← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 49

Sashe 29

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 6 min read

Har yau har gobe idan Ummi ta kira La Mama dan su gaisa, sai La Mama ta k'ara jaddada mata akan ta kula da mijinta sannan saita fad'a mata wani abu da zata k'aru da shi ko dan rayuwar gaba.
*WATA BIYU*
A lokacin ne su Jawahir suka fara shirye shiryen komawa makaranta, in da Ummi ita ma ta nemi izinin Salman akan ya barta ta koma makaranta, sam Salman yak'i amincewa yace sai tayi hankali sannan zata fara fita ma daga gidan.

Ummi tayi kuka tayi magiya tayi rarrashi amma sam yak'i yarda, dole Ummi ta hak'ura ta shafa ma kanta lafiya, yayin da su Jawahir suka fara karatu sai dai suma suna kewar Ummi sosai duk da tana gaba dasu a ajin, amma dai koba komai zasu dinga had'uwa.

Tun lokacin sai Ummi ta sauya gaba d'aya ta daina walwala ba kamar da ba, yanzu duk abinda Salman zai mata bata kula shi sai dai ta bishi da ido kawai, hakan ba k'aramin tab'a Salman yayi ba dan kuwa farin cikinta shine nashi, amma yanzu gashi ta daina gaba d'aya, dole Salman ya nemi mafita daga matsalar dan a ganinshi koda ace ba abinda yake da iko a kanshi bane ai zaiyi k'ok'arin ganin ya sata farin ciki, bare kuma yana da iko.

Ummi na zaune a falo tana kallo tare da uban tagumin data rabka Salman ya shigo da sallama, kallo d'aya ta masa ta kau da kanta tana amsa sallamar, zaune yayi kusanta yana kallonta, ledar dake hannunsa ya mik'a mata ta karb'a tana kallonsa ta aje ledar dan a tunaninta irin kayan k'walam d'in da yake siyo mata ne.

Kallonta yayi yace "miye haka kuma? ya za'a baki abu amma ba zaki duba ba ki gani, kawai saiki aje."
Ko kallonshi ba tayi ba ta d'auki ledar ta fara dubawa, take farin ciki ya lullub'eta saboda ganin d'inkakken tenue (uniform) da sauran kayan makaranta da duk abun da d'an makaranta zai buk'ata.

Fiddo kayan tayi ta mik'e tsaye tana gwadasu a jikinta bak'ak'e (tenue 'yan lyc
e ne na moufida), riga iya gwiwa wacce ta bud'e sosai da gajerun hannuwa sai dogon wando mai forme d'in slim da kuma hijab daya wuce rigar, sannan da nik'ab, cikin mamaki tace,
"Wannan fa yaya Salman na miye?"
Murmushi yayi yana kallon tsantsar farin cikin dake kan fuskarta yace "naki ne"
Bud'a baki tayi cike da farin ciki tace "wow, yaya Salman amma naji dad'i sosai, hakan kenan na nufin zan koma makaranta nima?"
Da ido kawai ya mata alamar Eh, cike da farin ciki ta k'araso wajenshi ta zube k'asa tana fad'in,
"Kai amma yaya Salman naji dad'i sosai, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya k'ara bud'i na alkairi, Allah bar min kai, Allah ya saka maka son...."shiru tayi ta kasa k'arasawa.

Mamaki ne ya bayyana a fuskarshi tare da fad'in "ya saka min son mi?" kai kawai ta girgiza alamar ba komai, mik'ewa yayi ya nufi d'akinshi ita ma haka, suna kaiwa k'ofar d'akin Ummi tace,
"Yaya Salman yaushe zan fara tafiya?"
"Gobe mana"ya fad'a yana bud'a d'akinshi, murmushi tayi wanda ya bayyana hak'oranta tare da dinple d'inta sosai, Salman dake k'ok'arin shiga d'akinshi ne tsaya tare da dawowa yana kallonta, a hankali yasa d'an yatsarshi akan dinple d'inta ya latsa, ita kam k'ura mashi ido tayi tana kallo yayin da shi kuma kasa had'a ido da ita saboda tartsatsin da yake ji idan yana kallon idonta ma abota girma da fari.

