Sashe 15
Auren Hadi Part 1 Complate Hausa Novel · about 7 min read
Baifi minti talatin ba jawahir ta dawo gidan, ta samu Ummi kwance akan kujera tana ta kuka, kusa da ita ta zauna ta cire hijab d'inta ta d'ago da ita k'yar ta fara tambayarta" sister lafiya, miya faru ne haka kike kuka?"
Share hawayenta tayi tace" babu komai, ba kuka nake ba" hararanta tayi tace" karki rainamin wayo mana, ko yaro ya ganki a haka ai yasan kuka kike, ki fad'amin abinda ke damunki kawai"
Kai ta girgiza tace" nace maki babu komai, karki damu kanki" tashi tayi ta shige d'akinta, binta tayi da kallo tana tunanin abinda ke damunta, dan a iya saninta bata tab'a ganin Ummi na kuka ba tunda take.
Sallah kad'ai ke fiddo Ummi waje, amma ko abinci ta kasa ci duk bata jin dad'in komai, madararta kad'ai take kurb'awa kad'an kad'an, jawahir duk ta shiga damuwa da hakan, shiyasa ma ta kira khamis ta tambayeshi ko akwai abinda yama Ummi ne, amma yace babu komai sannan yace ta rabu da ita.
Har khamis ya dawo gidan baiga Ummi ba, jawahir ta rok'eshi yaje yaji abinda ke damunta har yasa ta kuka amma yak'i, saima fad'a mata da yayi auren da Salman ke son k'arawa da zaran ya dawo tare da nuseiba.
Cikin rashin Fahimtar jawahir tace" aure kuma, da nuseiba, nuseiba dai k'anwarka, amma yaushe yaya Salman yayi aure har yake tunanin sak
wani auren, kuma yaushe suka fara ma soyayyar b
tare da kowa ya sani ba.?" kallonta yayi yace" e ita, ni bama wannan ne a gaba na ba, kinsan mamarmu tana so ta had'a rumana da Salman, shi kuma nuseiba ce tafi kwanta masa a rai, dukansu 'yan uwana ne amma fa rumana ciki d'aya muka fito, duk inda na goyi baya sai na shiga matsala, shiyasa nake so ya nemi k'uri'arshi da kanshi bana so na shiga cikin maganar."
Bata sake cewa komai ba, dan a ganinta hakan bai dace ba kuma yaya Salman zaiyi hakane dan ya nuna ma duniya baya son Ummi.
*Bayan kwana uku*
Salman ne a d'akinshi keta birgima a k'asa, duk yayi kaca-kaca da d'akin da kaya ya barbaza komai, hatta zanin gadon ya jayoshi izuwa k'asa ya rufe jikinshi dashi.
Abu guda kawai yake fad'i a bakinshi" Allah Allah Allah na wayyo Allah" kamar mazari haka jikinshi ke rawa, duk jijiyoyinshi sun tashi idonshi jawur kamar garwashin wuta, hak'oranshi had'e sai hard'ewa suke.
Cikin wannan yanayin ya d'auki wayarshi ya dannan, pic d'in Ummi ne ya bayyana, kallo yake kamar zai had'iyeta, sai gani nayi ya buga wayar da bango yana wani irin gunji kamar kuka kamar kuwa, saidai ya kasa furta ko kalma d'aya.
Da k'yar ya iya rairafawa ya kai ga jakarshi ya d'auki magani har kala biyu ya b'alli guda bibbiyu ya had'a.
A hankali ya fara dawowa normal kamar yanda yake, nunfashinshi ya daidaita saidai har yanzu akwai zafi a jikinshi, hawayene ke bin fuskanshi a hankali yake fad'in" bazan yafe maki ba har abada, shekara d'aya kenan rabon da naji irin haka, amma gashi yau na kusa mutuwa saboda kin shigo rayuwata, kin kusa tarwatsani."
" Dole na koma gida kafin na aikata ba daidai ba, dole naje gida na samu alhaji na rok'eshi ya auramin nuseiba kafin na mutu, wallahi ke kuma sai kinyi kuka da idonki muguwa marar imani, ba zan sak
kallonki ba daga yau harna mutu."
_Salman kuma haka abin ya zama
*Ummi* na zaune d'aki, number naga tana danna kira tana kashewa, tun tuni haka takeyi kamar wasan yara, d'aga kanta tayi sama tana fadin" miyake damuna, miyasa na damu da tunaninsa, miyasa na kasa mantawa da maganar aurenshi, miyasa nake jin haushinshi dan zai k'ara aure?"
Siraran hawayene suka biyo kuncinta, a hankali ta sak
fad'in" ni dai nasan bana son yaya Salman domin kuwa da muguntarshi ya raine ni, haka kuma ba ban tab'a jin koda k'aunarsa ba a zuciyata ba, to miyasa?" kukan da tafe dashi ya jawo hankalin jawahir dake zaune ita da khamis suna hira, tashi tayi ta shiga d'akin ta zauna kusa da ita ta fara magana.
"Ummi sai yanzu ne nagane wani abu, ban tab'a tunanin zaki iya b'oyemin wani abu daya shafeki ba, na d'auka ni da ke d'aya ne zaki fad'amin komai dake damunki, kamar yanda nake fad'a maki abinda ke damuna kuma na nemi shawarar ki, ashe ke ba haka bane a wajenki"
" Ki duba ki gani mana, yaya Salman ya amince da kizo gida na ki zauna, bayan kuma ga k'anwarshi nan khairat, ga hafsat da nadia duka suma yan uwanshi ne amma baice kije can ba,sai yace kizo nan, miyasa yace haka?"
