tsaya, hannunshi ta kama kamar yaro ta d'ora a gefen fuskarta tace "kace Allah ya min albarka, kamar yanda Abba yake min."
Duburburcewa yayi ya rasa me zai fad'a, gaba d'aya ya rasa network d'inshi take idonshi suka sauya suka fara canja launi, Ummi kam tsoro ne ya rufeta dan haka taja da baya tana fad'in "ina zuwa yanzu."
Kamar zai tashi sama haka ya fita daga d'akin ya shiga nashi, gado ya fad'a ruf da ciki yana taro abinda k'wak'walwarshi ta gane mashi hakan yasa kuma ciwonshi ya k'ara tunzura yana dad'a gaba.

Maganinshi ya d'auko ya b'alla yasha tare da mai sa bacci yasha, lokaci k'alilan bacci yayi gaba dashi ba dan ciwon ya bari ba.

Ummi na fitowa cuisine ta shiga ta fara had'a abincin rana mai sauk'in sarafawa, 14:40 ta kammala d'akin Salman ta shiga ta tashe shi daga bacci, yana fitowa tare suka ci abinci suna idawa ta d'auke kwanukan ta mayar cuisine ta wanke ta goge duk inda ta b'ata.

Tana fitowa Salman ta gani da jakar makarantar ta ya fiddo litattafanta yana dubawa, k'arasowa tayi tana kallonshi ta zauna, kallonta yayi yace "kin gane darasin da aka maki yau?"
Gyara zama tayi tace " taya zan gane da zuwa d'aya, dole ina buk'atar na samu mai koyamin idan na dawo gida."
Cike da raha Salman yace "to in hakane ki dinga biyana duk
wata saina dinga koya maki."
Matsowa tayi kusa dashi tace "da gaske yaya Salman? to ka fad'i nawa kake so na baka?"
Cike da fara'a yace " ki fad'a da kanki me zaki iya bayarwa duk wata."
"Duk wata?" ta tambayeshi, kai ya d'aga mata alamar Eh, dan haka tace "ok, to ka koyamin, ni kuma duk wata zan biyaka ta hanyar haifa maka kyakyawan yaro ko yarinya masu kama da kai."
Salman bai san lokacin daya fashe da dariya ba yana fad'in "yara dai, duk wata? ba kida dama Abu."
Turo baki tayi gaba cike da shagwab'a tace "Eh mana, miye a ciki?"
Da k'yar ya tsagaita da dariyar yana kallonta yace "to amma me yasa sai masu kama dani, me yasa ba kya san ki haifi masu kama dake?"
K'asa tayi da kanta tace "to ai ka fini kyau ne shi yasa."
Ya mutsa fuska yayi yace "Ummi waya fad'a maki ba kya da kyau?"
Kallon idonshi tayi tace "kasha fad'amin haka sau da dama, har wani lokaci ma ka kan kwatantani da mage ko aljana."
K'asa yayi da kanshi dan bai tab'a tunanin abin yana cikin ranta ba har yanzu, kallonta yayi yace "Abu karki damu da wannan, kawai ina fad'a ne amma ba wai yana nufin ke mummuna bace, kina da abinda ba kowa keda shi ba."
Hararan wasa ta masa tace "hmm, kamar me kenan?"
Kallonta yayi sosai kafin yace "kamar idonki masu abin al'ajabi, wanda basa kalluwa ga ragon namiji bare kuma mace, sannan kina da dinple wanda yake k'ara maki kyau idan kina dariya ko murmushi ke har ma da kuka idan kina yi."
Wai dad'i kashe Ummi, yau Salman d'inta ne ke yabanta haka, farin ciki ne ya k'umeta yasa tayi fari da ido cikin kissa tace "hmm, to ni dai naji muyi karatun."
*A kwana a tashi* lokaci na tafiya al'amura na faruwa da dama daga rayuwar Salman da Ummi, tun lokacin Salman kema Ummi lesson ba dare ba rana in dai har yana gida, shak'uwa sosai ta k'ara shiga tsakaninsu a wani b'angaren kuma suna k'ara zurfafa soyayyar da sukewa junansu.
*Sati uku* da fara karatunta Salman ya sake tafiya Cotonou, da k'yar ya iya kwana goma a cikin sati biyun daya d'iba zaiyi, dan kuwa babu abinda yake daya wuce tunanin Ummi da kewarta.

Haka ma a wajen Ummi, dan kuwa ko abinci ta daina ci sosai dan yanzu ta saba da cin abinci tare da Salman, kafin ya tafi saida ya d'auko Islam tare da Momy (
autar su Salman) ya kawosu dan su tayata bacci, hakanne yake rage mata damuwa da tunani da kuma k'arfafa gwiwar da Salman yake mata akan karatu duk lokacin da sukayi waya.

Tunda safe Salman ya kan kirata yaji ya suka tashi, kasancewar yana da jadawalin lokacin karatunta (emploi du temps) yasa tana fitowa daga aji kiran Salman zai shigo wayarta, da dare haka zasu sha hira abinsu har dama karatu yana k'ara kwatanta mata a waya.
*Ranar* da Salman ya dawo, ya dawo da k'udirin sauke hakk'in dake kanshi, yayi niyyar kusantar Ummi ta hanyar data dace bawai ko ta halin yaya ba.

