← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 49

Sashe 18

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read

Sannu da zuwa su mama suka masa cike da mamakin yanda yazo bai sanar da kowa ba, tsaye yayi kusan k'afafunta data ji ciwo k'afar dama an nad'eta da bandeji tun daga wajen ijiyar sau har zuwa cikin tafin k'afar saboda k'arfen daya karceta har farar coka ta fito, sai k'afar hagu kuma gurjewa ne a gwiwa amma saboda buguwa da k'afar tayi kuma adaidaitar ta tausheta hakan yasa tayi kumburi sutum da ita, sai kuma hannun dama data fad'a samanshi ba daidai ba ta goce.
_Hum dama 'yan magana sunce, in haka ji bari ba kaji hoho_
Da k'yar ya tambayi abinda ya faru, ana fad'a masa ya kalli Jawahir dake gefe da 'yar gurjewarta a hannu yace
"Kingani ko Jawahir da yake ke kina jin maganar mijinki, kinga baki ji ciwo sosai ba Allah ya k'ara kiyayewa"
Take La mama ta maida kallonta ga Ummi, Ummi kam da hannu ta mashi alamar yayi shiru, dan inhar La mama taji to abinda zata mata sai yafi ciwon dake jikinta yi mata zafi.

Zagayowa yayi ya zauna kusa da ita, saida ta sauk
ajiyar zuciya saboda shak'ar kamshin turarenshi har cikin zuciyarta taji dad'in zaman da yayi kusa da ita, ji tayi kamar ta fad'a jikinshi ya rumgumeta, kallonta yake sosai dan har yanzu yana mamakin abinda ta aikata, baiyi tsammanin zata tafi ba daya hanata ashe da gaske take zata tafi.

Cikin shagwab'a tace "yaushe ka dawo?" kafin ya bata amsa La mama tace "abinda ya kamata ki tambayeshi kenan?" k'ara kwab'e fuska tayi tace" kazo lafiya, ya hanya?"
Tsawa La mama ta mata tace "Ummi mijinki kike kira da kai, babu girmamawa a ciki ba zaki iya cewa kunzo ba, saidai kazo?" kamar zatayi kuka amma ba tace komai ba, Hajia Zeinabou ba zata juri ganin b'acin ranta ba dan haka tace,
"Kai kuma ka amsa mana, yarinyar dake cikin halinnan ai tayi 'ko'kari ma data iya gaishe shi." kallon Hajia yayi yace "ba zan amsa ba Hajia saboda bakisan m
ta aikata ba"
Yana fad'a ya mik'e ya fita harabar asibitin, La mama tashi tayi tabi bayanshi, tsaye tayi tana Kallonshi kafin tace,
"D'ana ka fad'amin meta maka dan Allah?" kallon La mama yayi cike da kunya sannan yace "La mama babu komai wasa nake mata"
Murmushi La mama tayi tace "Salman yaushe ka fara b'oyema mahaifiyarka farin cikinka da damuwarka dama sirrinka?" baya b'oyema La mama komai, idan har bai fad'a mata abinda zata nutsu ba to ya san zata iya huce haushinta akan Ummi dan zata titsiyeta saita fad'a mata.

"A'a La mama bawai na b'oye maku bane, kawai jiya munyi wayane da ita kuma munyi akan ba zata sak
kashe waya ba, amma nayita kira tun safe bata d'auka ba sai yanzu nazo na tarar da abinda ya faru."
Ko kad'an La mama bata yarda ba, amma bata so ta takurashi dan haka tace "shikenan ba damuwa" ciki La mama ta dawo amma badan mutanen dake d'akin ba da sai ta tambayeta abinda ya faru.

Salman ya jima yana jin babu dad'i yana tunani akan abinda Ummi tayi "me yasa tayi haka, me yasa da nace ta zauna tak'i zaunawa, shin abinda ya fad'ane da wasa dan ya hanata fitar shine ya faru da gaske, shin dama haka bakin miji keda ta siri akan matarsa, inko hakane dole nasan me zan dinga fad'a mata tunda dai ita ba zata ji maganarshi."
"Yanzu gashi abinda ya faru da ita, yanzu da ita ce fa abinda ya faru da mai adaidaita sahun ya faru da ita fa saime ya faru da ni?" ya tambayi kanshi.

Zunbur ya mik'e tsaye daga kan tabarmar da yayi sallah la'asar, cikin sauri ya nufi d'akin da suke yana fad'in "ina babu abinda zai sameta insha Allah, tana nan tare da ni ba zata mutu ba muna nan tare."
Tsaye yayi k'ofar d'akin saboda mutanen dake ciki, idonshi akan Ummi wace idonta sukayi jawur alamar har yanzu tana kuka, juyawa yayi ya fita daga d'akin gida yasa Khamis ya kaishi.

Wanka yayi ya shirya sannan suka fito tare restaurant (maqui) ya ajeshi dan yaci abinci amma saiya kasa, tunaninshi ya koma kan Ummi da ciwonta dan gani yake kamar shine silar hatsarinta, haka suka dawo asibiti suna zuwa lokacin magrib yayi dan haka suka tsaya masallaci sukayi sallah sannan suka wuce d'akin da Ummi take.

