Sashe 16
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read
Kwance ta koma tare da d'aukar pillow dake gefenta ta rumgume, a hankali take tariyar rayuwarta a gidan Salman da tayi.
_Tambayoyi ne ta jero ma kanta" miyasa nake damuwa, miyasa nake jin haushin shi dana Nuseiba, miyasa nake jin zafi a zuciyata, miyasa nake so naji muryarsa, kuma miyasa na kasa kiranshi?"_
```in bata amsa, koko cikin ku akwai wanda zata bata?```
_Ma ch
rie ta Hakima fito mucashe, lokaci ya kusa yan bak'in cikin Salman saidai a mutu
05/03/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
_My seeya fatan alkairi da godiya tare da addu'ar ya fiyar Ubangiji a bisa kurakuran da ki kayi, daidai kuma Allah ya baki ladar fad'akarwa da ki kayi, *BAMU DACE DA JUNA BA,* darasi nishad'antarwa tare da ilimi da fad'akarwa ne a cikin shi._
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*Page*
Tunda safe haka Ummi ta tashi sukuku jiki babu k'wari, Jawahir ce ta fad'ama Khamis halin da take ciki, kiranta yayi tana zuwa da kanshi ya zuba mata abinci a plate ya aje mata tare da fad'in" maza cinye ki bani plate d'in"
Kallonshi tayi tace" yaya Khamis ko zanci ba zan iya cinye wannan ba" yanda ya had'e rai yace" Ummi ina wasa dake?" kai ta girgiza tace" kayi hak'uri yaya Khamis wallahi yamin yawa"
"Ke, ina wasa dake ne, za kici ko saina takaki?" tsawar daya mata ce tasa tayi saurin jan plate d'in a gabanta ta fara kai loma baki, Jawahir ma 'yan cikinta ne suka kad'a, haka nima saida na saki alk'alamin.
Tana ci tana kuka tana rok'onshi ya isa haka, amma ya tsareta saida ta cinyeshi duka ta bashi plate d'in, tunda uwar Ummi ta haifeta bata tab'a cin abinci mai yawan haka, shiyasa Khamis na fita Ummi ta fara tsula amai, abin ya d'aga hankalin Jawahir dan da farko tayi tunanin idan ta amaye abinci zata daina, amma sai taci gaba da shek'ashi.
Cikin tashin hankali ta fara kiran Khamis ta fad'a mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali yace da ita "gani nan zuwa saimu kaita asibiti"
suna jiranshi Salman ya kiran Jawahir dan tunda ya tashi bai fita ba, gab'a d'aya hankalinshi ya koma gida, hakan yasa ya kira iyaye maza da mata da kakannin amma saiya ji baibar kewa da damuwa na gidan ba, dole ya kira Jawahir ya tambayeta Ummi.
Tana d'auka cikin damuwa tace "assalama alaikum, ina kwana yaya Salman?" gabanshi yaji ya fad'i, da k'yar ya daure yace "lafiya lau, kun tashi lafiya?"
Kamar zata fashe da kuka murya na rawa tace "yaya Salman da sauk'i dai, kaga Ummi nan tana ta amai wallahi, nifa na fara jin tsoro" cikin d'aga sauti yace "amai kuma, miyasa meta to?"
Cikin kuka tace "yaya Salman daga taci abinci fa shine take amai "innalillahi wa'inna illaihir raju'un, kinga bata wayar" ya fad'a tare da nuna tsantsar damuwarshi a fili.
Mik'a mata wayar tayi, wata harara ta wurga mata tare da kau da kai, maida wayar tayi a kunne cikin sanyin murya tace "yaya tak'i karbar wayar" abun mamaki na d'auka Salman zaiji haushine, amma sai naji yace "Jawahir karki min k'arya, ki fad'amin abinda ke damunta?"
