← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 49

Sashe 46

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 6 min read

Gashi dai Ummi tana so ta ci amma ina ta kasa, a hankali Salman ya dinga dib'a yana sa mata baki, amma koda ta karb'a sau uku bata k'ara na hud'u ba, cikin rarrashi yace "haba Mamar 'yan biyuna ki k'ara mana ko kad'an ne."
Kamar za tayi kuka tace "La Mama ki fad'a masu su daina cemin Mamar 'yan biyu."
Bud'ar bakin La Mama cewa tayi "haba Ummi wannan girman ciki naki masha Allah in baki haifi 'yan uku ba ko yan hud'u, ai dai kya haifi 'yan biyu."
Salman bushewa yayi da dariya yace "ahan, kinga ashe La Mama ma kallon Maman 'yan uku da hud'u take maki."
Ba tayi magana ba Islam ta shigo hannunta rik'e da Ihsan autar Sa'ada, wajen Ummi ta zauna tana mata magana amma ko jinta ba tayi, Salman ne yace "Ihsan ki rabu da auntynki bata lafiya nak'udar 'yan biyu take." ya fad'a yana shek'ewa da dariya.

Cikin d'umin yara Ihsan tace "eh tonton, ai kasan aunty 'yan biyu zata haifa ko?"
Cike da fara'a yace "ashe kema kin sani, to waya fad'a maki?"
"Wallahi ko tonton 'yan biyu ne ni da kaina na gani."
Dariya La Mama tayi tace "shi kenan ya tabbata 'yan biyu zaki haifa insha Allah, sai dai fatan Allah ya sauke ki lafiya sannan muga mi zaki haifa."
Tun Salman na hira da Abba ya lura da Ummi bata jin dad'i sosai, haka ma Abba yana kallonta duk saiya ji tausayinta ganin yanda ta canja k'afafu a mik'e ko motsin kirki bata iya yi, ai kam sai nak'uda tace salamu alaiki Ummi gadan gadan ta taso mata, tuni suka d'auketa sai asibiti yayin da Mama dasu Hajiyoyin Alhaji suka biyo bayansu, 22:30 suka je asibiti amma cikin ikon Allah da addu'o'in iyaye sai ga santalen santalen kyawawan yara maza guda biyu an fito ma dangi dasu waje su gani da misalin k'arfe 23:40.
```FARIN CIKI KENAN```
'Yan biyun farko kenan a cikin famillyn Alhaji Manu mai dala (tsoho mai ran karfe), irin farin ciki da walima tare da kyaututtukan da 'yan biyu suka samu basa misaltuwa, mahaifin yara bakinshi ya kasa rufuwa komai siyowa yake wa yara da mai jego, ya bawa Ummi kyautar yaran dukansu saboda bai san me zai bata ba, amma matsayinshi na uba yayi alk'awarin kula dasu, haka aka gudanar da suna aka kashe kud'i sosai Ummi ma tayi bajinta dan ba komai take cewa Salman yayi ba ita ma nata kawai take yi da guminta.

Yara sun samu suna ```MOHAMED TAUFIK' da ```MOHAMED RAFIK', Allah ya rayaku akan sunna.

Kwana biyu da biki Inna da aunty Fateema suna shirin tafiya, Salman ya shigo d'auke da ledoji biyu d'ayar ya bawa su Inna d'ayar kuma ya mik'awa Ummi wai na 'yan biyu ne, tana bud'awa kayan yara ta kuma gani kuma abin dariyar kowane iri hud'u hud'u, cikin jin haushi Mama tace,
"Wai kai miye haka, abu kamar hauka ina ma laifin ka siyo kala biyu, amma saika siyo kowane har hud'u hud'u, duk me za ayi dasu ka duba kaga gudan tarin tilin kayan da yaran nan suka samu fa."
"Ayi hak'uri Mama, ai sai a aje ko wasu an bawa idan anyi haihuwa." cewar Ummi da taji babu dad'i kalaman da Mama ke fad'ama jarumin nata.

Haka suka dinga tafiyar da sabuwar rayuwarsu tare da yaransu masu kama da mhaifinsu sai dai kumatunsu suna lotsawa ko murmushi sukayi kamar dai mahaifiyarsu haka kuma jikin mahaifiyarsu dan 'yan lukutayene yaran, Islam da Momy ne suka zauna gidan bayan tafiyar mai tsaronta suke tayata kula da yaran, gashi har yanzu bata iya masu wanka ba sai Salman keyi masu, nono kad'ai ke had'ata dasu da sunsha su Momy zasu karb'e su suyita jagula sai in sunyi bacci kawai, idan kuma babansu ya dawo to suna hannunshi dan ko bacci sai dai ya d'orasu akan k'irjinshi yana shafasu har suyi bacci.