Rashin sa'a a ranar daya zo, a ranar bak'on Ummi yazo (period), bayan wannan kuma gashi suna shirin shiga satin jarabawa, hakan yasa Ummi ta zama busy sosai bata da lokacin komai har lokacin kanta, hak'uri kawai Salman yayi amma ba dan haka yaso ba.
*Litinin* Ummi suka shiga zana jarabawa, kwana uku sukayi kuma a kwana ukun nan Ummi ko abinci bata san ci sai Salman ya matsa mata lamba sannan, hasali ma ba ita ke dafa abincin ba siyowa Salman keyi, ririta ta kawai yake dan shirin shi shine suna gama jarabawa tofa shima dole ya shiga hq dan tashi jarabawar.
*A kullum d'an Adam na nashi ne, Allah ma yana nashi, mutum baya da ikon tsarawa kansa rayuwa sai yanda Allah ya tsara masa* su Ummi na fitowa daga aji aka fara ruwa kamar da bakin k'warya, zuwan Salman dan ya d'auketa yasa Ummi fitowa daga mafakarta ta k'arasa in da yake, ruwa sun jik'ata sosai hakan yasa tana shiga mota ta cire hijab d'inta da jakarta, suna zuwa gida ma haka suka tsaya suna kallon juna ganin yanda ruwan ke sauka da k'arfi.

Cike da shagwab'a Ummi tace "to yaya Salman kaine namiji kuma mai hakk'in kula dani, dan haka ka rufeni saimu shige ciki."
Hararanta Salman yayi yace "ahan, kenan yau kin tuna haka ko?"
Turo baki tayi gaba tace "to ni dai wallahi idan na shiga ruwan nan zan iya mura, dama gashi na riga dana jik'e."
"To shikenan, ki shirya zan fita yanzu kema saiki fito."
Fita yayi ya zagaya ma zauninta ya kamo hannayenta ta fito, rumgumota yayi a jikinshi ya matseta a hankali ya d'agata ya d'ora k'afafunta akan nashi sannan ya d'auko hijab d'inta ya masu runfa dashi, a hankali ya fara takawa saboda tana bisa k'afafunshi ne kamar ya d'auketa ne, idon Ummi na kan k'irjin Salman data d'ora hannayenta ta kasa had'a ido da shi, shi kam fuskarta kawai yake kallo tare da k'ara matse kunkuminta da duka hannayenshi biyu.

Suna shiga falo ta zame jikinta daga nashi, sai dai duk da haka saida suka jik'e da ruwa take jikin Ummi ya fara rawar d'ari, kallonta Salman yayi lokacin da yake cire takalmanshi k'afa ciki, saida ya gama cirewa ya d'ago yana b'alle ma b'allan rigarshi yace,
"Ya dai malama?"
Bud'ar baki tayi zatayi magana ji kake "hatshimmm." ta b'arzo wata atshiwa, ja baya Salman yayi yana fad'in "kai, haba ke kuwa atshiwa ba sanarwa kawai saiki fyace ni."
Wata maganar taje tayi amma ina sai wata atshiwar tare da fitowar majina a hancinta, ajiyar zuciya Salman ya sauke cike da tausayawa ya matso kusa da ita yana kallon fuskarta, kallabinta ya cire ya jefar a kujera haka ma ribom (chouchou) d'inta take gashinta marar kitso ya zube a bayanta wanda ya jik'e da ruwa sai k'amshin man kai yake *(BLACK QUEEN {COCONUT OIL} )*.

A hankali ya had'ata da k'irjinshi ya zura hannayenshi a bayanta ya zuge zif d'in rigarta, tana kallonshi har ya rabata da rigarta yayi saura bras d'inta fara, sunkuyawa yayi yana shirin zame wandonta daga jikinta tayi saurin ja da baya tana fad'in "a'a ya isa haka....atshimm." ta k'arasa maganar tana k'ara atshaweshi.

Tissue ya ciro a aljihunshi ya matso kusanta yasa ya goge mata majina har da cewa "fyato" kallonshi tayi sai dai ba tayi magana saboda ya rufe mata hanci da tissue, bud'e mata ido yayi ya sake cewa "fyato"
Tsaf Ummi ta fyato ya goge mata, juyawa tayi ta bud'e d'akinta ta shige tana ci gaba da atshiwar, shi kam binta yayi da kallo kafin shi ma ya nufi nashi d'akin.

Zuwa dare Ummi ta galabaita sosai dan mura bata mata da dad'i dama in dai ta damk'eta abinka ga jar fata duk ta fita hayyacinta ta sukurkurce, tun doguwar rigar data saka dawowarta har yanzu ita ce a jikinta, kanta duk ya yamutse saboda kwanci da take hancinta har yayi ja saboda goge majina, idonta banda ruwa ba abinda sukeyi ko magana bata ji sosai dan kunnuwanta sun d'ume, haka gaba d'aya mak'oshinta ciwo yake ga bala'in ciwon kai, duk ta rikita Salman da kukan shagwab'ar da take bata tab'a tunanin zai damu haka ba, amma data ga ya nuna damuwa a fili saita k'ara narkewa tana zuba shagwab'arta.
Chapter 32 · 0% Book details