Sashe 48
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 6 min read
Hira suka fara yayin da Soumayya zuciyarta keta tafasa saboda bak'in ciki, ko kallon Ummi da yaranta bata san yi Rumana kam rayuwarta take bata damu ba dan dama bata sa a kai ba, Jawahir ce ta kalli Salman ta kalli Ummi tayi murmushi tana fad'in,
"Duniya kenan, yau ga Ummi da Salman a inuwa d'aya a matsayin ma'aurata masu k'aunar junansu."
Dukanta Ummi tayi a kafad'a tace "ke kuma da tashin tashina, miye na tado abinda ya wuce?"
Khamis ne ya harareta yace "karki sake dukar min mata, an tuna bayan."
Salman ne ya doki kafad'arshi yana fad'in "an doka d'in me zaka yi?"
Jawahir ce tace "wannan fa zalinci ne, kawai dan kuna gaba damu sai ku dinga d'irkanmu."
Hajia babba ce tace "to ai dole ne Ummi, dan idan aka had'a rayuwarku ta dah data yanzu dole kowa zaiyi mamaki, kullum idan muka ganku sai mun tuna da shiriritarku ta baya."
Kallon juna sukayi da Salman lokaci d'aya suka k'yabtawa juna ido tare da siririn kiss, dariya tayi tace "to Hajia ai dai aikin gama ya gama sai a daina tuna baya."
Hajia Abu ce tace "ank'i a daina tuna bayan, rayuwa in ba'a d'an tab'o abinda ya faru baya ai babu armashi."
La Mama ce tace "to ai bata da gaskiya ne shi yasa take so abar maganar."
Mama ce tace "ai shine mai laifi tunda shine mai dukanta ko ba tayi laifin komai ba."
Daga gefe Salman yace "haba Mama ta yaya za'a doki mutum baiyi laifi ba, ai da kunga na daketa to wani abu tamin."
Hararanshi Mama tayi tace "dubeshi dan Allah har wani dad'in fad'a kake ji."
Sa'ada ce tace "kuma su La Mama ai kun zama kamar b'era da mage idan su Ummi suna tare kuma saiku koma mafad'ata."
Dariya akayi Abba ne da Rafik' k
e hannunsa yace "to ai kowa akwai team d'in da yake, kowa baya so aga laifin nashi."
Alhaji dake zaune a kujerarshi yana kallon kowa yace "to waini abinda ma ban gane ba, bansan miye ya haddasa wannan rikici ba a tsakaninsu? ni dai naga kawai suna fad'ansu."
Kallon juna sukayi ita da Salman sukayi dariya, Ummi ce tace "to nima dai ban sani ba, amma ku tambayi papan 'yan biyu kuji."
Wata harara Soumayya ta jefi Ummi da ita ta gefen ido jin abinda ta fad'a, Salman kam cewa yayi "a'a nima ban sani ba, ke zaki iya tunawa."
Hajia babba ce tace "uhum, kun gani ko, a k'arshe ma basu san akan me suke wannan shirmen ba kawai rashin hak'uri ne da k'uruciya dake damunsu."
Ummi ce tace "a'a Hajia, ni dai nasan cewa a waccen lokacin yaya baya san ana murgud'a masa baki da harara, uwa uba kuma ka masa tsaki, to ni kuma kawai saina ji inayi idan muna tare dashi amma bawai dagangan nake ba."
Wani kallo Salman ya mata yace "ai ko yanzu bana so, kawai dai na daina dukane yanzun saboda na samu hanyar da tafi ta dah."
Wani kallo Ummi ta masa tare da wurga mashi ido alamar akwai mutane fa, Alhaji ne yace "to koma dai miye yanzu ai gashi nan suna zaune lafiya kamar ba sune lokacin da aka d'aura auren suketa kururuwa ba suna fad'in basa so, amma yanzu na tabbata da za'a ce a rabasu to sai dai ku jisu a asibiti."
Abin mamaki bakin Salman dana Ummi ne suka had'u wajen fad'in "sai dai k'abari."