Bai bar latsa kumatunta ba yace "Ummi na barki ki koma makaranta ne saboda tabbacin da nake da akan ki, na san zaki kula da kanki sannan zaki karemin mutunci na dama mutuncinki."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon cikin idonshi tace "insha Allah yayana, ba zan tab'a baka kunya ba, sannan ba zanyi abinda zai shafi mutuncin ku ba, zanyi iya bakin k'ok'arina wajen ganin na kare maku hakk'inku da yake kaina musamman ma kai."
Murmushin jin dad'i yayi yace "me yasa musamman ma ni?"
K'asa tayi da idonta cikin jin kunya tace "saboda kai mijina ne." tana fad'a ta k'arasa shigewa d'aki tana dariya, Salman ma haka d'aki ya shiga yana jin wani sanyi na ratsashi yana ji ina ma ace Ummi ta fad'a mashi kalmar so a matsayin godiyar abinda ya mata.

Tun asuba Ummi da tayi sallah bata kwanta ba, tana gama had'a abinda kari ta d'an gyara abinda zata gyara a d'akinta da falo dama cuisine, tana kammalawa ta shiga wanka tana fitowa tsaf ta shirya cikin tenue d'inta.

Jakarta ta d'auko da hijab da nik'ab ta fito falo ta ajesu saman kujera sannan ta nufi d'akin Salman dan ta tashe shi, da sallama ta shiga amma shiru bai amsa ba alamar bacci yake, saida ta k'arasa har gabanshi ta k'ura mashi ido tana kallo yana baccinshi cikin kwanciyar hankali.

Rumgume hannayenta tayi a bayanta a hankali tace "ina sonka yaya Salman, sai dai ba zan iya fad'a maka ba, dan na san kai baka sona kuma ba zaka soni ba, amma zan ci gaba da jiran lokaci na san zai zo."
Lek'a fuskarshi tayi taga sosai yake baccinshi dan haka ta sunkuya daf da k'eyarshi ta sumbata, mik'ewa tayi tare da zura hannunta ta rufe hancinshi, da sauri ya juyo da kanshi yana bud'a idonshi yana ganin Ummi ya tashi zaune yana ci gaba da kallonta, murmushi kawai take masa kafin yace,
"Wannnan kuma wane irin tayar da mutum daga bacci ne?"
D'aga kafad'u tayi tare da d'aga gira sama alamar ba magana, saukowa yayi daga kan gadon yana fad'in "saina ji kamar an sumbace ni a kaina ko?"
Bud'e baki tayi cike da mamaki, lokaci d'aya kuma tayi k'asa da kanta tana wuru wuru da ido, gaf da ita ya matso yace "kece ko, ko dai akwai abinda kike b'oyewa ne ban sani ba?"
D'ago ido tayi suka kalli juna, ja tayi da baya tana fad'in "haba dai sumbata fa? sai kace wani jariri."
Toilet ya nufa yana fad'in "banyi mamaki ba dan kince haka, amma ki sani wani lokacin ma miji yafi jariri buk'atar kulawa."
Kallonshi tayi tace "to, ni dai na san ana cewa namiji kamar k'aramin yaro ne, duk in da kayi dashi can zaiyi."
Tsaye yayi yana kallonta kafin yace "kuma ke kin yarda da abinda aka fad'a d'in?"
Murmushi tayi tace "me zai hana ko, tunda mune ke jan ragamar."
Ganin ya tun karota yasa tayi saurin ja da baya tana fad'in "dan Allah ni dai kaje ka shirya kar nayi late a zuwan farko."
Sai lokacin ya lura da kayan dake jikinta dan haka yace "oh, hakane fa, ok ki bani 5 minute ina zuwa."
Kallon agogon dake gefe gadon tayi tace "ah bon, 5 minute?
Chapter 29 · 0% Book details