← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 49

Sashe 13

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read

Suna shiga gidan suka fashe da k'ara ita da Jawahir suna ta tsalle kamar yara tsabar farin ciki, Khamis dai fita yayi ya barsu bayan ya had'a mata wayar ta ya bud'a mata WhatsApp,haka suka wuni Ummi nata bawa Jawahir labari irin muguntar da Salman ke yi mata ita dai Dariya kawai take, tare su kayi girkin dare suka kammala suka shirya Suna zauna anan Jawahir ta bawa Ummi numbobin k'awayensu da nasu Nadia nan fa aka hau charting k'arshe ma d'aki ta shige tare da maradarta tana kurb'a tabar Jawahir tana jiran mijinta ya dawo.
28/02/2019
17:02 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)
*Page*
Tunda Khamis ya dawo ya tambayi Jawahir ina Ummi, data fad'a masa tana d'aki wayar shi ya ciro ya turawa Salman numberta sannan ya shiga harkokin gabanshi.

Ummi hira kawai take da k'awayenta a groupe d'insu musamman RAYUWAR M
A YAU, tana jin dad'in hirar sosai dan duk ta k'aruwace a keyi, 23:30 ta wuce bak'uwar number ta shigo wayarta, dubawa tayi dan taga ko waye sak'one a rubuce kamar haka,
_"waya baki izinin bud'a WhatsApp, sannan mi kike har yanzu da kike en ligne?" take Ummi ta fahimci ko waye, amma tayi niyyar raina masa hankali dan haka ta maida masa ita ma tace" wanda ya baka izinin bud'awa a lokacin da ka bud'a, sannan abinda kake yi nima shi na keyi" bada jimawa ba ya maido mata yace" karki raina min wayo, ina hira ne da budurwata mai deb'emin kewa" dakewa tayi ta maida masa ita ma" kenan jirgi d'aya ya d'auko mu ni da kai, dan nima nayi kewar samari na ne shiyasa nake rage dare da su" wani irin takaici ne ya kama Salman dan yasan ta aika, maida mata yayi" ke bana san iskanci wallahi ki sauka ko kuma ranki ya b'ace" dariya Ummi tayi ta maida masa da"
" take ya maido mata yana fad'in" wa kike juyama bakin? wallahi ki kiyaye ni" dariya tayi t
koshi sannan ta maida masa" kaga malam dan Allah nifa matar aure ce ka kemin mad'e, idan mijina ya sanka to zai kashe ka, dan haka sai anjima" harta koma cikin groupe ya aiko da wani sak'on dubawa tayi taga yace" har haka mijin naki ke sonki dama?" maida mashi tayi da" sosai kam, yana sona fiye da ransa, nice mahad'in rayuwarshi" dariya yayi yace" to ko zan iya ganin photonki da na mijin naki?"cewa tayi" mi zai hana, amma karka ce mijin yafi matar kyau idan ka gani" kafin ya aiko ta dunk'ule photo kusan talatin ta aika masa wanda Jawahir ta tura mata d'azu, bud'a photunan yayi ya fara kallo, sak'onta ne ya sak
shigowa tace" idan ka fiddo ni a ciki zan maka kyauta" sai lokacin ya sak
duba photunan da kyau, babu inda take ita kad'ai duk ita da su Jawahir ne sai kuma k'annanta su Islam da Mubbashir, inda ya ganta tare da su Jawahir da Khairat Kwance akan gado tana tsakiyar su tayi dariya sosai hak'oranta sun bayyana ga kumatunta sun lotsa kamar ka saka k'wandala kuma ta zauna daram, babu ko d'igon Kwalli a fuskarta amma tayi kyau, shi ya aika mata yace" wacce tafi zama bak'a a ciki to ke ce ita, kuma banga mijin naki ba?" dariya ta aika masa tace" ka canka dai-dai, dan haka ka zo da kumatunka ka karb'i cadeaux d'inka, banda photon mijina" _tambayarta yayi" ban gane kumatuna ba? miyasa baki da photon mijinki?" maida mashi tayi" kaga nifa ina da abinyi , dole ne saina samu photonshi?nida nake ganinshi kullum a cikin zuciyata, dan haka sai anjima_ " _tana aika masa ta sauka ta kwanta sai bacci_ .

