← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 49

Sashe 4

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Dak'yar ta kammala sabida zazzab'i gashi duk jikin ta ciwo yake sabida dukan da tasha, falo ta same shi zaune cikin shiri a jiyewa tayi ta juya zata koma cuisine tunda har yanzu bai bata d'aki ba," ke zo nan" a hankali ta dawo zaune tayi hankalin ta a tv, cikin b'acin ray yace" miye wannan kika dafa?" wani banzan kallo ta masa tace" aw kai bakasan ko miye wannan ba?" tassss ya kwashe ta da mari yana fad'in" ke dan kin raina ni na zauna ina jiran abinci tsawon minti ashiri, amma a k'arshe ki kawomin wannan abar a matsayin abinda zanci na fita, to bari kiji ni ba haka nake kayana ba komai ina yinshi da tsari ki buda kunnuwanki kiji abinda zan fad'a maki" ganin gaba d'aya hankalin ta na kan tv yasa ranshi ya k'ara b'acewa da k'arfi ya fizgota ta fad'o k'asa kusa da shi yana kallan idanta yace" ki nutsu idan b
haka ba wallahi jikin ki zai dinga fad'a maki kinji na fad'a maki sakarya kawai."
Kuka ta fara haka shi kuma ya fara zana mata sharad'an shi da k'a'idojin shi kamar dai....,
" ki tabbatar kowace safiya ina samun abun Kari na da missalin k'arfe 08:00, 08:01 tofa bazan d'aga maki k'afa ba, sannan k'arfe 14:00 na rana ki tabbatar abinci ya kammala kafin na shigo, haka zalika da k'arfe 20:30 na dare kiyi k'ok'arin gamawa kafin minti d'aya ya hau sama"
"Sannan ya zama wajibi gareki da kin idar da sallah asuba kije har d'aki na ki gaishe ni, sannan kowane dare kafin ki kwanta bacci sai kin tabbatar kin kaimin Tea mai kayan kamshi a ciki sannan ki kwanta."
"Sannan ba komai nake ci ba, da safe inasan karyawa da abu mai nauhi,da rana kuma inasan abu mai romo,da daddare kuma zaki iya kawomin komai naci amma banda kifi,Kwa
,tuwo,wake, bana cin su da dare."
"Sannan kowane sati ina azumin litinin da alhamis, dan haka kowane bud'a baki ina bukatar salade, lemon zob'o,kayan marmari, haka kuma duk juma'a zaki dinga dama min fura da rana ina sha, sannan kowace juma'a ina yanka dabba sabida sadaka dan haka zaki dinga sarrafashi ta hanyar data dace sai ayi sadakar, sannan kowace asabar ina gayyatar abokaina suna zuwa muci abinci dan haka zaki dinga dafa abinci mai yawa."
"Sannan kowace juma'a zaki dinga wanke min kaya na kanana sannan ki gogemin su,sannan kowace safiya idan nafita dole zaki gyaramin d'aki na kafin na dawo, wannan shine tsari na kibi ki zauna lafiya, ki k'i bi kisha wahala dan nidai ba zan gaji da dukan ki ba, sannan ki d'auke wannan abar dan bata daga cikin tsari na wannan saike jaka."
Wani kallo ta watsa mashi tace" jaka kuma, ni d'in?" e ke d'in koba jakar bace?" kauda da kai tayi gefe ba tare da yanda zai jita ba tace" jakuna dai" mikika ce?" girgiza kai tayi ta mike tsaye tace" to Malam naji dokokin ka amma kasani ba zan'iya ko d'aya ba, kaji mutum sai kace wani shiya haifeni ko ya hallice ni da zaka zauna ka zana min dokoki" sa'ar cabko hijabinta yayi ya zaunar da ita ya rik'o hannayenta duka biyu, saidai zafin da yaji a jikinta na zazzab'i yasa yace" kar Allah yasa kiyi ko daya d'aya daga cikin abubuwan da na zayyana maki kigani saina lahira yafiki jindadi shashasha kawai mai k'wak'walwar kifi." tsallaka ta yayi ya wuce da sauri tace" to ina zan zauna ni kuma, ko d'akin naka zan dinga kwana?" juyowa yayi yasa hannu aljihu ya ciro makullin ya jefa mata, tayi saurin cab'ewa kamar masu jira a tare suka aikama juna harara Oummi harda tukwicin murgud'a baki, wucewa yayi ya barta nan, d'akin ta ta shiga dak'yar tayi wanka sabida ciwon dake jikinta ta shirya cikin riga da wando ta kwanta kuka ta dinga rerawa sabida takaicin abinda aka mata gashi shi kuma ba imani ne da shi ba.
_Tofa wannan zama_
27/02/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
Samira Harouna
```Dedecated to My Meelat```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Komawa tayi ta kwanta dan ko zai kasheta ba zata yi abinda yace ba, yana fita gidan su ya nufa ya fad'awa Mahaifiyar shi duk abinda ya faru a daren jiya, ta tausaya ma Ummi, ta kuma k'ara jaddada mashi ya rik'eta amana, d'akin shi ya shiga ya ida harhad'a sauran kayan shi yace zai aiko azo a d'aukar masa.

Haka ma daya shiga gidan su Ummi ya gaishe da su La mamma ta had'a mata sauran kayan ta yace zai aiko a d'auka anjima.

Tana bacci a d'aki taji bugun k'ofa, cikin magagin bacci ta taso ta bud'e, matashin saurayi ne ya kawo kayan su, karb'a tayi ta koma d'akin nata tai masu wajen zama, nashi kuma ta bar su nan kafin ya dawo, kwance tayi tana tunani shikenan ta rabu da gida kenan har abada sai in taje da ziyara, tunda take bata taba jin labarin wacce aka kai gidan miji kamar ita ba, kuka ne ya kwace mata ta nayi tana ajiyar zuciya har bacci ya sak
d'aukar ta.