Ci gaba tayi da fad'in" saboda yana ganin munfi kusa da juna shiyasa, yasan kuma babu abinda zai dameki anan inhar muna tare, amma gashi yanzu kina cikin damuwa tsawon kwana uku, ba kicin abinci sosai sai kuka kike amma kin 'ki fad'amin damuwar ki saboda kina ganin ban kai nasani ba."
Kai ta girgiza mata tace" a'a jawahir ba wai baki kai bane, saidai bansan ta yanda zaki fahimce niba, ni kaina bansan miye yake damuna ba, bansan akan mi nake damuwa, saidai nasan za kimin dariya kuma ki fahimceni ba daidai ba idan na fad'a"
05/03/2019
17:28 - Mamar Latif
AUREN HA'DI
_Samira Harouna_
_My
K *BILKISU Z.
YA'U* murnar kammala wannan littafi naki mai sunan *SO MAHA'DIN RAYUWA* ha'ki'ka ya fad'akar ya nishad'antar, musammam ma a wajen mu 'yan soyayya, ina maki fatan alkairi ina rok'on maki Ubangiji da ya yafe maki kurakuran dake cikin wannan littafi, inda ki kayi dai-dai kuma Allah ya baki ladar fad'akarwa_
_Sai mun jiki a novel na gaba mutuniyata 'yar hannu dama na, ina mugun sonki BK ta_
``` daga samirar ki rabin ran bloodynki```
*ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_
*Page*
Jawahir tace" haba Ummi, ta yaya zan fahimceki ba daidai ba, ki fad'amin insha Allah zanyi k'ok'ari na fahimta yanda kike nufi" cikin kuka ta fara mata bayanin abinda take tunani.
"Jawahir bansan miyasa nake jin haushin yaya Salman ba tunda yaya Khamis ya fad'amin zai k'ara aure, na rasa dalilin tsanarsa nidai nasan ba kishinsa nake ba domin kuwa bana sonshi kuma bana k'aunarshi, to amma miyasa nake damuwa bansani ba" saida ta goge hawayen da suka zubo mata taci gaba da cewa.
" Jawahir wata'kila wannan itace 'kaddarar rayuwata, har abada bazan samu abinda nake so ba, da farko an min AUREN HA'DI da wanda bana so ba tare dana shirya ba, a bisa d'an k'ank'anin kuskure akamin dukan tsiya aka kawo ni gidan miji babu shiri, to yana iya dole na hak'ura tunda banda yanda zanyi, Jawahir dama bana tsammanin cin amarci ko farin ciki a tare da yaya Salman, saidai ina buk'atar na samu 'yanci kamar kowace mace mai ji da kanta, amma ina na kasa samu azabtar dani kawai yake a gidansa, ya tafi ya barni ko sati banyi a gidansa ba, shine yanzu zai k'ara aure dan yaci mutunci na, shin Jawahir kinsan mai zai faru idan ya k'ara auren nan?"
Kai ta girgiza, ci gaba tayi da cewa" zai kawo min Nuseiba a matsayin amaryarsa, yarinyar da bana jin ta cika shekara shabiyar a duniya, zata fini matsayi da 'yanci a gidanshi saboda ita yana sonta, cikin k'ank'anin lokaci zata fahimci zaman da muke da shi, daga nan saita fara jin ta fini sannan itace mowa a wajen mai gida hakan zaisa ta fara min gani-gani."
"Bayan wani d'an lokaci kuma zata samu ciki, kinga daga nan komai zai k'are, domin kuwa zata fara min gori akan hakan shi kuma zai dinga biye mata, d'awainiyarta hidimarta rainon cikinta zai zama duk nice, idan kuma na'ki nasha duka haka harta haihu daga nan zata fara min gorin haihuwa lokacin shi kuma ya d'auki soyayyar duniyar ya d'ora akan d'anta da ita kanta, zai dinga fita da su duk inda zaije koda barin garine, ni kuma zan zama 'yar gadin gida har lokacin da tawa zata zo k'arshe." kallabinta ta kama ta rufe bakinta da shi taci gaba da rera kuka.
Da k'yar Jawahir ta rarrasheta tayi shiru, kafin ta fara magana" 'yer uwata kiyi hak'uri, insha Allah duk abinda kika fad'a ba zai faru ba, ke da yaya Salman da Nuseiba duka 'yan uwane ku, babu wanda zai cutar da wani, kuma ni bana tunanin auren zaiyiwu, saboda yaya Khamis bayasan maganar gaba d'aya."
Kallonta Ummi tayi tace" dan yaya Khamis baya so, ba shi ke nufin zai fasa abinda yayi niyya ba." kafad'arta ta dafa tace" to naji ma ace ya aureta, miye Nuseiba keda shi da har zaki tashi hankalinki? ni kaina k'anwa take gareni, bare kuma ke da kika ban shekara d'aya, kinga kenan k'anwarki ce kema." wani murmushin kan labb'a tayi tace"Jawahir bakisan kishiya bane shiyasa, bata kad'an kuma bata k'arama"
Dariya jawahir tayi tace" yanzu ke harkin fara kallon nuseiba a kishiyarki? ai 'yer uwarki ce" hararanta tayi tace" lokacin da zata shiga tsakanina da mijina ba baki sani ba"kallon mamaki ta bita dashi tace" Ummi kece kike kiran yaya Salman mijinki, to inaga fa kamar anjima da kashe boss" da gudu tabar d'akin saboda dukan da Ummi takai mata.