← Book details Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 49

Sashe 17

Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwarsu take tunani tana murmushi ajiyar zuciya ta sauke tana mai k'ara fad'ad'a murmushinta tace "ina ma kadawo yau, da zan zauna da kai ko dukana ne kaci gaba dayi da wannan tattausan hannun naka"
Jawahir dake zaune gefe ita da Khamis ta kalleshi tace "mijina dubi mutuniyar murmushi take ita kad'ai, ina ga fa tunanin yaya Mane take"
Dariya suka saka gaba d'ayansu hakan ya janyo hankalinta, mamakine ya bayyana a fuskarta dan batayi tunanin suna nanba suma, saidai kallonsu kawai take saboda ganin k'afar Khamis a cinyar Jawahir tana masa wankin k'afa, take ta tuna da ranar da tama Salman yankan akaifu, wani murmushin ta koma saki tare da jin wani sanyi na lullub'eta, gaba d'aya taji kawai tana son ganin Salman ko fad'ane ma su dinga yi zata ji dad'i.

Jawahir ce data lura ba tada niyyar magana tace "Hajia Abu tunanin me ake ne haka?" kallonta Ummi tayi tace "ba komai"
Tab'e baki tayi tace "to naji ba komai, amma ya kamata ki shirya gobe muje muyi kitso" cikin farin ciki tace "yawwa dama nima ina so nayi kitso"
Cewa tayi "amma ai da kin bari har yaya Salman zai dawo sai kiyi" hararanta kawai tayi ba tace komai ba, Khamis kam cewa yayi "to nidai kamar kullum ne, indai har kina so kije to ki tabbatar kin kira mijinki kin fad'a masa."
Ba tada zab'in daya wuce ta kira ta fad'a masa dan haka tace "to yaya Khamis zan kira, na lura kaidai kana jin tsoron mutuminan sosai"
Hararan ta yayi yace "ke kuma baki tsoronsa ko jaruma?" dariya kawai tayi ba tace komai ba.

Ummi bata kira Salman ba saida safe sannan ta d'auki wayar ta kuna, ta danna numbershi tana fara k'ara taji gabanta ya fara dukan uku-uku, da k'yar ta iya daurewa tana sauraran ya d'aga.

Tana jin ya d'aga taji cikinta ya d'uri ruwa take taji tana buk'atar kewayawa, amma haka ta dake ba tare da tace komai ba, Salman dake saman hanyar dawowa yana ganin kiranta yaji farin ciki ya mamayeshi, ba tare daya kula ba ya samu kansa yana mai kasaitancen murmushi amma daya tuna wacece Ummi da kuma kashe wayar da tayi, kawai sai ya b'ata rai sannan ya d'aga.

"Oui je t'ecoute" ( na'am ina jinki) ya fad'a a tak'aice, cikin sanyanyen murya tace "haba ba ko sallama?"
Cikin dakakkiyar murya yace "ki fad'i abinda yasa kika kirani da gaggawa inada abinyi?" tab'e baki tayi tace "dama na kira ne dan na fad'a maka za muje waj
en kitso nida Jawahir yanzu, kuma yaya khamis yace dole saina fad'ama zanje shiyasa na kiraka."
Wani buhun haushi ne ya kama shi, wato badan Allah ta kirani bama kuma saida akace ta kira sannan ta kira, ba damuwa zanyi magananinki ya fad'a a ransa.

Bud'ar bakinshi yace "baza kiba to indai nine zan bada izinin, ni dama nasan kinfi k'arfin ki kira ni ki gasheni bare ki tambayeni ya nake saboda bakisan mi ake nufi da miji ba, amma yanzu buk'atarki tasa kin kirani bayan kashe waya da kika yi."
Haushi taji itama cike da tsiwa tace "kaga nifa na kirane badan kamin masifa ba, sannan da kake cewa na kashe waya, e na kashe saboda banga anfanin kirana da zaka yiba tunda kana da wacce zaka dinga hira da ita, kuma ni ba izininka nake jira ba ina so naje kitso kuma zanje."
Cikin tattausan murya yace "to kenan kin fad'amin ne dan nasan zaki tafi, ko ko kin fad'amin ne dan nasan kin isa da kanki, ko kuma umarni ne kike bani akan na baki izinin fitar?"
K'irjinta k'ara tsananta bugawa yake amma haka ta daure tace "ka d'auki d'aya da kaga yafi da cewa dani saika sani a mahalin" cikin jin haushi yace "Ummi ince dai nine mijinki ko?"
Kamar tana gabanshi saida ta murgud'a baki tace "to saime mijin da baisan hakk'in matarshi ba, zaka k'ara aure amma saidai naji a gari amma ba komai akwai Allah, dan haka ni yanzu ko ka bani izini ko ka k'i bani izini, fitata zanyi in yaso in kamatsu ka fara bada umarni to sai ka bari harka kawo k'waillar matar taka saika fara mulkarta, amma ba Ummi ba."
Salman daya saki baki yana sauraranta izuwa yanzu ya fara fahimtar inda zancen, wato tana jin haushi dan zan k'ara aure, murmushi yayi yace "babu ruwanki da amayarta yarinya mai nutsuwa da hankali, sannan na fad'a maki karki je ko ina har saina dawo"
Abinda ya fad'a shiya k'ara harzuk'ata, cikin fitina tare da k'ok'arin b'oye hawayenta tace "saina je d'in, idan ka dawo ka kasheni." cike da izza yace "aiko idan kika fita bada izinina b
, to zaki rasa k'afa ko ido"
Cikin kuka mai tsanani tace "e na rasa k'afar tunda kaine ubana da zaka min baki Ya kama ni." tana fad'a ta kashe wayar, toilet ta shiga ta wanke fuskar'ta sannan ta fito ta samu Jawahir da Khamis suna jiranta fitowarta.

