← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 49

Sashe 26

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Yana zuwa Khamis ya fito suka wuce, a hanya ne Salman ne ya kalli Khamis yace "Khamis dan Allah ka taimaka min, ka sanar dasu Abba ina neman auren Nuseiba wallahi bada wasa nake ba."
Cike da kosawa Khamis yace "Salman na fad'a maka ka daina sani cikin maganar nan, idan fa ka fad'a babu wanda zai hana ka auren Nuseiba amma ka tsaya ni kana takura min."
Cikin damuwa Salman yace "me yasa ba zaka gane ba Khamis? ina cikin wani hali kuma ina buk'atar taimako wallahi bana so na ci gaba da zama da yarinyar nan a gidan nan mu kad'ai, in ba haka ba ban san mi zai biyo baya ba."
"Khamis yau saura kad'an na aikata abun kunya, saura kad'an na jawa kaina raini, saura kad'an na aikata abinda zai dameni a gaba, saura k'iris na kusance ta."
Cikin raini Khamis yace "wai raini, kai a ganinka wannan ne raini?"
"To bari kaji, wallahi ko yanzu in kayi wasa to ina baka tabbacin cewa abinda ya faru a baya shine zai sake faruwa a yanzu, dan tabbas sai kaga likita."
"Cousin, kayi abinda ya dace da kai kafin ka jefa rayuwarka cikin matsala, kana da mata dan haka banga dalilin da zaisa ka bari ciwo ya illata ka ba."
"Malam ka sauke girman kai da izza ka kwashi albarkatun dake tattare da mace, Ummi yarinya ce sosai idan aka had'ata da kai, zaka iya tafiyar da ita yanda ranka yake so domin kuwa k'wace goriba a hannun kuturu abune mai sauk'i."
Girgiza kai yayi yana kallon gabanshi yace "baka san wacece wannan yarinyar ba shiyasa, ka san ma mi tace min?"
"A'a" kallonshi yayi yace "tace ba zata bani kanta ba saboda ban dace ba"
"Hahahaha, to ai gaskiya ta fad'a saboda yanda kake cin magani haka wacece zata yarda ta baka kanta? ai su mata saida rarrashi da lallami sannan idan kayi sa'a su baka ka lasa."
Cike da mamaki yace "bayan rarrashin ma sai kayi sa'a?"
Dariya Khamis yayi yace "sosai kuwa, tunda kayan marmarin suna gurin su."
Kai ya girgiza yace "wannan k'ask'anci ai yayi yawa, bayan ma jikina da zata gani saina tsaya ina lallab'ata bayan matata ce sadaki na biya, kuma a haka ace wai sai nayi sa'a haba."
Kallonshi Khamis yayi yace "kai ma ai jikinta zaka gani, ko kuwa?"
Tabe baki yayi bai sake magana ba har suka kai gidan, da sallama suka shiga sun samu su Mama duka a tsakar gida suna 'yan aikace aikace, gaisawa su kayi kafin suka zauna.

Mama ce ta fara kiran "Rumana, Rumana" daga cikin d'aki ta amsa da "iye"
"Ke ki kawo ruwa"
"To" ta fad'a a takaice, Salman kam takaici kawai yake wai ace mahaifiyar ki ta kira ki kice mata iye babu ladabi babu girmamawa, wannan shine dalilin da yasa baya san shiga harkarta ma.

Haka ta fito gantsar gantsar ta aje masu ruwa da wata doguwar rigarta ko d'an kwali babu a kanta, ko kallon ruwan Salman baiyi ba dan yanda yaga kanta a cunkushe yaji zuciyarshi ma na tashi, "ina kwana".

Ta fad'a tare da juyawa zata koma d'aki, cikin fad'a Salman yace "ke ina d'an kwalinki kike yawo haka?"
Cikin jin kunya tace "yana d'aki"
"Oho shine kike yawo haka? to in kika sake bari mu kayi ido biyu dake haka wallahi saina k'ona gashin nan"
Rumana kam dad'i ne ya kasheta dan wannan tsananin na yaya Salman shine yasa take sonshi, dan a tunaninta idan ta aureshi zata rik'eshi gam tsananin shi kuma zaisa ya d'auke kanshi daga wasu matan.

Tana shiga d'aki ya kalli Maman Nuseiba yace "Mama ina Nuseiba ne ko bata nan?"
Cewar Mama "tana d'aki kam kuma na san tana jinka, shiru dai tayi"
Shiru yayi har Khamis ya gama abinda ya kawoshi suka tashi zasu wuce, saida suka kai k'ofar gida Nuseiba ta fito tana fad'in "ina kwana yaya Salman?"
Juyowa yayi yana kallonta yace "ashe kina ciki kika yi banza dani?"
Wani fari tayi da ido mai kashe zuciya tace "lah yaya Salman ba haka bane, kawai dai ina so mu gaisa ne ba'a cikin mutane ba"
Shagala yayi da kallon bakinta daya sha pink d'in ja leb'e (in ji uncle d'i na), hira suka fara tab'awa suna dariya Khamis kam ya gama k'ulewa ganin yanda take wani fari da ido na kissa, haushi ne ya kamashi yace "kaga malam dan Allah wuce mu tafi, ke kuma wuce gida"
Saida ta harare shi ta k'asan ido tare da ji a ranta cewa yana mata bak'in ciki ne, ciki ta shiga su kuma suka wuce.

Tunawa da Salman yayi yaune ranar komawar Ummi asibiti yasa ya dawo gida suka shirya tare da Islam suka kama hanyar asibiti, suna zuwa suka nufi d'akin da zai sada su da wajen likitar data duba Ummi ranar.