Ummi na gama sallah azahar ta shiga cuisine ta dafa indomie, badan ita take so ta ci ba saidan k'iwa, tana ci ta koma ta kwanta nan saman kujerar bacci ya sak
d'aukar ta, ruwa da taji an watsa mata yasa ta tashi a tsora ce tana piki piki da ido, ganin Salman yasa ta fashe da kuka tana fad'in" ni dama nasani wallahi dan ka dinga min mugunta ne yasa ka aure ni, haka kawai ina zaman zama na an wani had'a ni da kai, gashi kana neman kashe ni" tsaki yayi kafin ya zauna idonshi a tv yace "kawo min abinci na," wata harara ta galla masa tare da juya baki tace "ban dafa ba, ai dama na fad'a maka ba bauta nazo yi ba."
Mik'ewar da tayi tsaye tana ta kakkabar riga, hakan yasa ya tashi tsaye cikin had'e rai yace "durk'usa" wani kallo ta mashi, hakan yasa ya d'auke ta da mari yana k'ara maimaitawa "ki durk'usa nace" zubewa tayi tana kuka ci gaba yayi da fad'in "ki saurare ni da kyau kiji, karki sak
bari na dawo gidan nan ban samu abinci shirye ba, sannan daga yanzu karki sake tashi tsaye in har ina zaune, ko ina zaune ke ma kina zaune, dole ki girmama ni a matsayi na na mijin ki kuma wanda yake gaba da ke, kina jina.?"
Cikin turo baki ta d'aga kai, zaune yayi yana kallonta yace "ki tabbata Kin kawo min ordevre nan da minti talatin, idan kuma ba haka ba to rai zai b'ace," ganin babu alamar wasa a al'amarin yasa ta tashi dan gabatar da abinda yace d'in, awa d'aya ya d'auke ta kafin ta kammala ta kawo masa ta koma ta d'auko ruwa ta aje masa, tana turo baki ta koma d'akin ta tana gunaguni.

Yana ida wa ya mik'e tsaye yana k'walla mata kira "ke! ke!! ke!! ko ba kiji ne.?"
Cikin gadara ta fito tayi tsaye tana kallon k'ofa, bugu ya kai mata a kai yana fad'in "me na gaya maki yanzu?" kamar zata fashe haka tana ji tana gani ta durk'usa gaban shi yana fad'in "saura ki kwanta bacci tsiya ki k'iyin abinda na saki, wallahi da kinga k'ask'anci a gidan nan dan sai na k'arya ki" kallan shi tayi tace "wai yaya Salman me kake nufi dani ne, wannan fa ba daidai kake yi ba, haka kawai kayi ta wani samin doka kamar kai ka halicce ni ko kuma siyo ni kayi. ?"
Waige waige da ya shiga yi ne na neman abun bugu yasa ta arta a guje ta shige d'aki ta Kulle tana fad'in "wallahi saidai ka kashe ni amma ba zanyi ba, haka kawai daga zuwa na zaka wani ce wai abokanan ka zasu zo dan bak'ar jaraba."
Jin abinda take fad'a ya santa farin sani ba zata yi b
, dan haka ya fita ana idar da sallah la'asar ya dawo gidan ya sata aikin dole hannun shi rik'e da tsumagiya, harta gama aikin tana kuka shiko ko a jikin shi tunda ta mashi abinda ya ke so wannan ba matsalar shi ba ce ko kukan jini zata yi.

Tana idar da sallah isha'i tayi wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci tunda babu wani abun daya rage mata daya wuce ta kwanta tayi kuka bacci ya d'auke ta, Salman ne ya k'wank'wasa k'ofar d'akin a hankali ta bud'e tana kallan shi tace" ya dai Malam?" tun daga sama har k'asa ya kalleta kafin yace "ki fito ku gaisa, amma ki sanyo hijjab." Wuce wa yayi ya barta ita ma ta koma ciki ta d'auko hijjab tasa sannan ta fito.

Oummi ta d'auka wasu bak'i ne ashe ma su Khamis ne da sauran y'an uwan nasu, cikin farin ciki suka gaisa Oummi ta zuba masu abinci ta aje a gaban kowan ne, Salman ta zuba ma tana dariyar mugunta da gangan ta zuba masa abincin a jiki, da sauri ya mik'e yana fad'in "ke! ke!! wai ke wacce irin sakarya ce baki gani ne?" juya baki tayi ta wuce tana rera waka ta barshi nan, hakuri Khamis ya bashi suka ci gaba da cin abinci suna hira cikin nishad'i.
_Yan Uwa ance tuna baya shine rok'o, amma ance waiwaye Adon tafiya_
27/02/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*ZAMAN AMANA WRITER'S* _
( _Gidan zaman lafiya da_ _amana_ insha Allah)_
*Page*
*Alhaji Usman mai Dala* Tshoho mai ran k'arfe haka jikokin shi suke kiran shi wani lokacin, ya nada mata hud'u, *_Hajia Salamatou_ _Hajia_ Zeinab* *Hajia Hawa'ou Hajia* *Mariya* , ya nada yaya ashirin da takwas jikoki da dama, mutum ne mai kakkausan ra'ayi mai tilasta iyalen shi akan duk wani abu da yake so koda basu san shi, ya d'auki turbar had'a tsakanin yayan shi da yayan yan uwa aure dan k'arfafa zumunci, duka yaran sa babu wanda ko wacce ta kawo zabinta duka *AUREN HA'DI* ya masu.
Chapter 4 · 0% Book details