"Yaya Salman nima bansan miyake damunta ba, amma dai jiya ta fad'amin wani abu wanda nake tunanin kaine silar shigarta wannan halin" cikin rashin fahimta yace "bangane ni nasa taba?"
"E yaya Salman amma kayi hak'uri nima zato ne nake, amma banda tabbaci" cikin jin haushi Salman yace "naji ni fad'amin me ta fad'a maki?"
Duk da tana d'ard'ar dashi haka ta daure ta fad'a masa duk abinda Ummi ta fad'a mata jiya, dariya yayi yace "Jawahir lallai yarinya ce ke, waya fad'a maki ana kishin wanda ba'a so?"
Saida ta sauke ajiyar zuciya tace "yaya Salman ai macen kenan, tsamar dake tsakaninku ba zata hana zuciyoyinku fallasa sirrin dake cikin taba, ko bata sonka zata iya kishinka saboda akwai aure tsakaninku, kamar yanda da zaka ganta da wani namiji za kaji zafi a zuciyarka, amma idan aka fahimci hakan zaka iya wayancewa ta hanyar cewa kana san kare martabar aurenka ne dake kanta, kaga kenan dan tayi kishinka ba abun mamaki bane."
Shiru yayi yana tunanin abinda ta fad'a, murmushi yayi kamar yana gabanta yace "Jawahir ban tab'a jin alamun haka a raina ba, ko zanyi soyayya zanyine da wata daban amma ba Ummi ba, yarinyar da idan naganta sai gabana ya fad'i saboda tunanin abinda zata min musammam idan ina cikin mutane"
Dariya tayi cike da jin k'arfin gwiwa tace "Yaya Salman ai fad'uwar gaba alamune na so" dariya yayi yace " ke Jawahir banasan sharri, ke har kinsan alamomin so?"
Dariya tace "na san wasu yaya Salman wanda nake ji a duk lokacin da naga yaya Khamis" cewa yayi "to fad'amin uku daga ciki, kuma idan ki kayi ba daidai ba to idan nadawo dole kisha rank'wasa a kai"
Hannu ta d'ora a kanta dan b
zata manta rank'wasan daya tab'a mata ba har saida tayi ciwon kai, cewa tayi " yaya Salman duk lokacin da kaji gabanka ya yanke ya fad'i a lokacin da gaka wata 'ya mace, to alamune na zuk'atanku suna shirin k'ulla wata alak'a koda ku baku shirya hakan ba.
"Sannan lokacin da kaji komai na wata 'ya mace yana burgeka, komai yana nufin dariyarta, murmushinta, fara'arta, kai dama kukanta to shima akwai yiwuwar ka kamu da sonta ko kana shirin kamuwa."
"Yaya Salman akwai jin tausayinta duk lokacin da wani abu ya sameta na rashin jin dad'i, haka kuma akwai son ganinta a cikin farin ciki tare da mata fatan farin ciki mai d'orewa, son jin sautin muryarta a koda yaushe, son ganinta a kusa da kai a kullum."
"Yaya Salman duk lokacin da kayi nesa da ita tunaninta zai iya hanaka sukuni, zaka kasa komai burinka bai wuce ka dawo ka ganta ba, zaka ji kewarta na yawan damunka kana buk'atar kasancewa da ita, sannan yaya Salman duk wacce kake so za kaga murmushin da kake mata ma na dabanne, haka kallon da kukewa junanku ma zuk'atanku ne kad'ai zasu iya fassarashi, don ko mai kallonku ba zai iya fassara maku shi ba."
"Ke" ya daka mata tsawa yana fad'in" nawa na tambayeki ni uku fa nace, waike sarauniyar soyayya ko?" kai ta girgiza alamar a'a, tace " yaya nadai fad'a maka abinda na sani ne kawai, amma ina so ka sani kai da Ummi koda baku son junanku, to ku sani akwai jinin 'yan uwantaka da yake yawo a sassan jikinku wanda baku isa ku cireshi ba, ko babu so a tsakaninku akwai k'auna, yaya Salman abune mai sauk'i samun masoyi, amma samun wanda yake k'aunarka da gaskiya shine mai wahala, mafiyawancin soyayya tana farawane daga k'iyayya sannan ta koma so wannan shine."