Layin da suka gani yasa su tsayawa suna k'ara kallon mutanen dake wurin, Salman mota ya koma kafin layin ya rage, mutane na shiga kuma suna fitowa dan danan haka yasa layin ya ragu sosai, mutane uku suka rage su Ummi su shiga Salman na ganin an kusa kawowa garesu ya fito daga mota ya zo.

Suna haka wani kyakyawa kuma matashin likita ya fito daga wani d'aki kusa dasu, yana ganin Ummi ya washe baki tare da fad'in "lah mutuniyar kece kika dawo? a to bari na kai sak'on nan na dawo na rik'e ki dan na san yauma ba zaki tsaya ba."
Murmushi kawai ta masa shi kuma ya wuce d'aya d'akin, Salman kam kamar a tab'a shi ya fashe saboda cika, an d'an d'auki lokaci kafin Ummi ta mik'e zata shiga, cikin fushi Salman ya fizgo hijabinta yana fad'in "waye waccen?"
Saida ta kalleshi sama da k'asa tace "ban gane waye waccen ba?kai baga ko waye ba ko baka iya fahimtar kayan aikin mutane?"
"Kamar zai bigeta kuma dai ya tsaya tare da fad'in "ina tambayar ki kina tambayata, ki fad'a min miye tsakanin ki dashi?"
Ummi kam tuna Nuseiba tayi da irin haushi da k'uncin data shiga saboda su, dan haka tace masa "ayya ai ya taimaka min ne ranar da muka zo nan shi ya rik'e ni aka min d'inki da allura."
"Ya rik'e ki" wucewa tayi ta barshi nan, bin bayanta yayi Islam kam na zaune daga waje da k'yar Ummi ta mik'a k'afarta dan a cire mata zaren da aka mata d'inki, saida Salman ya matse ta ya tutsa kanta a cikin k'irjinshi sannan aka fara d'ebe mata.

Ana gamawa Ummi ta d'ago kanta fuskarta duk ta jik'e da hawaye da majina, Salman kam duk rigarshi ta jik'e sai kuma ta bashi tausayi haka aka gama masu suka kama hanyar gida.

Daidai *Maradi Store* yayi parking, Islam ya kalla dake baya yace "Islam muje ko."
Fita tayi shi kuma ya kalli Ummi yace "ki jira anan muna zuwa yanzu" har zai fita Ummi tace "ni kad'ai zan zauna, me yasa ba zamu je tare ba?"
A dak'ile yace "banga anfanin zuwanki ba, idan kuma kina da sak'o ki kawo na siyo maki?"
Ba tare data kalleshi ba tace "ina da amma dole sai in ni naje da kaina."
Bud'a murfin motar yayi yace "sai kiyi ta zama anan to"
Ta jima zaune kafin suka fito daga ciki, ledar hannunshi ya mik'a mata tana karb'a ta bud'e farin ciki ne ya bayyana a fuskarta ganinta kayan k'walam da mak'ulashe, bata tsaya b'ata lokaci ba ta d'auki wata chocolat ta fara sha, jefi jefi Salman ya kan kalleta yana mamakin yanda ta kasa masa godiya, amma Islam ma dake k'arama ta masa tun kafin su fito, ya san ba daga tarbiya bace kawai dai tsarinta ne haka, haka har suka isa gida.

Ko abincin rana Ummi bata ci ba saboda ciye ciye da tayi, da yamma ma kam suna zaune farfajiyar gida ita da Islam Jawahir ta shigo a hargitse, Ummi ce tace "ke kuma lafiya haka, daga ina kike kamar an koro ki?"
Saida ta zauna ta cire nik'ab da hijab tace "kedai bari wallahi, hadari ne a gari shiyasa nayi saurin k'arasowa karya riske ni a hanya"
Sai lokacin Ummi ta kalli sama tace "hadari fa, kinga muna nan sai a tashi duniya bamu sani ba."
Dariya Jawahir tayi tace "idan aka kawo gareku ai zaku sani" kafin Ummi tayi magana iska ya taso da k'arfi, dan haka suka koma ciki nan fa aka fara ruwa kamar da bakin k'warya dan dama an kwana biyu ba ayi ba.
21:00 aka d'auke ruwa ba jimawa kuma Salman da Khamis suka shigo gidan, Ummi ko kallon Salman ba tayi amma ta gaishe da Khamis, haka ta shirya Islam suka tafi tare da Jawahir, tunda Salman ya fita ya matsu ya dawo gidan dan sosai yaji haushin banzan da tayi da shi gaban mutane.

Yana dawo har cikin d'akinta ya shiga amma abun mamaki kwance take tana hawaye, tunani yayi ko dan Islam ta tafi ne, matsowa yayi cikin muryar fad'a yace "Ummi naga har yanzu ba kya neman zaman lafiya da ni, ke kinfi k'arfin ki gaishe ni ko?"
Zuciyarta a wuya take dama dan haka ta harareshi sama da k'asa tare da tsaki ta kau da kanta gefe, mamaki ne ya bayyana a fuskarshi cikin b'acin rai da zafin nama ya cabko hannunta yana fad'in,
"Wa kike harara, ni kike wa tsaki?"
Cikin muryar kuka da fitar hayyaci Ummi tace "ka sake ni mugu kawai azzalumi, wallahi sai Allah ya saka min kuma wallahi ka auri Nuseiba sai zaman gidan nan ya gagareta dan babu abinda zai hana ni ci mata uwa, mugu kawai kana fad'a wai ni nama k'aramta amma kuma shine zaka auri yarinyar dana bata shekara hud'u, dama ita kake so shi yasa zaka aure ta."
Sakinta Salman yayi dan yanzu kam ya fahimci abinda ke cikin zuciyarta ne ya fito fili, lallai har yanzu tana kishi da shi to amma me yasa.?
Chapter 26 · 0% Book details