Sun samesu sun shirya suna jiransu zasu tafi gida, Hajia ce ta kalli Salman tace "kaga tunda ba zata iya takawa ba, ka d'auketa ko"
Ido ya fiddo ya kalli kowa dake d'akin yace "haba Hajia ai k'wara na d'aukeki na goya akan wannan b'ulleliyar, dan zata iya karyani gashi dama ina jin yunwa, kinga saimu fad'i daga ni har ita."
"Kaga banasan rainin wayo, in zaka d'auketa ka wuce muje ka d'auketa, in kuma ba zaka d'auka ba nasa Khamis ya d'aukarmin 'yar leleta." ta fad'a tana kashe ma Khamis ido.
05/03/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
```DEDECATED TO```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
_Kunada karamci a gareni matsayinku da girmanku ya mafi haka, domin daga cikinku ne na samu makusanta masu nunamin k'auna a kowane lokaci *Yan ZAMAN AMANA* ina k'aunaku dukanku._
'KUNGIYATA ABAR ALFAHARI MAI NUNA DAMUWA GA WANDA YAKE CIKINTA
*Page*
Matsowa Khamis yayi kamar zai d'auki Ummi, saiko Salman ya hankad'eshi yana fad'in" dallah malam gafara daga nan" bushewa sukayi da dariya, shi kuma sunkuyawa yayi ya zura hannunshi ta bayanta ya tallabota, d'aya hannun kuma ta k'asanta nanma ya ciccib'ota gaba d'aya.

Kamar zuciyarta zata fasa k'irjinta ta fito haka yake jiyo bugun zuciyarta, yana sama da ita Ummi ta rufe ido ta kau da kanta gefe, Salman kam wucewa yayi su Hajia na gaba suna baya, tafiya kawai yake fuskarnan a had'e kamar hadarin gabas gashi babu wani alamu daya nuna yana jin nauyin abinda ya d'auka.

Dan kuwa a tsaye yake k'yam, dan shi anashi b'angaren kawai bai d'auketa mai nauyi ba duk da k'ibarta, dan k'arafan da yake d'auka ma sunfita nauyi, suna haka ne wayarshi ta fara ruri, ba tare daya kalleta ba yace,
"Malama fiddomin wayata".

Sai lokacin ta juyo da kanta, a hankali tasa hannu a cikin aljihun rigarshi na gaba ta ciro wayar kamar ta d'auko maciji, tana ganin sunan daya fito a
cran d'in wai *REINE*(sarauniya).

Hawaye taji sun zubo mata haka kawai saiko ta jefar da wayar k'asa, Salman na ganin haka ya tsaya cak tare da kallonta yace "miye haka Ummi kina lafiya kuwa, kodai had'arin harda kanki ya tab'a?"
Kawai saita k'ara fashewa da kuka tana fad'in "azzalumi kawai dama kasan wacce zata kiraka wato sarauniyarka shiyasa kace na d'auka dan dai naji haushi ko, to wallahi sai Allah ya sakamin mugu kawai."
Sai lokaci yasan ko wacece ta kirashi, tabbas Nuseiba ce dan ita ya sama sunan sarauniya, (kenan abinda Jawahir ta fad'a gaskiya ne, Ummi tana kishin shi, to amma miyasa?),.

K'ara matseta yayi a jikinshi ya sunkuya ya d'auki wayar data fashe yasa aljihu, sannan suka wuce.

Jiniyar kukan da take ne yasa yace "kenan wannan kukan na kishi ne ?"
Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "Allah ya sawak'e nayi kishinka"
Ba tare daya kalleta ba yace "kenan najin dad'ine kike saboda na d'aukeki?"
Mitsiniya ta fara tana cewa "kaga ni saukeni dan Allah zanje da k'afata, abinda hannun ma sai tauri kamar katako"
Tana fad'in haka hannunshi dake kusa da k'irjinta ya ida zurawa ya matse mata mama, yar k'aramar k'ara ta saki saboda yanda taji zafi, kallonta yayi ya d'aga mata gira yace "mi kika ji 'yan mata?"
Cike da shagwab'a tace "Allah saiya sakamin kuma ban yafe ba mugu"
Rufe idonshi yayi lokaci d'aya kuma ya bud'e, harga Allah baya so yaji tana fad'a mashi irin haka, amma ya zaiyi bakinta ya riga ya saba ba zata iya dainawa ba.

Suna kaiwa Jawahir ta bud'
masu k'ofa ya ajeta sannan kowa ya shiga suka wuce, gaba d'aya gidansu suka wuce, Hajia saida ta d'ora ruwan zafi ta barma Salman sallahun ya gasa mata k'afa ya kuma tabbatar tasha magani sannan ta kwanta, haka ma mahaifiyarshi saida ta sak
jaddada masa kula da ita sannan suka bar gidan Khamis ya mayar dasu gida.

Ruwan nayin zafi ya d'auko tare da d'an k'aramin towel, kusa da ita ya zauna inda ta mik'e k'afafunta, towel d'in ya tsoma cikin ruwa ya fiddo ya matse sannan ya aza mata a k'afar, k'ara ta saki tare da janye k'afar da sauri, saidai ina ta manta ciwon da take mata, runtse ido tayi saboda azaba ta fara matso k'walla.

Salman kam in banda d'aci babu abinda zuciyar shi keyi masa, ji yake kamar ciwon ya dawo jikinshi zaifi mashi sauk'i, rik'e k'afar yayi yace "sannu ko, bari na maki hankali"
Mamaki ne ya lullub'e Ummi dan haka ta saki baki tana kallonshi, a hankali ya dinga gasa mata k'afar Ummi kam tun tana jin zafi harta fara jin dad'i, kallonshi kawai take zuciyar ta na k'ara narkewa akan son wani abu da bata so taji tana jinshi akan Salman d'in.
Chapter 18 · 0% Book details