```Muje zuwa```
29/03/2019
20:22 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
*FIN*
```{k'arshe}```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Salman ne zaune k'asa ya mik'e k'afafu yasa robar wankan yara tsakiyar k'afafunshi da Taufik' a hannunshi yana masa wanka sai lumshe ido yake alamar bacci yake ji, Ummi kuma na gefensa da Rafik' tana shiryasa cikin k'ananan fararen kaya masu kyau, masha Allah yaran sun girma dan har sun iya zama suna k'ok'arin fara rarrafe, wasa take masa shi kuma yanata dariya yayin da kumatunshi keta lotsawa ciki kamar na Ummin, doguwar hammar da Salman yayi ce yasa ta kalleshi amma ba tace dashi komai ba, saida ya k'arashe sannan tace "haba 'yallab'ai irin wannan doguwar hamma haka, duk ta kwanan ce?"
Cikin muryar bacci yace "Eh mana, ya kike so nayi to? tunda kin kasa barina nayi baccin."
Tab'e baki tayi tace "hum, to nidai ku kula karku sakawa yarona kunfa a hanci, dan in haka ta faru ba yarda zanyi ba." ta k'arashe tana murguda baki.

Kallonta yayi yace "ke yanzu ko kunya ba kiji ba da ki kace d'anki, to d'anki dawa ya baki?"
Cikin kuri tace "Allah ne ya bani."
Ci gaba yayi dayi masa wankan yana fad'in "hum, amma kuma har yanzu baki san yanda zakiyi kiyi masu wanka ba, watansu biyar a duniya amma bana jin kin tab'a masu wanka ko sau d'aya."
Turo baki tayi gaba tana fad'in "to ai dai zan iya nima, kuma kune ku kace kun d'auki alhakin yi masu wanka , dan haka ni kuma bana masu."
Kallonta yayi yace "shi yasa kenan kike tayar dani daga bacci yanzu dan nayi masu wanka?"
"Eh mana." ta fad'a tana sumbatar kumatun Rafik' data gama masa shirinsa.

Yana gama d'auraye ma Taufik' jikinshi ya sakashi cikin towel ya mik'a mata ta karb'a dan ta shiryashi, mik'ewa yayi tsaye yana fad'in "dan Allah kiyi zuciya ki iya yi masu wanka da kanki, sannan zanje na kwanta kiwa Allah karki tasheni ki bari na k'arasa hantsewa."
Hararan sama da k'asa tayi masa kafin tace "sannu, na barku kuyi bacci?ai bazai yiyu ba tunda baku gama dani ba."
Dafe k'ugu yayi da duka hannayenshi biyu yace "duk ni kad'ai keda wannan hararan?to na gode, amma dan Allah ki barni na huta, kefa kinfi kowa sanin gajiyar dana deb'o kuma ban shigo garin nan ba sai cikin dare har kunyi bacci, amma shine duk da haka kin kasa barin mijinki ya huta."
Dariya tayi tace "shikenan kuje ku kwanta, ba zan tayar daku ba, amma zan shigo kumin wanka ku shiryani saboda lokaci yayi na tafiya gidan Alhaji, ko kun manta yau k'arshen wata ne?"
Wucewa yayi yana fad'in "to ni dai zan kwanta ba yanzu zanje ba saina huta gajiya."
Tana gama shirya Rafik' cikin shiga irinta Taufik' ta ajiyeshi kusa da Taufik', ita kuma ta d'auke robar da akayi masu wankan ta gyara wurin sannan ta aje masu kayan wasa a gabansu ta sunkuya tace masu "zanje wajen papanku yamin wanka, kuyi wasa kafin na dawo."
Tana fad'a ta shiga ciki, kwance ta sameshi cikin blanket, yaye blanket d'in tayi ta haura kan gadon ta hayeshi ta fara mashi magana cikin kunne "ku tashi kafin na tayar daku."
Saida ya k'ara dunk'ulewa yace "um um, ba zan tashi ba, dan Allah ni ki d'agani kin wani zo ki sakar min nauyinki."
K'ara mak'alewa tayi a jikinshi tace "wallahi ku tashi kafin na tayar daku, kunsan dai zan iya ko?"
"Nak'i d'in, kiyi abinda za kiyi." ya fad'a yana tutsa kanshi tsakiyar pillow.
Chapter 46 · 0% Book details