Tin tsirewa akayi da dariya Hajia ta d'ora da "ja'iran yara kawai, ku kun d'auka *AUREN HA'DI* da ake maku ana maku dan ba'a sonku ne, amma idan har zakuyi hak'uri kuyi biyayya to ku zaku fi kowa jin dad'inshi da moriyarshi."
Saida akayi sallah azahar aka ci abinci sannan Alhaji ya tara iyalin nashi ya masu nasiha tare da gargad'i da mahimmancin had'a kansu, ya kuma nuna masu da lokacinshi ya kusa dan haka yace "yanzu ya rage naku ku ci gaba da had'a 'ya'yanku aure, ko kuma ku barsu su auri zab'insu, amma ni dai Allah ya sani nayi yina wajen ganin na had'a kan iyalina na k'ulla zumunci a tsakaninsu ko bayan ba raina, wasu tunaninsu kawai ina masu *AUREN HA'DI* ne saboda ina gaba dasu da iyayensu, amma ba haka bane babban dalilina shine naga kun tashi kanku a had'e kuna son junanku sannan ranar lahira fiyayyen halitta (S A W) yayi alfahari da zuri'ata, da wannan nake bawa duk wani wanda nama ba daidai ba hak'uri nake kuma neman yafiyarku."
"Sannan ku zama tsintsiya mad'aurinki d'aya, ku had'a kawunanku ta yanda babu wani mahaluki da zai iya ganin bayanku, kar wanda ya ware kanshi daga cikin 'yan uwanshi dan duk lokacin da wani bala'i ya taho, to zai fara tunkarar wanda ya ware kanshi shi kad'ai, dan Allah ku zama masu k"aunar junanku kuso junanku ku zauna lafiya, dan da hakane zan samu kwanciyar k'abarina cikin lumana, sannan ina rok'on duk wanda yaji dad'in abokin zaman dana had'ashi dashi, to ya aikamin da sak"on addu'a a k'abarina a lokacin da nabar duniya, dan shine kad'ai tukuicin da zaku iya yimin."
"Sannan daga yanzu na daina saka hannuna a al'amuran da suka shafi rayuwarku, kowa zai iya cin gashin kanshi amma kuma kowane mahaifi ko mahaifiya zata iya yanke hukunci akan d'an da koda ba daga cikinka ya fito ba, haka kuma duk wani daya girmema wani koda da kwana d'aya ne to yana da damar da zai iya tsawatarwa dana k'asa dashi, da wannan nake cewa Allah ya maku albarka, Allah ya albarkaci rayuwarku, Allah ya had'a kawunanku, Allah ya sakama zuriarku albarka, Allah ya kareku daga sharrin masharranta, Allah ya kawar da idon mak'iya daga kan wannan zuria tawa mai tarin albarka, duk wani mai son ganin bayanku Allah shiryashi idan mai neman shiriyane, idan kuma ba haka ba to Allah ya mana maganinshi."
Kamar yanda suka dinga amsa masa da ameen, haka a k'arshen addu'ar ma suka amsa da "ameen."
Ana gama sallah la'asar kowa ya koma gida, Mama da k'yar ta basu 'yan biyu suka tafi dan ji take kamar su bar mata su su kwana anan, suna zuwa gida Ummi ta cire masu kayan ta saka masu marasa nauyi itama ta canja sannan ta shiga girki.
Salman na kwance akan gado yana kallon tv da bai jima da yasa aka mak'ala mashi ita ba, remonte ce a hannunshi ko riga babu a jikinshi sai dogon wango, Ummi ce ta shigo d'akin cikin wata had'add'iyar kwalliya mai d'aukar hankali, doguwar rigar bacci ce a jikinta kad'an ya rage ta sauka k'asa sai dai shara shara ce da siraren hannuwa, best colour d'in da Salman yafi sone wato bleue sai fari da bak'i sosai rigar ta mata kyau, ga wasu dogayen takalmi data saka suma bleue sai gashinta data saki ya sauka a bayanta, tafiyar da take yi ce ta d'auki hankalinshi sosai bai d'auke ido daga kanta ba har saida ta cire takalminta tabi ta kanshi ta kwanta gefenshi suna kallon juna.