Kashe wayar yayi ba tare da sunyi sallama ba, maida kallonta tayi ga Ummi dake kwance tana bacci, Khamis na zuwa Ummi tace taji sauk'i, dan babu abinda ta tsana kamar shan magani da allura, dole suka k'yaleta da sukaga jikin yayi sauk'i ta daina aman.
_Wato dai 'yarta bakin Salman baki son shan magani sai abun dad'i_
05/03/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*MEELAT*_(my meelat)_
*HEENAT*_(my heenat)_
*CHOUKRA*_(habibaty)_
*FATIMA*_(mom dady)_
*HALIMA*_(kakale ta)_
*SAFIYA*_(ma ch
rie)_
*AZEEMA*_(k'awata)_
*RAMATOU*_(rammess)_
*MAMAN LABYB*_(momy na)_
*MOMYN SULTAN*_(aunty)_
*MOMYN DEEJA*_(ma belle)_
*HAWA JAMIL*_(aunty na)_
*HAKEEMA*_(ma ch
rie)_
```WANNAN PAGE SADAUKARWA CE GAREKU, DAN HAKA KUYI YANDA KUKE SO DA ITA TAKU CE KYAUTACE DAGA GARENI```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Yanda Salman yaga rana haka yaga dare ba tare daya rintsa ba, kalaman Jawahir sun gigita tunaninshi sosai ya kasa fayyace gaskiya da k'arya, indai har fad'uwar gaba yana d'aya daga cikin alamun so, to kenan tun Ummi na matashiya yake sonta, domin ko duk lokacin daya ganta sai gabanshi ya fad'i sannan baya jurar kallon idanunta, suna sashi yaji wani yanayi a tare dashi, hakan ma yasa yake kiranta da mai idon aljanu kona mage wani lokacin.
Ya yanke shawarar komawa gida jibi, dan haka ya ciro ticket haka ya k'agu safiya ta waye ko ya kama hanyar gida,yayi niyyar bankad'o gaskiyar abinda Jawahir ta fad'a masa zaiyi k'ok'arin gano gaskiya ta hanyar lalubo kishin Ummi sannan yasan dalilin kishin nata.
08:00 na safe suka kamo hanyar zuwa niamey, banda kallon pic d'in Ummi babu abinda yake, ko abinci baisa a bakinshi har suka sauka, duk da gobe zai wuce amma yayi niyyar bazai fad'ama kowa ba yana so ya masu bazata, sannan yaga yanda Ummi zatayi.
Bayan ya huta sosai abu d'aya yake da buk'ata yayi wato bacci, amma ina ya kasa samuwa duk da cewar baiyi bacci daren jiya ba, wayarshi ya d'auka yana so ya kira Ummi amma yana tuna ya fad'i bazai k'ara kiranta ba, haka ya daure ya kirata amma abun haushin wayar kashe, haka ya k'urama pic d'inta ido yana kallo har bacci b'arawo ya d'aukeshi.
*Washe gari* da safe Ummi ce ta fito farfajiyar gidan dan tasha iska, sanye take da doguwar riga mai colour ja da bak'i da fari, sama a matse sai k'asa daya bud'e ba tada dan kwalli dan haka ta d'ora na abaya ba'ka, zaune tayi akan 'yar gajerar katangar da aka kewaye rabin harabar gidan da ita, jingina bayanta tayi ta rumgume hannayenta a k'irji tayi shiru tana kallon 'yar k'aramar bishiyar mangaro, a hankali ta tuna ranar da suka fito tare da Salman ta rakoshi zai fita, da kuma ranar da ta fad'i saboda jiri ya d'auketa sannan ya kawo mata madara tasha.