Tunda Ummi tayi sallah ta koma ta kwanta sabon bacci, dan rabon da tayi baccin safe harta manta, lokacin da Khamis zai fita yana break ya tambayi Jawahir Ummi, data fad'a masa tana bacci dariya yayi yace" to wannan baccin haka take yin shi ko gidan malam manu?inko hakane akwai dangwarma dan shi nasan ba yada da'bi'ar siyan abincin waje, kuma yana fita da wuri to kenan ya yake oho"Jawahir ce tace" ai in fad'a maka yaya Salman yanzu ya fara gyara mata zama, dan jiya zuwanta nasha labari , nidai har cikina ma ya fara ciwo tsabar dariya" da gaske kike?" ya tambayeta, " e mana, amma gaskiya yaya Salman baya kyautawa dan inda kaga jikinta duk duka ne,wallahi sai taban tausayi kuma da naga jikinta a farfashe" wani iska ya hurar yace" ni nasan dama sai haka ta faru, dan Ummi ba taji, Sa
lman kuma ba yada hak'uri ga zuciya" to mijina me zai hana ka masa magana akan dukanta, kaga fa hakan babu kyau tunda yanzu tana yin abinda ya sata" ajiyar zuciya ya sauke yace" zan masa, amma sai ya dawo daga tafiya, dan kinsan halin shi murd'add'an mutum ne" haka su kaci gaba da tattaunawa harya gama break ya fita.

Jawahir ce zaune a falo tana charting, Salman ta gani en ligne dan haka ta gaishe shi ya amsa, tambayar ta yayi ina Ummi tace tana bacci, cewa yayi taje ta tasheta, haka taje tasa Ummi gaba tana tadi amma tak'i tashi, dole ta fad'a masa tak'i tashi, kiranta yayi appel vid
o yace ta bata wayar, da k'yar Ummi ta bud'a idonta ta kalli wayar sai magagin bacci take da hamma,
"ke dallah tashi malama, wato an samu dama ko?" juya baki tayi tace" dole kam na dama, tunda nazo gidan yanci, ba kamar wancen kurkukunba" tsaki yayi yace" yanzu ai kin fad'i komai, tunda kinga bana kusa dake" d'an karamin tsani tayi tace" wai ni malam miye na sawa a tasheni ina bacci na dan Allah? kuma kai b
wani abu mai anfani zaka fad'amin ba, ko dai harka fara kewata ne tun yanzu?"cike da takaici yace" waye zaiyi kewar ki? ni?

Allah ya kiyaye" a cikin muryar baccinta tace" in dai hakane to kashe wayar" tana gama fad'a yako kashe wayar, tsaki tayi ta koma ta kwanta.
k'arfe 10:15 tana ta baccinta saiko Ihu da kwaramniya anata jinjigarta ana fadin" ki tashi ki tashi ke" cikin Farin ciki ta bud'a ido dan ta d'auki muryar yan uwan nata, Kallonsu tayi tace" Khairat daga ina kuke yanzu?" kinga kedai taso muje falo" hannunata taja suka wuce da kayan bacci a jikinta riga da wando k'anana,falo suka fito, tana fad'in" wai ku kuma miya kawoku nan ne ku dukan ku?" Nadia ce da duk yayi wani yaushi tace" dama mun san yaya Salman zaiyi tafiya, shine yaya Khamis yace kina nan , shiyasa muka zo dan munyi kewarki" gyara zamanta yayi tace" amma kuma su yaya suka kawo ku?" cikin zumud'i Khairat tace" e mana, kuma sunce ma zasu dunga kawo mu har lokacin da zaki koma" aifa nan hira ta b'arke Ummi ko wanka ta kasa yi saboda dad'in hirar da suke, haka lokacin ya tafi har azahar kafin Ummi ta kalli Jawahir tace"uwar gidan Khamis ba kishan furarki saida nono" dariya tayi tace" kai yar uwa duk wannan kirari haka, ai saiki fasamin kaina" ita ma dariya tayi tace" to ai girman ki ne, kinga nifa yunwa nake ji, me kika dafa mana ne?" hararan ta tayi tace" saidai kije ki dafa, dan wanda na dafa munci ni da Mijina" baki bud'e Ummi tace" lallai ma yarinya, kina nufin ina bak'uwarki amma zanje na dafa abinci da kaina, kamar a gidan wancen mugun, ai kam ba zata sab'u ba"dariya Jawahir tayi ta mik'e tsaye tace" to uwar gidan yaya manu mi kike so in dafa maki?" k'ara shigewa tayi cikin Kujera tace" ki kawo min Tea da bred,sai ki soya kwai yaji albassa sosai,amma karki samun arom ( d'and'ano),gishiri kawai ya isa." wucewa tayi tana murmushi ta shiga cuisine, Khairat kuma cewa tayi" yayi dai hajia Abu, kenan haka kike bawa Yayana umarni ko a gidan?" tab'e baki tayi tace" ke wannan yayan naki? wanda ko murmushi ba yayi bare dariya ai shi kibar shi inda kika ganshi kawai"
Tana gamawa ta kawo mata, k'asa ta zauna tana ci suna hira harta kammala, haka suka wuni a gidan cikin farin ciki, tare sukayi girkin rana dana dare, suna idawa Jawahir ta shiga wanka ta cab'a kwalliya wa mijinta, tana fitowa ta d'auko blander tasa jik'akk'en dabino data jik'a da ranke da kanunfari a ciki ta markad'a, ta koma tasa kankana ta markad'a ta tace ruwan, sannan tasa maltina a ciki da madara peak da k'ank'ara (glasse).
Chapter 13 · 0% Book details