Khamis ne yace "kin kirashi?" kai ta fara girgizawa sannan tace "na kira kuma yace naje, amma wai karna dad'e" hakan data fad'a yasa Khamis ya tabbatar data kirashi d'in.

Cikin farin ciki Khamis ya aje su gidan mai kitson, amma yace idan an ida su hau adaidaita sahu su koma gida tunda suce sai sun biya 'yar kasuwa sunyi siyayya.
_Ummi kam akwai marar jin magana, ko baki ji maganarsa a matsayinshi na mijinki ba, ai kin ji ko a matsayinshi na yayanki._
05/03/2019
17:30 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
```OH ALLAH KABAWA
K LAFIYA ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD S.W.A, ALLAH YASA KAFFARA NE```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Saida su kayi sallah azahar a gidan mai kitson sannan suka fito, a k'afa suka k'araso 'yar kasuwa saboda duk bisa hanyane babu nisa sosai, sayayya su kayi sosai musammam Ummi, duk kud'in da Salman ya bata kaf ta kashesu ga k'ananan kaya da kayan bacci da kuma kayan kwalliya.

Ana kiran sallah la'asar suka tsaya bakin titi suka shiga adaidaita.
_Tsotsayi kenan wanda ba'a sa mashi rana, idan ya wuni tofa baya kwana_
Sun d'auki babbar hanyar da zata sadasu da gidan saiko wani mai mota daya fito daga cikin kwana da iya k'arfinsa cikin ganganci, saiko yayi gaba da adaidaitar dasu Ummi ke ciki.

B'angaren da Ummi take nan adaidaitar ta fad'a, mai adaidaitar na fad'owa k'asa kuma wani mai babur ya taka kanshi take ko shurawa baiyi ba yace ga garinku nan, tuni aka kewaye su ana k'ok'arin basu agaji, wasu samari ne suka kama Jawahir ta taka adaidaitar ta fito ta sama, sannan aka d'aga adaidaitar dan a janye Ummi.

Ana d'aukewa Ummi ta tashi zaune idonta ne suka sauka kan mai adaidaita, tana ganinshi ta dafe kanta tare da zankad'a uwar k'ara take kuma ta sak
zubewa k'asa somammiya, Jawahir da jiki keta mata rawa ta kasa tsayawa daidai wani dattijo ne ya janyeta daga wajen, kafin aka d'aukesu aka nufi babbar asibiti da su.

Jawahir gurjewa kawai tayi a goshi, dan haka ana gama dubata aka amshi wayarta aka kira Khamis, Khamis bawon Allah tashin hankali ne ya shiga wanda bai tab'a shiga irinsa ba, haka ya garzayo yazo asibitin.

Saida aka bashi tabbacin jikinsu da sauki sannan ya tafi gida ya fad'ama manyansu halin da ake ciki.

Babu wanda yayi yink'urin zuwa ba tare daya fad'ama Alhaji ba, amma sam ya rufe ido yace a barta can ita da halinta, ran kowa ya sosu musammam ma iyayenta sunfi kowa shiga damuwa sai kuma Hajia Zeinabou wacce babu wanda ya kaita d'aga hankalinta.

Ganin ba zai barsu ba yasa Hajia Zeinabou ta fara rera mashi kuka tana lallab'arshi, ba zai juri kukanta ba shiyasa ya amince duk mai so yaje ya ganta amma hakan ba yana nufin ya yafe mata bane.

Dan-danan sai asibiti ta cika da yan uwa, an masu barka ta wani b'angaren kuma an jajanta masu, Khamis duk ya rud'e ya rasa ta yanda zaiyi ya kira Salman ya fad'a masa, dan a ganinshi babu dad'i ace an baka amana amma amanar ta salwanta a hannunka.

Missalin 17:20 Salman ya doko ma Khamis kira wanda yasa gabanshi tsinkewa, da k'yar ya d'aga basu ko gaisaba Salman yace "kazo ka d'auke ni dan Allah na gaji da kiranka" kashe wayar yayi ba tare daya jira me zaice ba.

Haka Khamis yaje gidan bus d'in ya d'aukoshi, kallo d'aya Salman yama Khamis yasan akwai matsala amma baya cikin yanayin farin ciki shiyasa bai tanka saba, ganin sun d'auki hanya daban yasa yace "ina kuma zaka kaini malam? ka kaini gida dan Allah yunwa nake ji" baice masa komai ba sai cigaba da tuk'insa yake har suka kai babbar asibitin.

Tunda suka shiga gabanshi keta dukan uku-uku, yana da 'yan uwa dayawa dan haka ya rasa wa zaiyi tunani ke asibiti, zuciyarshi na raya mashi wani ko wata mai mahimmanci sosai ne a gareshi ke kwance anan d'in.

Ummi na zaune an gama mata dressing d'in ciwon, sai yanzu ne take jin zafin ciwon sai kukan shagwab'a take masu Hajia dasu Mama (mahaifiyar Salman) su kuma sai rarrashi suke cike da taussayinta, kwatsam Salman ya fad'o d'akin yana zare ido yana kallon ikon Allah.

Fad'uwar gabanshi ya k'ara tsananta duk jikinshi yayi sanyi ga wani jiri daya keji yana 'dibarshi, kukan da Ummi keyi yasa yaji takaici ya rufeshi, wato rainawa mutane hankali zatayi ma bayan bata ji maganarsa ba.
Chapter 17 · 0% Book details